Wajibi Ne Limaman Kiristoci Su Ki Yin Aure?
ADDINAI kamar su Buddha da Cocin Katolika da na Orthodox da dai sauransu a duniya sun umurci manyan limamansu cewa kada su yi aure. Wasu mutane kuma suna ganin cewa a dalilin wannan dokar ce ya sa ake zargin manyan malaman addinai da yawa da yin lalata da mata.
Amma shin Littafi Mai Tsarki ya hana manyan malamai yin aure ne? Don mu san amsar wannan tambayar, bari mu bincika tarihin wannan al’adar na ƙin yin aure da kuma abin da Allah ya ce game da hakan.
TARIHIN HANA LIMAMAI YIN AURE
A wani taron da aka yi a shekara ta 2006, Paparuma Benedict na Goma Sha Shida ya gaya wa Hukumar Cocin Roma cewa, ƙin yin aure wajibi ne domin “al’ada ce da ake yi tun a zamanin manzannin Yesu.”
Amma gaskiyar ita ce, Kiristoci a ƙarni na farko ba su haramta yin aure ba. Manzo Bulus da ya yi rayuwa a ƙarni na farko ya gargaɗi Kiristoci game da maza da suke “mai da hankali ga aljannu masu ruɗi” kuma suke “hana aure.”
A ƙarni na biyu ne coci suka soma wannan al’adar ƙin yin aure. Littafin nan Celibacy and Religious Traditions ya bayyana cewa, wannan al’adar “ta soma ne a daidai sa’ad da aka hana batun yin jima’i a Daular Roma.”
Da shigewar lokaci, sai limaman coci da kuma Ubannin Coci suka soma ɗaukaka batun ƙin yin aure. Suna ganin cewa yin jima’i yana ɓata limaman kuma yana hana su yin aikinsu
yadda ya kamata. Duk da haka, littafin nan Encyclopædia Britannica ya ce: “A kusan ƙarshen ƙarni na 10, firistoci da kuma limamai da yawa suna da aure.”A taron Lateran Councils da aka yi a ƙasar Roma a shekara ta 1123 da 1139 ne aka tilasta wa limaman cewa ba za su yi aure ba. Kuma har a yau Cocin Katolika suna bin wannan al’adar. Ta hakan, cocin sun hana limaman yin aure don kada su ɗauki kuɗi da kuma ƙaddarorin cocin su ba yaransu.
ABIN DA ALLAH YA CE GAME DA ƘIN YIN AURE
A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah ya faɗi yadda ya ɗauki batun ƙin yin aure. Yesu ya yi wani bayani game da waɗanda suka ƙi yin aure kamar yadda shi ya yi “sabili da Mulkin sama.” (Matta 19:12) Game da wannan batun kuma, Bulus ya yi magana a kan Kiristoci da suka zaɓa kada su yi aure saboda “bishara.”
Amma ba wai Yesu da Bulus suna tilasta wa Kiristoci masu hidima su ƙi yin aure ba ne. Yesu ya ce ba kowane mabiyansa ne za su iya ƙin yin aure ba. Sa’ad da Bulus yake magana game da waɗanda ba su yi aure ba, ya ce: “Ba ni da wani umurni daga wurin Ubangiji ba: amma shari’ata nake bayarwa.”
Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a ƙarni na farko, limamai da yawa har da Bitrus sun yi aure. (Matta 8:14; Markus 1:
Ba a hana yin jima’i a aure ba, domin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mijin shi ba matatasa abin da ya wajabce ta” kuma ‘kada ma’aurata su hana ma juna’ yin jima’i. (1 Korintiyawa 7:
SABODA BISHARA
Me ya sa Yesu da Bulus suka ce ƙin yin aure yana da kyau duk da cewa yin hakan ba dole ba ne? Domin idan mutum bai yi aure ba, hakan zai ba shi damar yi wa mutane wa’azi sosai. Waɗanda ba su yi aure ba ba sa fuskantar damuwar da ma’aurata suke fuskanta. Don haka, suna da isashen lokacin yin wa’azin bishara.
Alal misali, David ya bar aikinsa da ake biyan sa albashi mai soka a babban birnin Meziko kuma ya koma wani ƙauye a ƙasar Kwasta Rica don ya koya wa mutane Littafi Mai Tsarki. Shin David yana ganin rashin aure ya taimaka masa? Ya ce: “Ƙwarai kuwa. Ba abu mai sauƙi ba ne mutum ya saba da al’ada da kuma yanayin wani waje dabam ba. Amma da yake ba ni da aure, hakan ya sa ya yi mini sauƙi in saba da wajen.”
Wata ‘yar’uwa mai suna Claudia da ba ta yi aure ba ta je wurare da yawa da ake bukatar masu wa’azi sosai. Ta ce: “Ina jin daɗin hidimata. Idan na ga yadda Allah yake kula da ni, hakan yana ƙarfafa bangaskiyata kuma yana sa na ƙara kusantar sa sosai.”
“Ko kana da aure ko a’a, za ka yi farin ciki idan ka yi iya ƙoƙarinka a hidimar Jehobah.”
Bai kamata wanda ya ƙi yin aure ya riƙa ganin kamar kaya mai nauyi ya ɗauka ba. Claudia ta ƙara da cewa: “Ko kana da aure ko a’a, za ka yi farin ciki idan ka yi iya ƙoƙarinka a hidimar Jehobah.”