Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
Shin muna rayuwa ne a “kwanaki na ƙarshe”?
Me za ka ce?
E
A’a
Wataƙila
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce
‘Cikin kwanaki na ƙarshe miyagun zamanu za su zo.’ (2 Timotawus 3:1) Annabcin Littafi Mai Tsarki da kuma abubuwan da suke faruwa a yau sun nuna cewa muna “kwanaki na ƙarshe.”
Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?
A kwanaki na ƙarshe, za a yi yaƙe-yaƙe da yunwa da girgizar ƙasa da kuma munanan cututtuka.
—Matta 24: 3, 7; Luka 21:11. A kwanaki na ƙarshe, ɗabi’ar mutane za ta lalace kuma mutane ba za su so su kusaci Allah ba.
—2 Timotawus 3: 2-5.
Mene ne zai faru da ‘yan Adam a nan gaba?
Wasu sun yi imani cewa . . .a kwanaki na ƙarshe, za a halaka duniya da abubuwan da ke cikinta, wasu kuma suna sa rai cewa abubuwa za su gyaru a nan gaba. Mene ne ra’ayinka?
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce
‘Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.’
Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?
A ƙarshe, za a halaka mugayen mutane.
—1 Yohanna 2:17. Za a mai da duniya ta zama aljanna.
—Ishaya 35:1, 6.