Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Mulkinka Shi Zo”​—Addu’ar Da Miliyoyin Mutane Suke Yi

“Mulkinka Shi Zo”​—Addu’ar Da Miliyoyin Mutane Suke Yi

Mutane sun yi ɗarurruwan shekaru suna yin addu’a cewa: “Mulkinka shi zo.” Me ya sa suke wannan addu’ar? Domin Yesu ya ce mabiyansa su riƙa yin addu’a Mulkin Allah ya zo.

Da farko, almajiran Yesu ba su fahimci kome da kome game da Mulkin ba. Akwai lokacin da suka yi masa tambaya cewa: “Ubangiji, yanzu ne za ka mayar wa Isra’ila mulki?” Yesu bai ba su amsa kai tsaye ba kuma mai yiwuwa hakan ya ba su mamaki. (Ayyukan Manzanni 1:​6, 7) Shin, hakan yana nufin cewa ba zai yiwu mu san abin da ake nufi da Mulkin Allah, da kuma lokacin da Mulkin zai zo ba? A’a!

Wannan Hasumiyar Tsaro za ta taimaka maka ka sami amsoshin tambayoyin da ke gaba:

  • Me ya sa muke bukatar Mulkin Allah?

  • Wane ne Sarkin Mulkin Allah?

  • Yaushe ne Mulkin Allah zai soma sarauta a kan duniya?

  • Mene ne Mulkin Allah zai yi?

  • Me ya sa zai dace ka goyi bayan Mulkin Allah yanzu?

  • Mene ne Mulkin Allah?