Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yaushe Ne Karshe Zai Zo? Abin da Yesu Ya Ce

Yaushe Ne Karshe Zai Zo? Abin da Yesu Ya Ce

Kamar yadda muka koya a talifin da ya gabata, a duk lokacin da Littafi Mai Tsarki ya ambaci ƙarshen duniya, ba ya nufin cewa za a hallaka doron ƙasa ko kuma ’yan Adam gabaki ɗaya. A maimakon haka, yana nufin ƙarshen muguwar tsarin duniyar Shaiɗan da kuma waɗanda suke goyon bayansa. Amma Littafi Mai Tsarki ya gaya mana lokacin da hakan zai faru kuwa?

GA ABUBUWA BIYU DA YESU YA FAƊA GAME DA ƘARSHEN DUNIYA:

“Domin haka sai ku zauna da shiri, gama ba ku san ranar, ko a ƙarfe nawa ne ba.”​—MATIYU 25:13.

“Ku lura, ku zauna da shiri, domin ba ku san lokaci, ko ƙarfe nawa ne wannan zai faru ba.”​—MARKUS 13:33.

Don haka, babu mutumin da ya san ranar da ƙarshen zai zo. Amma Allah ya “ƙayyade lokaci,” wato ‘rana’ da kuma ‘ƙarfen’ da ƙarshen zai zo. (Matiyu 24:36) Shin hakan yana nufin ba za mu taɓa iya sani ko ƙarshen ya kusa ba? A’a. Yesu ya gaya wa almajiransa abubuwa da za su nuna musu cewa ƙarshen ya kusa.

ALAMUN

Waɗannan abubuwan ne Yesu ya ce za su zama alamun “ƙarshen zamani.” Ya ce: “Al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a kuma yi yunwa da rawar ƙasa a wurare dabam-dabam.” (Matiyu 24:3, 7) Ya kuma ce za a yi “bala’i,” wato ɓarkewar cututtuka iri-iri. (Luka 21:11) Shin kana ganin waɗannan alamun?

A yau mutane suna wahala sosai saboda yaƙe-yaƙe da yunwa da girgizar ƙasa da kuma cututtuka. Alal misali, a 2004, an yi mummunar girgizar ƙasa a Tekun Indiya da ta jawo ambaliyar da ta kashe wajen mutane 225,000. A cikin fiye da shekara ɗaya, annobar korona ta kashe mutane wajen miliyan 2.6 a duk duniya. Yesu ya ce abubuwa kamar haka za su nuna cewa ƙarshen ya kusa.

“KWANAKI NA ƘARSHE”

Littafi Mai Tsarki ya kira lokaci da ke dab da ƙarshen zamani “kwanaki na ƙarshe.” (2 Bitrus 3:​3, 4, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Littafin 2 Timoti 3:1-5, sun nuna cewa a kwanakin ƙarshe, mutane za su kasance da ɗabi’u marasa kyau. (Ka duba akwatin nan “ Dab da Ƙarshen Duniya.”) Shin kana ganin yadda mutane suke son kansu da yadda suke yin mugunta da kuma yadda suke ƙin juna? Waɗannan alamun ma sun nuna cewa muna kwanakin ƙarshe.

Yaushe kwanakin ƙarshen zai ƙare? Littafi Mai Tsarki ya ce lokaci “kaɗan” ne ya rage. Sa’an nan Allah zai “halaka masu halaka duniya.”​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 11:15-18; 12:12.

DUNIYA TA KUSA TA ZAMA ALJANNA!

Allah ya riga ya ƙayyade rana da lokacin da zai hallaka wannan muguwar zamani. (Matiyu 24:36) Amma, akwai albishiri, Allah “ba ya so wani ya halaka.” (2 Bitrus 3:9) Don haka, Allah yana ba wa ’yan Adam damar koya game da shi da kuma yi masa biyayya. Me ya sa? Domin yana so mu tsira a lokacin da zai hallaka wannan duniyar, kuma mu shiga sabuwar duniya.

Allah ya tabbata cewa kowa yana da damar koyan abin da yake bukata ya yi don ya kasance a sabuwar duniya. Yesu ya ce za a yi wa’azin Mulkin Allah ‘ga dukan al’ummai.’ (Matiyu 24:14) A duk faɗin duniya, Shaidun Jehobah sun yi fiye da sa’o’i biliyan biyu a 2019 suna wa’azi da koya wa mutane abin da ke Littafi Mai Tsarki. Yesu ya ce za a yi wa’azin nan a dukan faɗin duniya kafin ƙarshen ya zo.

Mulkin ’yan Adam ya kusa ya zo ƙarshe. Amma albishirin shi ne za ka iya tsira wa ƙarshen duniya kuma ka shiga aljanna da Allah ya yi alkawarin ta. Talifi na gaba zai tattauna abin da za ka iya yi don ka yi rayuwa a sabuwar duniyar.

Annabcin da Yesu ya yi game da “kwanaki na ƙarshe” ya ba mu bege