Muna Bukatar Sabuwar Duniya!
Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya António Guterres ya ce: “Duniya tana cike da matsaloli.” Ka yarda da hakan?
Labaran duniya suna cike da abubuwa masu tā da hankali, kamar
Cututtuka da annoba
Bala’o’i
Talauci da yunwa
Gurɓata mahalli da ɗumamar yanayi
Aikata laifi da ta’addanci da cin hanci
Yaƙe-yaƙe
Lallai muna bukatar sabuwar duniya, inda za a sami
Ƙoshin lafiya
Zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali
Abinci a yalwace
Mahalli marar guba
Adalci don kowa
Salama a duk duniya
Amma me muke nufi idan muka yi maganar sabuwar duniya?
Me zai faru da duniyar da muke ciki yanzu?
Me za mu yi don mu yi rayuwa a sabuwar duniya?
Wannan fitowar Hasumiyar Tsaro tana ɗauke da amsoshin da Littafi Mai Tsarki ya bayar ga tambayoyin nan, da ma wasu.