Allah Ya San da Zamanka Kuwa?
ABIN DA HALITTU SUKA KOYA MANA
Awa ɗaya na farko da jariri yake yi bayan an haife shi yana da muhimmanci sosai. Me ya sa? Domin idan uwaye suka kasance da jariransu da zarar sun haife su, hakan zai taimaka wa yaran sosai a lokacin da suke girma. a
Me ya sa uwa take kula da jaririnta da kyau? Wata farfesa mai suna Jeannette Crenshaw ta bayyana a cikin mujallar nan The Journal of Perinatal Education cewa, “yadda mahaifiya take riƙe jaririnta da shayar da shi da kuma kallon sa ne yake kara sinadarin hormone da ake kira oxytocin. Kuma sinadarin ne yake daɗa ƙaunar da take wa jaririn.” Akwai wani sinadarin hormone da mace take fitarwa a lokacin. Sinadarin ne yake “sa ta riƙa taimaka wa yaron” da sauri idan yana bukatar wani abu. Me ya sa hakan yake da muhimmanci?
Mahaliccinmu Jehobah b ne ya ƙulla dangantakar da ke tsakanin uwa da jaririnta. Sarki Dawuda ya ce Allah ne ya fitar da shi ‘daga cikin mamarsa’ kuma ya kiyaye shi sa’ad da mahaifiyarsa take renonsa. Don haka, ya yi addu’a ya ce: “An danƙa ni a hannunka tun kafin haihuwata, kai ne Allahna tun lokacin da mamata ta haife ni.”—Zabura 22:9, 10.
KA YI LA’AKARI DA WANNAN: Tun da Allah ya halicci irin waɗannan sinadaran don ya tabbatar da cewa uwa ta kula da jaririnta da kyau sa’ad da yake bukatar wani abu, ba ka ganin cewa Allah yana kula da kowannenmu ba?
LITTAFI MAI TSARKI YA CE ALLAH YA SAN DA ZAMANMU
Yesu Kristi wanda ya san Mahalicci fiye da kowannenmu ya ce: “Ba ana tsayar da ɗan tsuntsu guda biyu kobo ɗaya ba? To, ba ɗayansu wanda zai faɗi a ƙasa ba tare da sanin Ubanku ba. Ai, ko gashin kanku ma an ƙirga su. Saboda haka, kada ku ji tsoro. Ai kun fi ɗan tsuntsu daraja barkatai.”—Matiyu 10:29-31.
Ba dukanmu ba ne mukan mai da hankali ga tsuntsayen da muke gani ba balle ma a ce mun san lokacin da ‘ɗayansu ya faɗi a ƙasa.’ Amma Mahaliccinmu ya san da zaman kowannensu! Duk da
haka, tsuntsaye da yawa ba su fi ’yan Adam daraja a gare shi ba. Wane darasi ne muka koya? Mun koya cewa bai kamata mu “ji tsoro” ko mu ɗauka cewa Allah bai san da zamanmu ba. Amma mu sani cewa ya damu da mu!Allah ya damu da yanayinmu sosai kuma yana tausaya mana
Nassosi sun tabbatar mana cewa
-
“Idanun Yahweh suna ko’ina, suna lura da masu mugunta da masu kirki.”—KARIN MAGANA 15:3.
-
“Idanun Yahweh suna a kan masu adalci, kunnuwansa kuma suna jin kukansu.”—ZABURA 34:15.
-
“Zan yi murna da farin ciki saboda ƙaunarka marar canjawa, gama ka ga wahalata, ka san damuwar zuciyata.”—ZABURA 31:7.
“NA ƊAUKA JEHOBAH BA YA ƘAUNATA”
Sanin cewa Allah yana ƙaunarmu kuma ya damu da yanayin da muke ciki zai ƙarfafa mu kuwa? Babu shakka, sanin hakan zai ƙarfafa mu. Wata mai suna Hannah, c daga ƙasar Ingila da ta shaida hakan ta ce:
“A lokuta da yawa, na ɗauka cewa Jehobah ba ya ƙaunata kuma ba ya jin addu’o’ina domin ban da bangaskiya. Na ga kamar yana min horo ne don ban da wani muhimmanci a gare shi. Kuma ba ya damuwa da ni.”
Amma yanzu Hannah ba ta shakkar ko Jehobah ya damu da ita ko kuma yana ƙaunarta. Me ya canja ra’ayinta? Ta ce: “A hankali na canja ra’ayina. Na tuna da wani jawabi daga Littafi Mai Tsarki shekaru da yawa da suka shige game da fansar Yesu da ya sa na tabbata cewa Jehobah yana ƙaunata. Kuma a duk lokacin da Jehobah ya amsa addu’o’ina, nakan fashe da kuka don na gane cewa yana ƙaunata sosai. Ban da haka ma, yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma halartan taro sun taimaka mini na san Jehobah sosai da halayensa da kuma yadda yake ɗaukanmu. Yanzu na tabbata cewa Jehobah ya damu da mu kuma yana ƙaunar mu duka. Ban da haka ma, yana marmarin taimaka wa kowannenmu.”
Furucin da Hannah ta yi abin ƙarfafa ne sosai. Amma ta yaya za ka tabbata cewa Allah ya san ka da kyau kuma yana yin la’akari da kai? Za a amsa wannan tambayar a talifi na gaba.
a Wasu mata da suke fama da ciwon da ake kira postpartum depression da ke sa ɓacin rai, yana musu wuya su kasance da yaransu a lokacin da suka haifi yaran. Amma bai kamata su riƙa ganin kansu da laifi ba. Cibiyar da ke nazari a kan lafiyar ƙwaƙwalwa ta Amirka wato, U.S. National Institute of Mental Health ta bayyana cewa “mahaifiya ba ta kamuwa da wannan cutar don wani abin da ta yi ko abin da ba ta yi ba . . . amma wataƙila wasu abubuwa a jikinmu ne suke janyo cutar nan.” Domin samun ƙarin bayani a kan batun nan, ka dubi talifin nan “Understanding Postpartum Depression” da ke Awake! na 8 ga watan Yuni, 2003.
b Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Jehobah ko Yahweh shi ne sunan Allah.—Zabura 83:18.
c An canja wasu sunayen a jerin talifofin nan.