Wa Ke Sa Mu Wahala?
Idan ba Allah ba ne yake haddasa wahalar da muke sha, to me ya sa ake rashin abinci da talauci da yaƙe-yaƙe da cututtuka masu muni da kuma bala’i? Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abubuwa guda uku da suke janyo wahalar da ’yan Adam suke sha:
Sonkai da Haɗama da kuma Ƙiyayya. ‘Lokacin da mutum ya sami iko bisa wani, yakan cuce shi.’ (Mai-Wa’azi 8:9, Littafi Mai Tsarki Cikin Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Mutane suna shan wahala saboda abin da mugayen mutane suke yi.
Sa’a da Tsautsayi. Mutane suna shan wahala domin “sa’a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu.” (Mai-Wa’azi 9:11, Littafi Mai Tsarki) Ayar nan tana nufi cewa, a wasu lokuta wasu abubuwa suna faruwa ne idan mutum ya kasance a wani wuri a lokacin da bai dace ba. Ƙari ga haka, hatsari yakan faru idan mutum bai mai da hankali sosai ba.
Mugun da Yake Iko da Duniya. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana ainihin dalilin da ya sa mutane suke shan wahala. Ya ce: “Mun sani mu ’ya’yan Allah ne, ko da yake duniya duka tana a hannun mugun nan.” (1 Yohanna 5:19) Shaiɗan shi ne “mugun nan,” kuma a dā shi mala’ikan Allah ne mai iko sosai amma “ba ya tsaya a kan gaskiya ba.” (Yohanna 8:44, Littafi Mai Tsarki Cikin Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Wasu mala’iku sun haɗa kai da Shaiɗan kuma suka yi wa Allah tawaye don su cim ma bukatunsu. Hakan ya sa sun zama aljanu. (Farawa 6:1-5) Tun daga lokacin da Shaiɗan da aljanunsa suka yi tawaye, sun yi amfani da ikonsu wajen haddasa wahala a duniya musamman a zamaninmu. Yanzu, Shaiɗan yana fushi sosai kuma yana ‘ruɗin dukan duniya,’ hakan ya sa ’yan Adam suna fama da wahala a duniya. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:9, 12) Hakika, Shaiɗan mugu ne. Yana farin ciki sosai idan ya ga mutane suna shan wahala. Don haka, Shaiɗan ne yake haddasa wahalar da muke sha ba Allah ba.
KA YI LA’AKARI DA WANNAN: Wanda ba shi da tausayi ne zai sa mutane su riƙa shan wahala haka kawai. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Saboda wannan halin da Allah yake da shi, “ba zai taɓa aikata mugunta ba! A wurin Mai Iko Duka babu kuskure!”—Ayuba 34:10.
Amma kana iya tambayar kanka, ‘Har yaushe Allah zai ƙyale Shaiɗan ya ci gaba da iko da duniya?’ Mun koya cewa Allah ya tsani mugunta kuma yana damuwa don wahalolinmu. Ƙari ga haka, Kalmarsa ta ce: “Ku danƙa masa dukan damuwarku, gama shi ne mai lura da ku.” (1 Bitrus 5:7) Allah yana ƙaunar mu kuma yana da iko ya cire dukan wahaloli da kuma rashin adalci da muke fuskanta. Talifi na gaba zai bayyana mana hakan. a
a Don samun ƙarin bayani game da dalilin da ya sa muke shan wahala, ka duba darasi na 26 a littafin nan Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! Shaidun Jehobah ne suka wallafa kuma za ka iya sauƙar da shi a dandalin www.dan124.com/ha.