TALIFIN NAZARI NA 20
WAƘA TA 67 Mu Yi “Waꞌazin Kalmar Allah”
Bari Kauna Ta Sa Ka Ci-gaba da Yin Waꞌazi!
“Kafin ƙarshe ya zo, dole ne a yi wa dukan alꞌummai shelar labarin nan mai daɗi.”—MAR. 13:10.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga yadda ƙauna za ta sa mu yi waꞌazi da ƙwazo da kuma dukan zuciyarmu.
1. Mene ne muka koya a taron shekara-shekara na 2023?
A TARON shekara-shekara na 2023, a mun sami ƙarin haske a kan wasu abubuwa da muka yi imani da su, kuma an yi wata sanarwa mai daɗi game da waꞌazinmu. Alal misali, mun koyi cewa wataƙila wasu za su samu damar soma bauta ma Jehobah bayan halakar Babila Babba. An kuma sanar da cewa daga watan Nuwamba 2023, masu shela ba sa bukatar su ba da rahoton dukan abubuwan da suka yi a waꞌazi. Shin hakan yana nufin cewa ba ma bukatar mu yi waꞌazi da gaggawa kuma ne? Aꞌa, ba abin da ake nufi ke nan ba!
2. Me ya sa muke bukatar mu ƙara yin waꞌazi da gaggawa duk wayewar gari? (Markus 13:10)
2 Yanzu ne ya kamata mu fi yin waꞌazi da gaggawa yayin da ƙarshen yake ƙara matsowa. Me ya sa? Domin lokaci yana ƙurewa. Ka lura da abin da Yesu ya ce game da waꞌazin nan da muke yi a kwanakin ƙarshe. (Karanta Markus 13:10.) A littafin Matiyu, Yesu ya ce za a yi waꞌazin labarin nan mai daɗi a dukan duniya kafin “ƙarshen” ya zo. (Mat. 24:14) Ƙarshen yana nufi lokacin da za a halaka duniyar Shaiɗan gaba ɗaya. Jehobah ya riga ya shirya rana da kuma daidai lokaci da zai yi hakan. (Mat. 24:36; 25:13; A. M. 1:7) Duk wayewar gari, muna ƙara yin kusa da ƙarshen. (Rom. 13:11) Amma kafin ƙarshen ya zo, dole mu ci-gaba da yin waꞌazi.
3. Me yake motsa mu mu yi wa mutane waꞌazi?
3 Ga wata tambaya mai muhimmanci da ya kamata kowannenmu ya yi ma kansa yayin da yake yin waꞌazi: Me ya sa muke yin waꞌazi? Amsar ita ce, ƙauna ce take sa mu yi waꞌazi. Yayin da muke waꞌazi, muna nuna cewa muna ƙaunar Jehobah da sunansa, muna ƙaunar mutane kuma muna son labari mai daɗi da muke waꞌazin sa. Bari mu tattauna su ɗaya bayan ɗaya.
MUNA WAꞌAZI DON MUNA SON LABARI MAI DAƊI DA MUKE WAꞌAZIN SA
4. Yaya muke ji idan aka gaya mana labari mai daɗi?
4 An taɓa kawo maka labari mai daɗi? Yaya hakan ya sa ka ji? Mai yiwuwa ka ji cewa wata a danginku ta haihu, ko an ba ka wani aiki da ka daɗe kana neman sa. Ba mamaki ka yi farin ciki sosai, kuma nan-da-nan ka soma gaya ma ꞌyanꞌuwa da abokan arziki. Shin haka ka ji da aka kawo maka labari mai daɗi na Mulkin Allah? Ba shakka wannan labari ya fi kowanne labari daɗi.
5. Yaya ka ji lokacin da ka soma koyan gaskiya da ke Kalmar Allah? (Ka kuma duba hotunan.)
5 Ka tuna yadda ka ji a lokacin da ka soma koyan gaskiya daga Kalmar Allah. Ka ga cewa Ubanmu na sama yana ƙaunar ka kuma yana so ka shigo iyalinsa don ka bauta masa tare da mutanensa. Ya yi alkawari cewa zai kawo sabuwar duniya, zai cire baƙin ciki da wahala, kuma ya ce zai ta da waɗanda kake ƙauna da suka mutu. Ya ma ce zai yi abubuwa fiye da haka. (Mar. 10:29, 30; Yoh. 5:28, 29; Rom. 8:38, 39; R. Yar. 21:3, 4) Da ka ji abubuwan nan, ka yi farin ciki sosai. (Luk. 24:32) Ka so abin da ka ji sosai kuma ka soma gaya wa mutane.—Ka duba Irmiya 20:9.
6. Me ka koya daga labarin Ernest da Rose?
6 Ga abin da ya faru da wani ɗanꞌuwa. Sunansa Ernest, b kuma mahaifinsa ya rasu saꞌad da yake shekara 10. Ernest ya ce: “Na yi ta tunani: ‘Shin ya je sama ne, ko kuma ya mutu ke nan kwata-kwata? Nakan yi baƙin ciki idan na ga wasu yara tare da iyayensu.” Ernest yakan je kabarin babansa ya durkusa ya yi adduꞌa cewa: “Ya Allah ina so in san inda babana yake.” Shekaru 17 bayan mutuwar babansa, Ernest ya yarda Shaidun Jehobah su soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Da ya koyi cewa matattu ba su san kome ba, kamar barci mai zurfi ne suke yi kuma Littafi Mai Tsarki ya ce za a yi tashin matattu, hakan ya burge shi sosai. (M. Wa. 9:5, 10; A. M. 24:15) Yanzu ya samu amsar tambayoyin da suke damun sa a rai! Ya ji daɗin abin da ya koya sosai. Matarsa Rose ita ma ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ta so abin da take koya sosai. A shekara ta 1978 sun yi baftisma. Sun yi waꞌazi da ƙwazo sosai ga ꞌyan iyalinsu da abokansu da duk wanda ya so ya ji. A sakamakon haka, Ernest da matarsa Rose sun taimaka wa mutane sama da 70 su san Jehobah kuma su yi baftisma.
7. Me za mu yi idan muka so abin da muka koya daga Littafi Mai Tsarki sosai? (Luka 6:45)
7 Hakika idan muka so abin da muka koya daga Littafi Mai Tsarki za mu so mu gaya wa kowa game da shi. (Karanta Luka 6:45.) Za mu ji kamar mabiyan Yesu a ƙarni na farko da suka ce: “Ba za mu iya yin shiru a kan abin da muka ji, muka kuma gani ba.” (A. M. 4:20) Muna son abin da muka koya sosai har muna so kowa ya ji.
ƘAUNAR MUTANE TANA SA MU YI WAꞌAZI
8. Me ya sa muke so mu gaya wa mutane labari mai daɗi na Mulkin Allah? (Ka duba akwatin da ya ce, “ Ƙaunar Mutane Za Ta Sa Ka Almajirtar da Su.”) (Ka kuma duba hoton.)
8 Jehobah da Ɗansa Yesu suna ƙaunar mutane, kuma mu ma muna hakan. (K. Mag. 8:31; Yoh. 3:16) Muna jin tausayin waɗanda ‘ba su da Allah’ kuma ‘ba su da bege.’ (Afis. 2:12) Kamar suna cikin rami mai zurfi ne domin matsaloli da suke fuskanta, kuma labari mai daɗi na Mulkin Allah da muke waꞌazin sa, kamar igiya ne a hannunmu da za mu iya amfani da shi mu jawo su. Domin muna ƙaunar mutanen nan kuma muna jin tausayin su, muna yin duk abin da za mu iya yi don mu gaya musu labari mai daɗin nan. Labarin zai iya ba su bege, ya sa su yi rayuwa mai inganci a yau, kuma ya ba su damar samun “ainihin rai,” wato rai na har abada a sabuwar duniya.—1 Tim. 6:19.
9. Wane gargaɗi ne muke yi wa mutane, kuma me ya sa? (Ezekiyel 33:7, 8)
9 Ƙaunar da muke yi wa mutane tana sa mu yi musu gargaɗi cewa ƙarshen wannan duniyar ta yi kusa. (Karanta Ezekiyel 33:7, 8.) Muna tausaya wa danginmu da maƙwabtanmu da ba Shaidun Jehobah ba ne. Mutane da yawa suna yin rayuwa ba tare da sanin cewa za a yi “azaba mai zafi,” wato ƙunci mai girma “irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har zuwa yanzu, ba kuwa za a sāke yin irinta ba.” (Mat. 24:21) Muna so su san abin da zai faru a lokacin da Allah zai yi shariꞌa, wato cewa za a halaka addinan ƙarya, daga baya kuma a halaka muguwar duniyar nan a yaƙin Armageddon. (R. Yar. 16:14, 16; 17:16, 17; 19:11, 19, 20) Fatanmu shi ne mutane su ji gargaɗin nan da muke musu kuma su bauta ma Jehobah tare da mu. Amma me zai faru da ꞌyan iyalinmu da wasu da suka ƙi jin gargaɗinmu.
10. Me ya sa yake da muhimmanci sosai mu ci-gaba da gaya wa mutane cewa za a halaka Babila Babba?
10 Kamar yadda muka tattauna a talifin da ya gabata, wataƙila Jehobah zai ceci waɗanda suka tuba don sun ga an halaka Babila Babba. Saboda haka, yana da muhimmanci sosai mu ci-gaba da yi musu wannan gargaɗin. Ka tuna cewa: Sai mun gaya musu ne za su iya tuna da gargaɗin da muka yi musu. (Ka duba misalin da ke Ezekiyel 33:33.) Mai yiwuwa su tuna cewa mun yi musu wannan gargaɗi kuma hakan ya sa su soma bauta ma Jehobah tare da mu kafin lokaci ya kure. Alal misali, sai da aka yi “wata babbar rawar ƙasa” ne mai gadin kurkuku na birnin Filibi ya tuba. A zamaninmu ma, wataƙila waɗanda suka ƙi jin gargaɗin da muke musu a yau su tuba idan suka ga an halaka Babila Babba, don wannan halakar za ta jijjiga dukan duniya.—A. M. 16:25-34.
MUNA WAꞌAZI DON MUNA ƘAUNAR JEHOBAH DA SUNANSA
11. Ta yaya muke ba wa Jehobah ɗaukaka da girma da kuma iko? (Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11) (Ka kuma duba hotunan.)
11 Abu mafi muhimmanci da yake sa mu yi waꞌazin labari nan mai daɗi shi ne, muna ƙaunar Jehobah da sunansa. Muna ɗauka waꞌazi da muke yi a matsayin hanya mai muhimmanci na yabon Allahnmu da muke ƙauna. (Karanta Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11.) Mun yarda da dukan zuciyarmu cewa Jehobah ya cancanci ya karɓi ɗaukaka da girma da iko daga wurin amintattun bayinsa. Muna ɗaukaka da girmama shi yayin da muke nuna wa mutane tabbaci cewa shi ne ya “halicci kome da kome,” kuma muna a raye ne domin sa. Muna ba wa Jehobah iko, wato ikonmu, yayin da muke amfani da lokacinmu da ƙarfinmu da dukiyarmu wajen yi wa mutane waꞌazi iya gwargwadon ƙarfinmu. (Mat. 6:33; Luk. 13:24; Kol. 3:23) A taƙaice, muna jin daɗin gaya wa mutane game da Allahnmu da muke ƙauna. Muna kuma marmarin gaya wa mutane game da sunansa da abin da sunan yake nufi. Me ya sa?
12. Ta yaya muke tsarkake sunan Allah yayin da muke waꞌazi?
12 Ƙaunar da muke yi wa Jehobah tana sa mu tsarkake sunansa. (Mat. 6:9) Hakan yana nufi cewa muna so mu taimaka wa mutane su san cewa abubuwa da Shaiɗan ya faɗa game da Allah ƙarya ne. (Far. 3:1-5; Ayu. 2:4; Yoh. 8:44) Muna marmarin gaya wa mutane gaskiya game da Allah yayin da muke waꞌazi. Muna so kowa-da-kowa ya san cewa halin da ya fi nunawa shi ne ƙauna, yana yin mulki cikin adalci da gaskiya, kuma Mulkinsa zai kawo ƙarshen dukan matsaloli da muke fuskanta. Saꞌan nan kowa a duniya zai zauna cikin salama da kwanciyar hankali. (Zab. 37:10, 11, 29; 1 Yoh. 4:8) Idan muna gaya wa mutane abubuwan nan game da Jehobah, muna tsarkake sunansa ke nan. Kuma muna farin ciki don mun san aiki da ya kamata mu yi ke nan. Me ya sa muka ce hakan?
13. Me ya sa sanin cewa mu Shaidun Jehobah ne yake sa mu farin ciki sosai? (Ishaya 43:10-12)
13 Jehobah ya zaɓe mu mu zama ‘shaidunsa.’ (Karanta Ishaya 43:10-12.) A shekarun baya, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta tura wata wasiƙa da ta ce: “Gata mafi girma da kowannenmu zai iya samuwa shi ne zama Mashaidin Jehobah.” c Me ya sa? Ka yi laꞌakari da wannan misali. Idan kana bukatar wanda zai ba da shaida a kanka a kotu, ba shakka za ka zaɓi wanda ka yarda da shi kuma yana da suna mai kyau, domin a yarda da shaidarsa. Jehobah ya zaɓe mu mu zama Shaidunsa. Hakan ya nuna cewa ya san mu sosai, kuma ya tabbata cewa za mu ba da shaida mai kyau cewa shi kaɗai ne Allah na gaskiya. Muna farin ciki sosai don wannan gata da ya ba mu, shi ya sa muke amfani da kowane zarafi don mu gaya wa mutane sunansa, kuma mu nuna cewa abubuwan da Shaiɗan ya faɗa game da shi ƙarya ne. Ta haka, muna yin aikinmu a matsayin Shaidun Jehobah!—Zab. 83:18; Rom. 10:13-15.
ZA MU CI-GABA DA YIN WAꞌAZI HAR ƘARSHE
14. Waɗanne abubuwa masu ban shaꞌawa ne za su iya faruwa a nan gaba?
14 Muna farin cikin sanin abubuwa masu ban shaꞌawa da za su iya faruwa a nan gaba! Fatanmu shi ne mutane da yawa su soma bauta ma Jehobah tare da mu kafin a soma ƙunci mai girma. Ƙari ga haka, sanin cewa mai yiwuwa a lokacin ƙunci mai girma ma, mutane da yawa za su tuba kuma su soma bauta ma Jehobah tare da mu, yana sa mu farin ciki!—A. M. 13:48.
15-16. Mene ne za mu ci-gaba da yi, kuma har yaushe?
15 A yanzu dai, muna da sauran aiki. Muna da gatan yin waꞌazin Mulkin Allah a dukan duniya. Wannan aiki mai muhimmanci ne da ba za a sake yin sa ba. Yayin da muke waꞌazin nan, bari mu ci-gaba da yi wa mutane gargaɗi game da abin da zai faru nan ba da daɗewa ba. Mutane suna bukatar su san cewa ƙarshen wannan muguwar duniya ya yi kusa. Saꞌan nan idan ƙarshen ya zo, za su san cewa gargaɗin nan da muka yi musu, daga wurin Jehobah ne.—Ezek. 38:23.
16 Don haka, mene ne ya kamata mu ƙuduri niyyar yi? Ya kamata mu ci-gaba da yin waꞌazi da niyya, da gaggawa, da ƙwazo, har sai Jehobah ya ce “ya isa,” domin muna son labari mai daɗin, muna ƙaunar mutane, mafi muhimmanci ma, muna ƙaunar Jehobah da sunansa.
WAƘA TA 54 ‘Wannan Ita Ce Hanyar Rai’
a An yi taron a ranar 7 ga Oktoba, 2023, a Majamiꞌar Babban Taro na birnin Newburgh a jihar New York, na ƙasar Amurka. Daga baya, an nuna Kashi na 1 na taron a shirin Tashar JW na Nuwamba 2023, Kashi na 2 kuma a Janairu 2024.
b Ka duba talifin da ya ce, “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane—Yadda Littafi Mai Tsarki Ya Amsa Tambayoyina Ya Burge Ni,” da ke Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Fabrairu, 2015.
c Ka duba littafin nan, 2007 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafi na 3.