Abin da Zai Taimaka Maka Idan Ka Canja Ikilisiya
KA TAƁA ƙaura kuma ka canja ikilisiya? In haka ne, mai yiwuwa za ka yarda da abin da wani mai suna Jean-Charles ya faɗa, ya ce: “Idan ka ƙaura, ba zai yi ma kai da iyalinka sauƙi ku ci-gaba da yin ayyukan ibada ba yayin da kuke ƙoƙarin sabawa da sabuwar ikilisiyar.” Idan mutum ya ƙaura, mai yiwuwa ya soma neman aiki, ko gida ko kuma makarantar da zai sa yaransa. Ƙari ga haka, zai yi ƙoƙari ya saba da sabon yanayi, da alꞌadar mutanen, da kuma yin waꞌazi a yankin.
Ɗanꞌuwa Nicolas da matarsa Céline kuma sun fuskanci wata matsala dabam. Reshen ofishinmu da ke Faransa ya gaya musu su ƙaura zuwa wata ikilisiya. Sun ce: “Da muka ƙaura mun yi farin ciki sosai, amma daga baya mun soma kewar abokanmu, domin ba mu gama sabawa da ꞌyanꞌuwa da ke sabuwar ikilisiyarmu ba.” a Da yake ƙaura yana tattare da matsaloli, me zai taimaka maka? Ta yaya ꞌyanꞌuwa za su taimaka? Ta yaya za ka amfana kuma ka taimaka wa ꞌyanꞌuwa da ke sabuwar ikilisiyarku?
ABUBUWA HUƊU DA ZA SU TAIMAKA MAKA
1. Ka dogara ga Jehobah. (Zab. 37:5) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Kazumi daga ƙasar Japan ta yi shekaru 20 a wata ikilisiya, amma da aiki ya kai maigidanta wani wuri dabam, ta bar ikilisiyar. Ta yaya ta ‘danƙa wa Yahweh hanyar rayuwarta’? Ta ce: “Na yi adduꞌa sosai ga Jehobah kuma na gaya masa kome. Na gaya masa tsoron da nake ji, da yadda na kaɗaita. A duk lokacin da na yi adduꞌa ga Jehobah, yakan ba ni ƙarfin jimrewa.”
Me zai taimaka maka ka ƙara dogara ga Jehobah? Ga wani misali: Idan ba a yi wa shuka ban-ruwa, kuma ƙasar babu taki, shukar ba za ta yi girma da kyau ba. Haka ma, muna bukatar mu yi abubuwan da za su sa bangaskiyarmu ta ƙaru. Ɗanꞌuwa Nicolas da muka ambata a baya ya gano cewa, yin tunani mai zurfi a kan labaran mutane da suka yi sadaukarwa sosai don su yi nufin Allah, ya sa ya ƙara dogara ga Jehobah. Mutanen da ya yi tunani a kansu su ne Ibrahim, da Yesu, da kuma Bulus. Idan ka ci-gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki, hakan zai taimaka maka ka
jimre da matsalolin rayuwa, kuma za ka koyi abubuwa da za ka yi amfani da su ka ƙarfafa ꞌyanꞌuwa a sabuwar ikilisiyarku.2. Ka daina kwatanta sabuwar ikilisiyarku da ta dā. (M. Wa. 7:10) Da Ɗanꞌuwa Jules ya ƙaura daga ƙasar Benin zuwa Amurka, ya yi mishi wuya sosai ya saba da alꞌadar mutanen. Ya ce: “Na zata cewa da zuwana za mu shaƙu da ꞌyanꞌuwan, kuma kowa zai riƙa tambaya na abubuwa da yawa game da rayuwata.” Ya faɗi haka ne, domin abin da ya saba gani ke nan a ƙasar Benin. Amma da hakan bai faru ba, sai ya soma janye kansa daga ꞌyanꞌuwan. Da Ɗanꞌuwa Jules ya ƙara sanin ꞌyanꞌuwan, sai ya canja raꞌayinsa. Ya ce: “Yanzu na gano cewa ꞌyanꞌuwa a koꞌina a duniya ɗaya ne. Sai dai yadda muke yin abubuwa ne ya bambanta. Don haka, kada mu ce lallai sai mutane sun zama kamar mu.” Kar ka gwada sabuwar ikilisiyarku da ta dā. Wata majagaba mai suna Anne-Lise ta ce: “Da na ƙaura, ban sa rai cewa abubuwa za su kasance daidai yadda suke a ikilisiyarmu ta dā ba. Don haka, na yi niyyar koyan sabbin abubuwa.”
Ya kamata dattawa da suka ƙaura su ma su guji kwatanta sabuwar ikilisiyarsu da wadda suka baro, domin za a iya yin abu ɗaya a hanyoyi dabam-dabam. Kafin ka ce a canja yadda ake yin wani abu, zai dace ka san dalilin da ya sa ake yin sa haka. (M. Wa. 3:1, 7b) Maimakon ka riƙa nacewa a kan raꞌayinka, idan kana yin abubuwa yadda ya dace, ꞌyanꞌuwa za su bi misalinka.—2 Kor. 1:24.
3. Ka riƙa yin abubuwa tare da ꞌyanꞌuwan. (Filib. 1:27) Yin ƙaura bai da sauƙi kuma yana cin lokaci. Duk da haka, yana da muhimmanci ka riƙa zuwa taro a Majamiꞌar Mulki da zarar ka ƙaura. Domin idan ꞌyanꞌuwan da ke sabuwar ikilisiyarku ba sa yawan ganin ka, zai yi musu wuya su taimake ka. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Lucinda ta tuna abin da ya faru lokacin da ita da ꞌyan matanta biyu suka ƙaura zuwa wani babban birni a Afrika ta Kudu. Ta ce: “Abokaina sun shawarce ni in riƙa yin abubuwa tare da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya, kamar yin waꞌazi da yin kalami a taro. Mun kuma yarda a riƙa yin taron fita waꞌazi a gidanmu.”
Yin “fama tare” da ꞌyanꞌuwa da ke sabuwar ikilisiyarku wajen yin ayyukan ibada, zai ƙarfafa ku duka. Dattawa sun ƙarfafa ꞌyarꞌuwa Anne-Lise da muka ambata a baya cewa ta yi ƙoƙari ta yi waꞌazi tare da kowa a ikilisiyarsu. Ta yaya yin hakan ya amfane ta? Ta ce: “Hakan ya sa na yi saurin sabawa da kowa a ikilisiya.” Wani abu kuma da zai nuna cewa ka ɗauki ikilisiyar a matsayin taka shi ne, idan kana bin ꞌyanꞌuwa yin shara ko gyare-gyare a Majami’ar Mulki. Idan ka ci-gaba da yin abubuwa tare da ꞌyanꞌuwa a sabuwar ikilisiyarku, ꞌyanꞌuwan za su saba da kai, kai kuma za ka ɗauke su a matsayin iyalinka.
4. Ka yi sabbin abokai. (2 Kor. 6:11-13) Hanya mafi sauƙi da za ka yi sabbin abokai ita ce, ka nuna cewa ka damu da mutane. Don haka, kafin taro da bayan taro, ka ɗau lokaci ka yi hira da ꞌyanꞌuwa don ka san su da kyau. Ka yi ƙoƙarin sanin sunayensu. Idan kana tuna sunayen mutane kuma kana yin faraꞌa, mutane za su so su kusace ka.
Ka nuna ma ꞌyanꞌuwan ainihin halinka, kada ka yi musu ɓoye-ɓoye. Ka bi halin ꞌyarꞌuwa Lucinda. Ta ce: “Yanzu muna da abokai da yawa, domin muna gayyatar ꞌyanꞌuwa su zo gidanmu.”
“KU KARƁI JUNA HANNU BIYU-BIYU”
Idan wasu suka shiga Majami’ar Mulki kuma suka ga mutane da yawa da ba su san su ba, sukan ji tsoro. Ta yaya za ka taimaka ma waɗanda suka zo ikilisiyarku sabo-sabo? Manzo Bulus ya ce: ‘Mu karɓi juna hannu biyu-biyu kamar yadda Almasihu ya karɓe mu.’ (Rom. 15:7) Dattawa za su iya karɓar irin ꞌyanꞌuwan nan hannu bi-biyu idan suna yin koyi da misalin Yesu. (Ka duba akwatin nan, “ Abin da Zai Taimaka don Ƙaurar Ta Zo da Sauƙi.”) Amma ba dattawa ba ne kawai, kowa a ikilisiya har da yara za su iya sa ꞌyanꞌuwan nan su ji cewa an marabce su.
Karɓar mutane hannu bi-biyu ya ƙunshi gayyatarsu zuwa gidanmu, da kuma taimaka musu a wasu hanyoyi. Alal misali, wata ꞌyarꞌuwa ta yarda ta nuna ma wata da ta ƙaura zuwa yankinsu yadda ake shiga mota, da wasu wurare a garin, da dai sauransu. Ta ji daɗin wannan taimako da ꞌyarꞌuwar ta yi mata, kuma ya sa ta yi saurin sabawa da wurin.
DAMA CE NA SAMUN CI-GABA
Za mu iya kwatanta abin da yake faruwa lokacin ƙaura da yadda bishiya take girma. Idan ana so bishiya ta miƙe kuma ta yi tsayi sosai, akan yanke wasu rassanta a yar. Haka ma, idan muka je sabuwar ikilisiya kuma muna so mu samu ci-gaba, muna bukatar mu yar da duk wani tunani da zai hana mu samun ci-gaba a ibadarmu. Ɗanꞌuwa Nicolas da Céline da muka ambata a baya sun ce: “Ƙaura zai iya koya wa mutum abubuwa da dama. Da muka ƙaura, sai da muka koyi sabbin halaye ne muka iya sabawa da mutanen
da kuma wurin.” Ɗanꞌuwa Jean-Charles shi ma da aka ambata a baya ya ce: “Ƙaurar ta sa yaranmu sun samu ci-gaba sosai. Bayan ꞌyan watanni, ꞌyarmu ta soma yin aiki a taron tsakiyar mako, ɗanmu kuma ya zama mai shela da bai yi baftisma ba.”Idan kana so ka ƙaura, wataƙila kana so ka je inda ake bukatar masu shela, amma yanayinka ya hana ka fa? Har ila za ka iya bin shawarwarin da ke talifin nan a ikilisiyar da kake. Hakan zai sa ka ƙara jin daɗin kasancewa a ikilisiyar. Ka ci-gaba da dogara ga Jehobah, kuma ka riƙa yin ayyukan ibada sosai tare da ꞌyanꞌuwa. Alal misali, ka shirya yadda za ka riƙa yin waꞌazi tare da ꞌyanꞌuwa dabam-dabam, ka yi sabbin abokai, kuma ka ƙara kusantar abokan da kake da su a yanzu. Idan akwai waɗanda suke da bukata ko waɗanda ba su daɗe da zuwa ikilisiyarku ba, ka taimaka musu idan zai yiwu. Yesu ya ce ƙauna ce za ta nuna cewa mu Kiristoci na gaske ne. Don haka, idan kana taimaka wa ꞌyanꞌuwa, za ka ƙara kusantar Jehobah. (Yoh. 13:35) Ka kasance da tabbaci cewa irin waɗannan ayyuka suna “faranta wa Allah rai.”—Ibran. 13:16.
Duk da cewa sabawa da sabuwar ikilisiya bai da sauƙi, ꞌyanꞌuwa da yawa sun yi nasara, kuma kai ma za ka iya! ꞌYarꞌuwa Anne-Lise ta ce: “Zuwa sabuwar ikilisiya ta taimaka min in ƙara ƙaunar ꞌyanꞌuwa.” ꞌYarꞌuwa Kazumi ta gano cewa zuwa sabuwar ikilisiya zai iya sa mutum ya daɗa ganin yadda Jehobah yake taimaka masa. Ɗanꞌuwa Jules kuma ya ce: “Yanzu da na yi sabbin abokai, ina ji kamar ina tare da ꞌyan iyalina ne. Yanzu ina ƙaunar ꞌyanꞌuwa da ke sabuwar ikilisiyarmu sosai, har ba na so wani abu ya raɓa ni da su.”
a Don samun shawara a kan yadda za ka jimre idan kana kewar mutanen gida, ka karanta talifin nan, “Coping With Homesickness in Godꞌs Service,” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Mayu, 1994.