Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 29

Ka Yi Farin Ciki don Ci-gaba da Kake Samu a Ibadarka!

Ka Yi Farin Ciki don Ci-gaba da Kake Samu a Ibadarka!

“Bari kowa ya . . . [yi] taƙama da abin da ya yi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba.”​—GAL. 6:4.

WAƘA TA 34 Mu Zama Masu Aminci

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Me ya sa Jehobah ba ya gwada mu da wasu?

JEHOBAH ba ya so kome da kome ya zama iri ɗaya. Mun san hakan ne domin Jehobah ya yi shuke-shuke da dabbobi da kuma ’yan Adam dabam-dabam. Kowannenmu ya fita dabam da ɗan’uwansa. Don haka, Jehobah ba ya gwada mu da wasu. Ya san ko kai wane irin mutum ne. (1 Sam. 16:7) Ya san abin da za ka iya yi, da wanda ba za ka iya yi ba, da kuma yadda aka yi renon ka. Kuma ba ya bukatar ka yi abin da ya fi ƙarfinka. Muna bukatar mu yi koyi da Jehobah ta wajen ɗaukan kanmu yadda yake ɗaukanmu. Hakan zai sa mu kasance da ra’ayin da ya dace, ba za mu rena kanmu ba kuma ba za mu ɗauki kanmu fiye da wasu ba.​—Rom. 12:3.

2. Me ya sa bai da kyau mu gwada kanmu da wasu?

2 Za mu iya bin misali mai kyau na ’yan’uwanmu. Alal misali, wataƙila akwai wani ɗan’uwa ko kuma ’yar’uwa da ta iya wa’azi sosai. (Ibran. 13:7) Za mu iya koyan darasi daga ɗan’uwan ko ’yar’uwar a kan yadda za mu inganta wa’azinmu. (Filib. 3:17) Akwai bambanci tsakanin yin koyi da misalin mutum da kuma gwada kanka da mutumin. Gwada kanka da wani zai iya sa ka soma kishi ko ka yi sanyin gwiwa ko kuma ka ɗauka cewa ba ka da daraja. Kamar yadda muka koya a talifin da ya gabata, yin ƙoƙari mu nuna cewa mun fi wasu zai iya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Don haka, Jehobah ya gargaɗe mu cewa: “Bari kowa ya gwada aikinsa ya gani. Idan ya yi kyau, sa’an nan zai iya taƙama da abin da ya yi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba.”​—Gal. 6:4.

3. Wane ci gaba ne ka samu a ibadarka ga Jehobah da ke sa ka farin ciki?

3 Jehobah yana so ka yi farin ciki don ci gaba da kake samu a ibadarka! Alal misali, idan ka riga ka yi baftisma ya kamata ka yi farin ciki domin ka cim ma maƙasudinka! Kai ne ka yanke shawarar yin hakan da kanka. Ka yi hakan ne domin kana ƙaunar Jehobah. Ka yi tunanin ci gaba da ka samu tun daga lokacin. Alal misali, shin kana jin daɗin karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin nazari fiye da dā? Yanzu kana addu’a daga zuciyarka sosai? (Zab. 141:2) Tattaunawa da mutane a wa’azi da kuma yin amfani da abubuwan da muke wa’azi da su ya soma yi maka sauƙi? Idan kana da iyali, Jehobah ya taimaka maka ka zama miji ko baba nagari? Za ka iya yin farin ciki domin ka sami wannan ci gaban.

4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 Za mu iya taimaka wa ’yan’uwa su yi farin ciki don ci gaba da suke samu a bautarsu ga Jehobah. Kuma muna iya taimaka musu su guji gwada kansu da wasu. A wannan talifin, za mu ga yadda iyaye za su iya taimaka wa yaransu, da yadda ma’aurata za su iya taimaka wa juna da kuma yadda dattawa za su iya taimaka wa ’yan’uwa. A ƙarshe, za mu tattauna ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su iya taimaka mana mu kafa maƙasudai da za mu iya cim ma bisa ga baiwarmu da kuma yanayinmu.

ABIN DA IYAYE DA KUMA MA’AURATA ZA SU IYA YI

Iyaye, ku nuna wa kowanne cikin yaranku cewa kuna farin ciki da abin kirki da yake yi (Ka duba sakin layi na 5-6) *

5. Kamar yadda Afisawa 6:4 ta nuna, me ya kamata iyaye su guji yi?

5 Iyaye suna bukatar su guji gwada yaransu da wasu yara, ko kuma su sa yaran yin abin da ya fi ƙarfinsu. Idan iyaye suna yin hakan, suna iya sa yaran yin sanyin gwiwa. (Karanta Afisawa 6:4.) Wata ’yar’uwa mai suna Sachiko * ta ce: “Malamaina a makaranta suna so in fi sauran ’yan ajinmu. Ƙari ga haka, mahaifiyata tana so in yi ƙoƙari a makaranta don malamaina da mahaifina da ba Shaidu ba su canja ra’ayinsu game da Shaidun Jehobah. Tana son in riƙa cin dukan jarrabawa a makaranta, amma ba yadda zan iya yin hakan. Ko da yake na daɗe da gama makaranta, a wasu lokuta, ina tunanin ko Jehobah yana farin ciki da abin da nake yi, duk da cewa ina yin iya ƙoƙarina.”

6. Mene ne iyaye za su iya koya daga Zabura 131:​1, 2?

6 Wani darasi mai kyau da iyaye za su iya koya yana Zabura 131:1, 2. (Karanta.) Sarki Dauda ya ce bai “damu da manyan abubuwa” ko kuma yin abubuwan da suka fi ƙarfinsa ba. Da yake shi mai sauƙin kai ne kuma ya san kasawarsa, hakan ya “kwantar” masa da hankali. Mene ne iyaye za su iya koya daga furucin Dauda? Wani abin da zai taimaka ma iyaye su kasance da sauƙin kai shi ne sanin kasawarsu da kuma kasawar yaransu. Iyaye za su iya taimaka wa yaransu su ga cewa suna da daraja ta wajen sanin abin da yaran za su iya yi da abin da ba za su iya yi ba, da kuma taimaka musu su kafa maƙasudin da za su iya cim ma. Wata ’yar’uwa mai suna Marina ta ce: “Mahaifiyata ba ta taɓa gwada ni da ’yan’uwana uku ko kuma wasu yara ba. Ta koya mini cewa dukanmu muna da baiwa dabam-dabam, kuma Jehobah yana daraja kowannenmu. Don haka, ba na gwada kaina da wasu.”

7-8. Ta yaya magidanci zai iya daraja matarsa?

7 Kirista yana bukatar ya riƙa daraja matarsa. (1 Bit. 3:7) Hakan ya ƙunshi kula da ita da nuna mata cewa yana ƙaunar ta. Ba zai ce ta yi abin da ba za ta iya yi ba. Kuma ba zai gwada ta da wasu mata ba. Idan ya yi hakan, yaya matarsa za ta ji? Mijin wata ’yar’uwa mai suna Rosa da ba Mashaidi ba ne yana yawan gwada ta wasu mata. Kalmominsa marasa daɗi sun sa Rosa ta rena kanta kuma ta ɗauka cewa ba mai ƙaunar ta. Ta ce: “Na bukaci in riƙa tunasar da kaina cewa Jehobah yana ƙauna ta.” Akasin haka, Kirista yana bukatar ya riƙa daraja matarsa. Ya san cewa yin hakan zai kyautata dangantakarsa da matarsa da kuma Jehobah. *

8 Magidancin da yake daraja matarsa zai riƙa yaba mata kuma zai nuna mata cewa yana ƙaunar ta. (K. Mag. 31:28) Abin da mijin Katerina wadda aka ambata a talifin da ya gabata ya yi ke nan don ya taimake mata ta daina ganin kamar ba ta da daraja. A lokacin da take ƙarama, mahaifiyarta tana yawan ƙasƙantar da ita kuma tana gwada ta da wasu yara, har da ƙawayenta. Saboda haka, Katerina ta soma gwada kanta da wasu, kuma ta ci gaba da yin hakan har a lokacin da ta zama Mashaidiyar Jehobah! Amma mijinta ya taimaka mata ta daina yin hakan kuma ta kasance da ra’ayin da ya dace game da kanta. Ta ce: “Ya nuna yana ƙauna ta, yana yaba mini domin abubuwa masu kyau da na yi kuma yana addu’a a madadina. Ya tuna mini halayen Jehobah masu kyau, kuma ya taimaka mini in daina tunanin da bai dace ba.”

ABIN DA DATTAWA DA ’YAN’UWA ZA SU IYA YI

9-10. Ta yaya wasu dattawa suka taimaka ma wata ’yar’uwa da take gwada kanta da wasu ta daina yin hakan?

9 Ta yaya dattawa za su iya taimaka ma waɗanda suke yawan gwada kansu da wasu? Ka yi la’akari da misalin wata ’yar’uwa mai suna Hanuni wadda a lokacin da take ƙarama, da wuya a yaba mata. Ta ce: “Hakan ya sa na zama mai jin kunya kuma na soma tunanin cewa wasu yara sun fi ni. Na soma gwada kaina da wasu tun ina ƙarama.” Bayan Hanuni ta soma bauta wa Jehobah kuma ta soma hidimar majagaba, ta ci gaba da gwada kanta da wasu. Hakan ya sa ta soma tunanin cewa ba ta da amfani a ikilisiya. Amma yanzu, tana farin cikin yin hidimar majagaba. Mene ne ya taimaka mata ta canja halinta?

10 Hanuni ta ce wasu dattawa sun taimaka mata. Sun gaya mata cewa tana da amfani a ikilisiya kuma sun yaba mata don bangaskiyarta. Ta ce: “Akwai wasu lokuta da dattawan suka gaya mini in ƙarfafa wasu ’yan’uwa mata da suke bukatar taimako. Wannan aikin ya sa na ga cewa ina da amfani. Na tuna lokacin da dattawa suka gode mini domin yadda na ƙarfafa wasu ’yan’uwa mata. Sai suka karanta mini 1 Tasalonikawa 1:2, 3. Hakan ya sa ni farin ciki sosai! Domin waɗannan dattawa masu ƙauna, yanzu na san cewa ina da amfani a ikilisiya.”

11. Ta yaya za mu taimaka wa “waɗanda an karya musu ƙarfin gwiwa” kamar yadda Zabura 34:18 ta ambata?

11 Karanta Zabura 34:18. Jehobah ya damu sosai da “waɗanda an karya musu ƙarfin gwiwa.” Dukanmu za mu iya ƙarfafa waɗannan ’yan’uwa, ba dattawa kaɗai ba. Hanya ɗaya da za mu iya ƙarfafa su ita ce ta wajen nuna cewa mun damu da su sosai. Jehobah yana so mu nuna musu yadda yake ƙaunar tumakinsa. (Kol. 3:12) Ƙari ga haka, za mu iya taimaka wa ’yan’uwanmu idan muna nuna sauƙin kai kuma mun san kasawarmu. Bai kamata mu mai da hankali ga kanmu har mu sa mutane su soma kishi ba. A maimakon haka, za mu yi amfani da iliminmu da kuma baiwarmu don mu ƙarfafa juna.​—1 Bit. 4:10, 11.

Mabiyan Yesu sun kusace shi domin bai nuna cewa ya fi su matsayi ba. Ya ji daɗin yin cuɗanya da abokansa (Ka duba sakin layi na 12)

12. Me ya sa talakawa suka ji daɗin kusantar Yesu? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

12 Za mu iya yin koyi da Yesu ta wajen bi da mutane yadda ya bi da mabiyansa. Shi ne mutum mafi girma da ya taɓa rayuwa a duniya. Duk da haka, shi “mai tawali’u ne, mai sauƙin kai.” (Mat. 11:​28-30) Bai yi fahariya domin ilimin da yake da shi ba ko kuma abubuwan da ya sani ba. Sa’ad da yake koyar da mutane, ya yi magana a hanyar da za su fahimta kuma ya yi amfani da kwatanci masu sauƙi. (Luk. 10:21) Yesu ba mai girman kai kamar limaman addinai ba ne. Ya sa mutane su ga cewa suna da daraja a wurin Allah. (Yoh. 6:37) Yesu ya daraja talakawa.

13. Ta yaya yadda Yesu ya bi da mabiyansa ya nuna cewa shi mai alheri da ƙauna ne?

13 Yadda Yesu ya bi da mabiyansa ya nuna cewa shi mai alheri ne da kuma ƙauna. Ya san cewa suna da baiwa dabam-dabam kuma yanayinsu ya bambanta. Don haka, ya san cewa ba za su iya yin ayyuka iri ɗaya ba, kuma yadda suke wa’azi ba zai zama iri ɗaya ba. Duk da haka, ya yi farin ciki domin dukansu sun yi iya ƙoƙarinsu. Yesu ya nuna hakan ta kwatancin zinariya da ya bayar. A kwatancin, maigidan ya ba kowane bawa aiki “daidai da ƙarfinsa.” Ɗaya daga cikin bayi biyu masu hikimar, ya sami riba fiye da ɗayan. Amma maigidan ya yaba wa su biyun da kalmomi iri ɗaya, ya ce: “Madalla, bawan kirki, mai aminci!”​—Mat. 25:14-23.

14. Ta yaya za mu yi koyi da yadda Yesu ya bi da mutane?

14 Yesu yana nuna mana alheri da kuma ƙauna. Ya san cewa dukanmu muna da baiwa dabam-dabam kuma yanayinmu ya bambanta, amma yana farin ciki idan muka yi iya ƙoƙarinmu. Zai dace mu bi da ’yan’uwanmu kamar yadda Yesu yake yi. Kada mu sa wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta ji kamar ba ta da amfani, ko kuma mu kunyatar da su domin ba za su iya yin abin da wasu ’yan’uwa suke yi ba. A maimakon haka, mu nemi damar yaba wa ’yan’uwanmu domin ƙoƙarin da suke yi a bautarsu ga Jehobah.

KA KAFA MAƘASUDIN DA ZA KA IYA CIM MA

Za ka yi farin ciki idan ka kafa maƙasudai da za ka iya cim ma kuma ka yi su (Ka duba sakin layi na 15-16) *

15-16. Ta yaya wata ’yar’uwa ta amfana domin ta kafa maƙasudan da za ta iya cim ma?

15 Rayuwarmu za ta kasance da ma’ana, idan mun kafa maƙasudai da muke so mu cim ma a hidimar Jehobah. Amma muna bukatar mu kafa maƙasudan da za mu iya cim ma. Ba sai mun kafa maƙasudai irin na wasu ba. Idan muka yi hakan, ba za mu iya cim ma maƙasudin ba, kuma hakan zai iya sa mu sanyin gwiwa. (Luk. 14:28) Ka yi la’akari da misalin wata ’yar’uwa majagaba mai suna Midori.

16 A lokacin da Midori take ƙarama, mahaifinta da ba ya bauta wa Jehobah yana kunyatar da ita ta wajen gaya mata cewa ’yan’uwanta da abokan ajinta sun fi ta. Ta ce: “Hakan ya sa na ɗauka cewa ba ni da amfani.” Amma da ta girma, Midori ta daina ɗaukan kanta a matsayin marar daraja. Ta ce: “Ina karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana don in sami kwanciyar rai, ta hakan na gane cewa Jehobah yana ƙauna ta.” Ƙari ga haka, ta kafa maƙasudan da za ta iya cim ma, kuma ta roƙi Jehobah ya taimaka mata ta cim ma waɗannan maƙasudan. A sakamakon haka, Midori tana farin ciki domin ci gaba da take samu a hidimarta ga Jehobah.

KA CI GABA DA YIN IYA ƘOƘARINKA A HIDIMARKA GA JEHOBAH

17. Ta yaya za mu ci gaba da ‘sabunta tunaninmu da hankalinmu,’ kuma wane sakamako za mu samu?

17 Yana iya ɗaukan lokaci kafin mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kanmu. Don haka, Jehobah ya gargaɗe mu cewa mu ci gaba da ‘sabunta tunaninmu da hankalinmu.’ (Afis. 4:23, 24) Abin da zai taimaka mana mu iya yin hakan shi ne, yin addu’a da nazarin Kalmar Allah da kuma yin bimbini a kan abin da muka karanta. Ka ci gaba da yin waɗannan abubuwa kuma ka roƙi Jehobah ya taimaka maka. Ruhunsa mai tsarki zai taimaka maka ka daina gwada kanka da wasu. Ƙari ga haka, Jehobah zai taimaka maka ka san ko ka soma kishi ko girman kai, kuma zai taimake ka ka kawar da waɗannan halayen nan da nan.

18. Ta yaya kalmomin da ke 2 Tarihi 6:​29, 30 za su ƙarfafa ka?

18 Karanta 2 Tarihi 6:29, 30. Jehobah ya san abin da ke zuciyarmu. Ya san cewa muna yin iya ƙoƙarinmu don mu guji halayen mutanen duniya kuma ya san muna fama da ajizancinmu. Sa’ad da Jehobah ya ga irin ƙoƙarin da muke yi don mu guji waɗannan abubuwan, yana ƙara ƙaunar mu.

19. Ta yaya Jehobah ya bayyana yadda yake ƙaunar mu?

19 Jehobah ya yi amfani da misalin mahaifiya da jaririnta don ya kwatanta yadda ya damu da mu. (Isha. 49:15) Ka yi la’akari da misalin wata mahaifiya mai suna Rachel. Ta ce: “Na haifi ’yata mai suna Stephanie kafin lokacin da ya kamata in haife ta. Ta fito ’yar mitsitsi. A wata na farko da ta yi a cikin kwalba, likitan ya amince in riƙa ɗaukanta kowace rana. Hakan ya sa ni da ’yata mun kusaci juna. Yanzu shekararta shida kuma yara tsararta sun fi ta girma. Duk da haka, ina ƙaunar ta sosai domin ta yi iya ƙoƙarinta ta rayu, kuma tana sa ni farin ciki sosai!” Haka ma idan Jehobah ya ga muna iya ƙoƙarinmu don mu bauta masa, yana ƙaunar mu sosai, kuma hakan yana sa mu farin ciki!

20. Me ya sa bayin Jehobah suke da dalilin yin farin ciki?

20 Kana da daraja a gaban Jehobah domin kana bauta masa, kuma babu na biyunka. Jehobah ya jawo ka wurinsa ba domin ka fi wasu ba, amma ya jawo ka domin ya ga cewa kai mai sauƙin kai ne kuma kana shirye ka koya daga wurin sa kuma ka yi canji. (Zab. 25:9) Ka tabbata cewa yana farin ciki domin yadda kake yin iya ƙoƙarinka don ka bauta masa. Yadda kake jimrewa da kuma nuna aminci, tabbaci ne cewa kana da zuciyar kirki. (Luk. 8:15) Saboda haka, ka ci gaba da yin iya ƙoƙarinka a bautar Jehobah. Ta hakan, za ka yi farin ciki don ‘abin da ka yi da kanka.’

WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka

^ sakin layi na 5 Jehobah ba ya gwada mu da wasu. Amma za mu iya gwada kanmu da wasu kuma mu soma tunanin cewa sun fi mu. A wannan talifin, za mu tattauna dalilin da ya sa bai dace mu gwada kanmu da wasu ba. Ƙari ga haka, za mu tattauna yadda za mu iya taimaka wa iyalinmu da kuma ’yan’uwa a ikilisiya su riƙa ɗaukan kansu yadda Jehobah yake ɗaukansu.

^ sakin layi na 5 An canja wasu sunayen.

^ sakin layi na 7 Ko da yake abubuwan da aka tattauna game da mazaje ne, da yawa daga cikin ƙa’idodin sun shafi mata ma.

^ sakin layi na 58 BAYANI A KAN HOTUNA: Sa’ad da wata iyali ke ibada tare, iyayen suna farin ciki don dabbar da kowanne cikin yaran ya yi don ya saka a cikin jirgin Nuhu.

^ sakin layi na 62 BAYANI A KAN HOTUNA: Wata mahaifiya da ita kaɗai ce take renon ɗanta, ta shirya yadda za ta yi hidimar majagaba na ɗan lokaci, kuma ta yi farin ciki sa’ad da ta cim ma maƙasudinta.