Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ku Sa Jehobah Ya Inganta Kuma Ya Kāre Aurenku

Ku Sa Jehobah Ya Inganta Kuma Ya Kāre Aurenku

Idan ba Ubangiji ya tsare birnin ba, rashin barcin mai-tsaro banza ne.”ZAB. 127:1b.

1, 2. (a) Me ya sa wasu Isra’ilawa 24,000 suka rasa gatan shiga ƙasar alkawari? (b) Me ya sa wannan labarin yake da muhimmanci a gare mu?

JIM kaɗan bayan al’ummar Isra’ila ta shiga Ƙasar Alkawari, sai dubban mazajen suka yi “fasikanci da ’yan matan Moab.” A sakamakon haka, Jehobah ya halaka mutane 24,000. Hakan abin baƙin ciki ne don suna gab da samun gadonsu shi ne sun faɗa wa wannan jarabar. Saboda haka, suka rasa gatan shiga ƙasar alkawari.—Lit. Lis. 25:1-5, 9.

2 An rubuta wannan labari mai ban tausayi ne “domin gargaɗi garemu, mu waɗanda matuƙan zamanu sun zo a kanmu.” (1 Kor. 10:6-11) Yanzu da “kwanaki na ƙarshe” suna ƙurewa, bayin Allah suna gab da shiga sabuwar duniya. (2 Tim. 3:1; 2 Bit. 3:13) Abin baƙin ciki shi ne wasu bayin Jehobah ba sa hattara. Sun yi lalata kuma hakan ya haifar da mummunar sakamako. Idan ba su tuba ba, za su rasa rai na har abada.

3. Me ya sa ma’aurata suke bukatar ja-gora da kuma kāriya daga Jehobah? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

3 Domin yadda lalata ta zama ruwan dare a yau, ma’aurata suna bukatar ja-gora da kuma kāriya daga Jehobah don kada ƙoƙarin da suke yi don su kāre aurensu ya bi ruwa. (Karanta Zabura 127:1.) Za mu tattauna yadda abubuwa biyar za su taimaka wa ma’aurata su ƙarfafa aurensu, wato kiyaye zuciya, yin abota na kud da kud da Allah, kasancewa da sabon hali, tattaunawar da ta dace da kuma biya wa juna bukata.

KU KIYAYE ZUCIYARKU

4. Wane yanayi ne ya sa wasu Kiristoci yin abin da bai da kyau?

4 Wane yanayi ne zai kai Kirista ga yin lalata? Mugun yanayin da yake kai ga yin lalata yakan soma da kallo ne. Yesu ya ce: “Dukan wanda ya dubi mace har ya yi sha’awarta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.” (Mat. 5:27, 28; 2 Bit. 2:14) Kiristoci da yawa da suka aikata abin da ba kyau sun soma ne da kallon batsa ko karanta littattafai da ke ta da sha’awa ko kuma kallon wasu shirye-shirye marasa ɗa’a a Intane. Wasu kuma suna kallon fina-finai da wasanni da kuma wasu shirye-shiryen talabijin da ke ɗaukaka lalata. Wasu sun je inda ake shakatawa da dare da inda ake rawan iskanci ko kuma wasu wurare don a yi musu taushi da ke ta da sha’awa.

5. Me ya sa muke bukata mu kiyaye zuciyarmu?

5 Wasu sun saka kansu a yanayin da zai kai ga yin lalata ta wajen yawan tattaunawa da wanda ba abokin aurensu ba. A duniyar nan da ba a kamun kai kuma lalata ya zama ruwan dare, yana da sauƙi rikitacciyar zuciya da ke cike da yaudara ta soma sa mutum tunani ko kuma sha’awar wani da ba abokin aurensa ba. (Karanta Irmiya 17:9, 10.) Yesu ya ce: “Daga cikin zuciya miyagun tunani ke fitowa, kisankai, zina, fasikanci.”—Mat. 15:19.

6, 7. (a) Mene ne zai faru idan mutum ya soma kasancewa da muguwar sha’awa a zuciyarsa? (b) Ta yaya za a iya guje wa wannan mugun yanayin?

6 Da zarar muguwar sha’awar ta shiga zuciyar mutane biyu da suke son juna, za su soma faɗa wa juna wasu batutuwan da suka shafi abokin aurensu. Da shigewar lokaci, sai su soma son kasancewa tare, suna shiri don su riƙa haɗuwa da juna a kai a kai kamar ba da saninsu ba. Yayin da sha’awarsu ya wuce gona da iri, kasancewa da aminci zai yi musu wuya. Idan suka ci gaba da irin wannan abotar duk da sanin cewa bai da kyau, zai musu wuya su daina.—Mis. 7:21, 22.

7 Irin waɗannan mutanen za su daina bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da sannu-sannu don mugun sha’awa da ta shiga zuciyarsu. Ƙari ga haka, za su soma riƙe hannun juna, suna sumba, suna tattaɓa da kuma yi wa juna daɗin baki. Alhali, wannan harka ce da ta shafi ma’aurata kawai. Ta yin hakan, sun bar ‘sha’awarsu ta janye su, ta yi musu tarko.’ Sa’ad da mugun sha’awar ta habala “takan haifi zunubi,” a wannan yanayin, zunubin shi ne lalata. (Yaƙ. 1:14, 15) Hakan abin baƙin ciki ne! Da a ce sun bar Jehobah ya inganta kuma ya kāre aurensu, da sun guje wa wannan mugun yanayin. Amma, ta yaya za su iya yin hakan?

KU CI GABA DA KUSANTAR ALLAH

8. Ta yaya yin abota da Jehobah yake kāre mu daga yin lalata?

8 Karanta Zabura 97:10. Yin abota da Jehobah yana da muhimmanci idan muna so mu kāre kanmu daga yin lalata. Idan muka yi la’akari da halayen Allah kuma muka yi ƙoƙarin zama “masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu,” muna “tafiya cikin ƙauna,” za mu ƙarfafa dangantakarmu da shi kuma mu guji “fasikanci da kowane irin aikin lalata.” (Afis. 5:1-4) Sanin cewa Allah zai shar’anta “fasikai da mazinata” zai taimaka wa ma’aurata su yi ƙoƙari su girmama aurensu kuma su kasance da aminci ga juna.—Ibran. 13:4.

9. (a) Ta yaya Yusufu ya guje wa jarabar yin lalata? (b) Wane darasi ne za mu koya daga misalin Yusufu?

9 Wasu daga cikin bayin Jehobah sun daina yin hattara ta wajen yin sha’ani da abokan aiki waɗanda ba Shaidun Jehobah ba bayan an tashi aiki. Mutum zai iya fuskantar jaraba a lokacin aiki ma. Wani saurayi mai suna Yusufu yana bakin aiki sa’ad da ya tarar cewa matar Shugabansa tana son sa. Kowace rana, tana ƙoƙari ta rinjaye shi. Wata rana, sai “ta kama shi a rigarsa, ta ce, Ka kwana da ni.” Amma Yusufu ya guje mata. Me ya ba wa Yusufu ƙarfin halin guje wa wannan jarabar? Ya riga ya ƙudura niyya cewa ba zai ɓata dangantakarsa da Allahn da ya sa ya kasance da tarbiyya mai kyau da kuma aminci ba. Saboda wannan matakin da ya ɗauka, ya rasa aikinsa kuma an jefa shi a cikin kurkuku, amma Jehobah ya albarkace shi. (Far. 39:1-12; 41:38-43) Bai kamata Kiristoci su saka kansu a cikin yanayin da zai sa su soma sha’awar mutumin da ba abokin aurensu ba, ko da a wurin aiki ko kuma a inda ba mutane.

KU KASANCE DA SABON HALI

10. Ta yaya kasancewa da sabon hali zai kāre ma’aurata?

10 Sabon hali yana “bisa ga Allah cikin adalci da tsarkin gaskiya.” Saboda haka, yana da muhimmanci ma’aurata su kasance da sabon hali don zai ƙarfafa aurensu. (Afis. 4:24) Waɗanda suke da wannan sabon hali suna “matar da” gaɓaɓuwansu a batun “fasikanci, ƙazanta, kwaɗayi, mugun guri, da sha’awa.” (Karanta Kolosiyawa 3:5, 6.) Wannan kalamin “matar da” tana nuna cewa wajibi ne mu ɗauki matakai masu tsanani don mu guje wa abubuwan da za su sa mu yin lalata. Za mu guji duk wani abin da zai sa mu soma sha’awar matar wani ko mijin wata. (Ayu. 31:1) Yayin da muke yin rayuwar da ta jitu da nufin Allah, za mu yi “ƙyamar abin da ke mugu” kuma mu “rungumi abin da ke nagari.”—Rom. 12:2, 9.

11. Ta yaya sabon hali zai iya ƙarfafa aure?

11 Jehobah ne tushen sabon hali. (Kol. 3:10) Saboda haka, Jehobah zai albarkaci ma’aurata idan suka yi ƙoƙari su ƙarfafa dangantakarsu da Shi ta wajen kasancewa da “zuciya ta tausayi, nasiha, tawali’u, ladabi, jimrewa.” (Kol. 3:12) Ƙari ga haka, za su ji daɗin aurensu sosai idan suka ‘bari salama ta Kristi ta yi mulki a cikin zukatansu.’ (Kol. 3:15) Abu mai kyau ne ma’aurata su ‘yi zaman daɗin soyayya da junansu’! Za su yi farin ciki idan suka ɗauki matakan bi da “juna cikin bangirma.”—Rom. 12:10.

12. Waɗanne halaye kake gani za su sa ma’aurata farin ciki?

12 Sa’ad da aka tambayi wani maigida mai suna Sid abin da yake sa su farin ciki a aurensu, ya ce: “Mun yi ƙoƙarin bi da juna cikin ƙauna a kowane lokaci. Ƙari ga haka, mun fahimta cewa sauƙin hali yana da muhimmanci.” Matarsa mai suna Sonja ta ce: “Yin alheri yana da kyau kuma mun yi ƙoƙarin kasancewa da tawali’u, ko da yake ba a kowane lokaci ba ne yin hakan yake da sauƙi.”

KU RIƘA TATTAUNAWA DA KYAU

13. Mene ne ma’aurata za su yi don aurensu ya dawwama, kuma me ya sa?

13 Babu shakka, magana da ladabi zai sa ma’aurata su ji daɗin zama tare. Abin baƙin ciki ne a ce ma’aurata ba sa ganin juna da mutunci sa’ad da suke tattaunawa. Har ma a wani lokaci, su ɗauki baƙi da dabbobinsu da daraja fiye da abokin aurensu! Sa’ad da ma’aurata suka tsawata wa juna da “ɗacin zuciya, da hasala, da fushi, da hargowa, da zage-zage,” suna ɓata aurensu. (Afis. 4:31) Maimakon ma’aurata su ɓata aurensu ta sūkar juna da baƙar magana, zai dace su ƙarfafa dangantakarsu da maganar alheri cikin hankali da kuma ƙauna.—Afis. 4:32.

14. Waɗanne halaye ne ya kamata mu guje wa?

14 Littafi Mai Tsarki ya ce akwai “lokacin shuru.” (M. Wa. 3:7) Hakan ba ya nufin cewa za mu yi gum da bakinmu don hakan zai hana tattaunawa da kyau. Wata mata a ƙasar Jamus ta ce, “Irin wannan yanayin zai iya ɓata ran mijinki.” Amma ta ƙara da cewa: “Ko da yake natsuwa bai da sauƙi idan akwai damuwa, amma bai dace mutum ya furta abin da ya ga dama ba sa’ad da yake fushi. Idan ka yi hakan, za ka faɗi abin da zai ɓata wa abokin aurenka rai, kuma hakan zai sa yanayin ya daɗa muni.” Mata da miji ba za su magance matsalolinsu ba idan suna tsawata wa juna ko kuma idan suka ƙi yi wa juna magana. Akasin haka, za su inganta aurensu idan suka yi ƙudiri cewa saɓani ba zai sa su riƙa faɗa da juna ba.

15. Ta yaya tattaunawa da kyau zai ƙarfafa aure?

15 Idan ma’aurata suka bayyana ra’ayinsu da kuma yadda suke ji, hakan zai ƙarfafa aurensu. Ya kamata ku mai da hankali ga yadda kuke magana da kuma abin da muke faɗa. Ta yaya? Ku riƙa tunanin abin da za ku faɗa kuma maganarku ta kasance da daɗin ji, ko a yanayi mai wuya ma. Ta hakan, aboki ko abokiyar aurenka za ta so ta saurari abin da kake faɗa. (Karanta Kolosiyawa 4:6.) Maigida da matarsa za su iya ƙarfafa aurensu idan suna tattaunawa da kyau ta wajen faɗa wa juna “abin da ke mai-kyau garin ginawa yayin da ake bukata, domin shi ba da alheri.”—Afis. 4:29.

Maigida da matarsa za su iya ƙarfafa aurensu idan suna tattaunawa da kyau (Ka duba sakin layi na 15)

KU RIƘA BIYA WA JUNA BUKATA

16, 17. Me ya sa yake da muhimmanci ma’aurata su riƙa mai da hankali ga juna a batutuwa na motsin rai da kuma jima’i?

16 Ma’aurata za su iya ƙarfafa aurensu idan suna yin abin da zai amfani abokin aurensu ta wajen sa bukatun abokin aurensu kan gaba da nasu. (Filib. 2:3, 4) Ya kamata ma’aurata su riƙa biya wa juna bukata a batutuwa na motsin rai da kuma jima’i.—Karanta 1 Korintiyawa 7:3, 4.

17 Abin baƙin ciki shi ne wasu ma’aurata suna ƙin yin soyayya da kuma jima’i da abokin aurensu, kuma wasu mazaje suna gani cewa idan ka bi mace cikin hankali, kai ba jan na miji ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku zauna da matayenku bisa ga sani.” (1 Bit. 3:7) Ya kamata maigida ya gane cewa ba yin jima’i ba ne kawai shi ne biyan bukata. Mace za ta ji daɗin kasancewa da mijinta idan yana ƙaunarta a kowane lokaci, ba lokacin jima’i kawai ba. Idan mace da miji suka nuna sanin yakamata a yadda suke bi da juna, za su biya bukatar juna a yadda ya kamata.

18. Ta yaya maza da mata za su ƙarfafa aurensu?

18 Ko da yake babu hujjar da mutum zai bayar na cin amanar aboki ko abokiyar aurensa, rashin nuna ƙauna ga matarka ko mijinki zai iya sa ya mai da hankalinsa ga wata. (Mis. 5:18; M. Wa. 9:9) Saboda haka ne Littafi Mai Tsarki ya ce wa ma’aurata: “Kada ku hana [biyan bukata] ma juna, sai dai da yardan juna domin kwanaki.” Me ya sa? “Domin kada Shaiɗan ya jarabce ku ta wurin rashin daurewarku.” (1 Kor. 7:5) Hakika, idan ma’aurata suka yarda Shaiɗan ya jarabce su saboda ‘rashin daurewa’ kuma ya sa ɗaya daga cikinsu ya yi zina, hakan zai haifar da yanayi na baƙin ciki ƙwarai. Akasin haka, idan kowannensu ba ya neman “ya kyautata wa kansa, sai dai ya kyautata wa ɗan’uwansa” kuma yana biyan bukatar abokiyar aurensa saboda ƙauna, ba don ya cika farilla ba, hakan zai sa su so juna sosai kuma su ji daɗin aurensu.—1 Kor. 10:24, Littafi Mai Tsarki.

KU CI GABA DA KĀRE AURENKU

19. Mene ne ya kamata mu ƙudura aniyar yi, kuma me ya sa?

19 Muna gab da shiga sabuwar duniya da za a yi adalci. Shi ya sa faɗa wa jaraba zai haifar da mugun sakamako kamar yadda ya faru da Isra’ilawa 24,000 a Filin Mowab. Littafi Mai Tsarki ya ambaci mugun sakamako da ya faru a lokacin kuma ya ba da wannan shawara: “Wanda yake maida kansa yana tsaye, shi yi lura kada ya fāɗi.” (1 Kor. 10:12) Saboda haka, yana da muhimmanci mu ƙarfafa aurenmu ta wajen kasancewa da aminci ga Ubanmu na sama da kuma abokin aurenmu. (Mat. 19:5, 6) Yanzu ne ya kamata mu mai da hankali sosai kuma yi ƙoƙari da anniya don a same mu “cikin salama, marasa-aibi marasa-laifi a gabansa.”—2 Bit. 3:13, 14.