Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Haka nan Ya Gamshe Ka Sarai”

“Haka nan Ya Gamshe Ka Sarai”

Ka ɓoye wa masu-hikima da masu-fahimi waɗannan al’amura, ka bayyana su ga jarirai.”—LUK. 10:21.

1. Me ya sa Yesu ya yi “murna a cikin Ruhu Mai-tsarki”? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

 SHIN za ka iya kwatanta irin “murna a cikin Ruhu Mai-tsarki” da Yesu Kristi ya yi? Wataƙila ya yi murmushi sosai da kuma farin ciki matuƙa. Me ya sa shi farin ciki haka? Bai daɗe da tura almajiransa 70 su yi wa’azin bishara game da Mulkin Allah ba. Yana son ya san yadda za su yi wa’azin. Amma maƙiyan bishara a lokacin suna da yawa kuma suna da iko, waɗannan sun haɗa da marubuta da Farisawa masu ilimi. Kuma sun zuga mutane su riƙa raina Yesu da almajiransa suna ganin Yesu kafinta ne kawai, almajiransa kuma “marasa karatu.” (A. M. 4:13; Mar. 6:3) Amma almajiransa sun dawo daga wa’azi suna farin ciki. Sun yi wa’azi duk da hamayya da suka fuskanta daga mutane da aljannu. Me ya sa suka yi farin ciki haka?—Karanta Luka 10:1, 17-21.

2. (a) Ta yaya almajiran Yesu suka zama kamar yara? (b) Mene ne ya taimaka wa almajiran Yesu su fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki masu muhimmanci?

2 Ka yi la’akari da abin da Yesu ya gaya wa Jehobah: “Ina yabonka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, da ka ɓoye ma masu-hikima da masu-fahimi waɗannan al’amura, ka bayyana su ga jarirai: I, ya Uba, gama haka nan ya gamshe ka.” (Mat. 11:25, 26) Hakika, Yesu ba ya nufin cewa almajiransa yara ne a zahiri. A maimakon haka, ya san cewa suna kamar yara idan aka gwada su da malamai da Farisawa da suke ganin kansu masu ilimi. Ƙari ga haka, Yesu ya gaya wa almajiransa su zama masu tawali’u kamar yara da suke so a riƙa koya musu abubuwa. (Mat. 18:1-4) Ta yaya suka amfana daga kasancewa da tawali’u? Jehobah ya taimaka musu ta ruhu mai tsarki su fahimci wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki masu muhimmanci da yake suna da tawali’u. Amma Shaiɗan ya makantar da malaman addinin Yahudawa da yake su masu fahariya ne.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Hakika, abin da ya sa Yesu farin ciki matuƙa ke nan. Ya yi farin cikin yadda Jehobah ya bayyana wa mutane masu tawali’u koyarwa masu wuya duk da cewa su ba masu ilimi ba. Ƙari ga haka, ya yi murna da yadda Ubansa ya amince da koyarwa a hanya mai sauƙi. Da yake Jehobah bai canja, ta yaya muka san cewa har ila yana amincewa da irin wannan koyarwar? Yayin da muke bincika amsar wannan tambayar, mu ma za mu iya yin farin ciki matuƙa kamar yadda Yesu ya yi.

TA YAYA AKA BAYYANA WA MUTANE KOYARWA MAI WUYA?

4. Ta yaya Hasumiyar Tsaro a Turanci mai sauƙi ta kasance kyauta mai kyau?

4 A shekarun nan, ƙungiyar Jehobah tana mai da hankali wajen koyar da Littafi Mai Tsarki a hanya mai sauƙin fahimta. Ka yi la’akari da misalai uku. Da farko, mun sami Hasumiyar Tsaro a Turanci mai sauƙi. a Mutanen da ba sa fahimtar Turanci sosai sun yi farin ciki matuƙa da suka sami wannan mujallar. Magidanta sun gano cewa yaransu sun fi fahimtar wannan mujallar wadda ita ce muhimmiyar hanya da Jehobah yake amfani da ita don koyar da mu. ’Yan’uwa da yawa sun rubuta wasiƙu zuwa ga Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah don su nuna godiyarsu. Wata ’yar’uwa ta rubuta cewa a dā ba ta yin kalami sa’ad da ake nazarin Hasumiyar Tsaro. Ta ce: “Nakan yi zamana shiru. Amma ba yanzu ba.” Bayan da ta yi amfani da Hasumiyar Tsaro a Turanci mai sauƙi, ta ƙara da cewa: “Yanzu ina yin kalami fiye da sau ɗaya a taro kuma ba na jin tsoro. Ina godiya ga Jehobah, ina gode muku.”

5. Me ya sa sabon juyin New World Translation of the Holy Scriptures yake da amfani sosai?

5 Na biyu, mun sami sabon juyi na New World Translation of the Holy Scriptures, da aka fito da shi a lokacin da aka yi taron shekara-shekara a ranar 5 ga Oktoba, 2013. b An yi amfani da kalmomi kaɗan kawai a ayoyi masu yawa, duk da haka, suna da ma’ana kuma an fi ganewa. Alal misali, a dā Ayuba 10:1 yana ɗauke da kalmomi 27, amma yanzu an rage zuwa 19; kuma an rage kalmomi 20 da ke Misalai 8:6 zuwa kalmomi 13. An fi fahimtar waɗannan ayoyin a sabon juyin. Wani Ɗan’uwa da yake da begen zuwa sama da ya daɗe yana bauta wa Jehobah ya ce: “Na karanta littafin Ayuba a wannan sabon juyin, sai na ƙara fahimtarsa da kyau.” Mutane da yawa sun yi irin wannan furucin.

6. Yaya kake ji game da ƙarin haske da muka samu game da Matta 24:45-47?

6 Na uku, ka yi la’akari da ƙarin haske na kwanan nan a kan yadda muka fahimci wasu abubuwa. Alal misali, mun yi farin ciki sosai da muka sami ƙarin haske game da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” da aka wallafa a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2013. (Mat. 24:45-47) An bayyana cewa bawan nan mai aminci shi ne Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah, kuma “iyalin gidansa” su ne dukan shafaffu da kuma “waɗansu tumaki” da suke amfana daga littattafan da ake tanadarwa da suke ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah. (Yoh. 10:16) Mun yi farin ciki matuƙa da wannan koyarwa da za mu koya wa sababbi. A waɗanne hanyoyi ne kuma Jehobah ya nuna cewa ya amince da koyarwa mai sauƙin fahimta?

BAYYANA LABARAN LITTAFI MAI TSARKI A HANYA MAI SAUƘI

7, 8. Waɗanne labaran Littafi Mai Tsarki ne suke wakiltar wasu abubuwan da za su faru a nan gaba?

7 Idan ka daɗe kana bauta wa Jehobah, za ka lura cewa an canja yadda ake bayyana labaran Littafi Mai Tsarki da ke cikin littattafanmu. Ta yaya? A dā, mukan ce wani labarin Littafi Mai Tsarki yana wakiltar wani abu mai muhimmanci a nan gaba. Akwai wata ayar Littafi Mai Tsarki da ta goyi bayan hakan? Hakika. Alal misali, Yesu ya yi maganar “alama ta Yunana annabi.” (Karanta Matta 12:39, 40.) Yesu ya bayyana cewa yadda Yunana yake cikin kifi yana wakiltar lokacin da Yesu yake cikin kabari.

8 Akwai wasu labaran Littafi Mai Tsarki da suke wakiltar wasu abubuwa da za su faru a nan gaba. Manzo Bulus ya tattauna wasu da dama a cikin su. Alal misali, dangantakar Ibrahim da Hajaratu da Saratu yana wakiltar dangantakar Jehobah da al’ummar Isra’ila ta dā da kuma sashen ƙungiyar Jehobah da ke sama. (Gal. 4:22-26) Hakazalika, mazauni da haikali da Ranar Kafara da babban firist da wasu fannoni na dokar da Allah ya ba Musa suna wakiltar “ishara ce kawai ta kyawawan abubuwan da ke gaba.” (Ibran. 9:23-25; 10:1, Littafi Mai Tsarki) Yin nazarin waɗannan annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki za su ƙarfafa mu. Shin za mu kammala cewa kowane mutum da abin da ya faru da wani abin da aka kwatanta a Littafi Mai Tsarki yana wakiltar wani mutum ko kuma wani abu?

9. Ta yaya aka bayyana labarin Naboth a dā?

9 A dā, littattafanmu sun bayyana cewa kowane mutum da abin da ya faru da wani abin da aka kwatanta a Littafi Mai Tsarki yana wakiltar wani mutum ko kuma wani abu. Ka yi la’akari da labarin Naboth, wanda Sarauniya Jezebel ta ƙulla masa makirci a kashe shi don ta so maigidanta, Ahab ya kwace gonarsa na inabi. (1 Sar. 21:1-16) Littattafanmu sun bayyana a shekara ta 1932, cewa wannan labarin yana wakiltar wani abu da zai faru. A dā mun bayyana cewa Ahab da Jezebel suna wakiltar Shaiɗan da ƙungiyarsa; Naboth yana wakiltar Yesu; mutuwar Naboth yana wakiltar mutuwar Yesu. Shekaru da yawa bayan haka, littafin nan “Let Your Name Be Sanctified,” (Bari a Tsarkake Sunanka) da aka wallafa a shekara ta 1961, ya ce Naboth yana wakiltar shafaffu kuma Jezebel tana wakiltar Kiristocin ƙarya. Don haka, yadda Jezebel ta tsananta wa Naboth yana wakiltar yadda ake tsananta wa shafaffu a kwanaki na ƙarshe. Shekaru da yawa, irin wannan bayanin ya ƙarfafa bayin Allah. To, me ya sa muka canja yadda muke bayyana abubuwa?

10. (a) Ta yaya hikima take sa bawan nan yake yin hankali wajen bayyana wasu labaran Littafi Mai Tsarki? (b) Mene ne littattafanmu suka fi mai da hankali a kai?

10 A shekarun da suka shige, da sannu-sannu Jehobah ya taimaka wa ‘bawan nan mai-aminci mai-hikima’ ya kasance da hikima sosai. Yanzu bawan nan ba ya bayyana cewa labaran Littafi Mai Tsarki suna wakiltar wani abu dabam sai dai idan akwai wata aya da ta nuna hakan. Ƙari ga haka, an gano cewa yadda ake bayyana cewa wasu labaran Littafi Mai Tsarki suna wakiltar wasu mutane ko kuma wasu abubuwa yana da wuyar fahimta. Mafi muhimmanci ma, idan aka mai da hankali ainun ga abu ko mutumin da labarin yake wakilta, yana da wuya a tuna darasin da za a koya. Saboda haka, littattafanmu suna mai da hankali ga darussa masu sauƙin fahimta game da bangaskiya da jimiri da ibada da wasu halaye masu kyau da muke koya daga Littafi Mai Tsarki. c

Misalin Naboth ya koya mana darasi mai kyau (Ka duba sakin layi na 11)

11. (a) Yaya muka fahimci labarin Naboth yanzu, kuma me ya sa dukanmu za mu iya amfana daga wannan labarin? (b) Me ya sa littattafanmu na kwanan nan ba sa bayyana cewa wasu labaran Littafi Mai Tsarki suna wakiltar wasu mutane ko kuma wasu abubuwa? (Ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” da ke wannan fitowar.)

11 To, ta yaya muka fahimci labarin Naboth yanzu? An fi ganewa yanzu. Wannan mutumi mai adalci ya mutu ba don yana wakiltar Yesu ko shafaffu ba, amma don shi mai aminci ne. Ya yi tsayin daka wajen bin dokar Allah sa’ad da yake fuskantar tsanantawa daga hannun masu sarauta. (Lit. Lis. 36:7; 1 Sar. 21:3) Labarinsa zai taimaka mana don kowanenmu zai iya fuskantar irin wannan yanayin. (Karanta 2 Timotawus 3:12.) Dukan Kiristoci za su iya su fahimci waɗannan darussa masu ƙarfafa bangaskiya, su tuna kuma su yi amfani da su.

12. (a) Mene ne bai kamata mu kammala game da wasu labaran Littafi Mai Tsarki ba? (b) Me ya sa muka fahimci wasu koyarwa masu wuya na Allah? (Ka duba ƙarin bayani.)

12 Ya kamata mu kammala cewa labaran Littafi Mai Tsarki suna koya mana darussa ne kawai ba su da wasu ma’ana? A’a. Maimakon littattafanmu su bayyana cewa wasu labaran Littafi Mai Tsarki suna wakiltar wasu mutane da wasu abubuwa, sun mai da hankali ga yadda labaran suke da alaƙa da juna. Alal misali, yadda Naboth ya kasance da aminci har mutuwa ya tuna mana da yadda Yesu da kuma shafaffu suka kasance da aminci. Har ila, hakan ya tuna mana yadda mutane da yawa da ke cikin “waɗansu tumaki” na Ubangiji suka kasance da tawali’u. Irin wannan bayani da yake da sauƙin fahimta ya nuna cewa Jehobah ne yake koyar da mu. d

AN BAYYANA KWATANCE-KWATANCEN YESU A HANYA MAI SAUƘI

13. Waɗanne misalai ne suka nuna cewa yanzu muna bayyana kwatance-kwatancen Yesu a hanya mai sauƙi?

13 Yesu ne babban Malamin da ya taɓa rayuwa a duniya. Ya fi son yin amfani da kwatanci sa’ad da yake koyarwa. (Mat. 13:34) Kwatance-kwatance suna da amfani don suna bayyana abubuwa masu wuya a hanya mai sauƙi don mu fahimta. Shin littattafanmu suna bayyana kwatance-kwatancen Yesu a hanyar da za mu fahimta kuwa? Ƙwarai kuwa! Mun yi farin ciki sosai a lokacin da aka bayyana mana kwatancin Yesu na yisti da ƙwayar mastad da kuma taru a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2008, ko ba haka ba? Yanzu mun fahimci sarai cewa waɗannan kwatance-kwatance suna magana game da Mulkin Allah da kuma nasarar da aka samu wajen taimaka wa mutane da yawa su yi tir da duniyar Shaiɗan kuma su zama almajiran Yesu.

14. (a) Ta yaya muka bayyana almarar Basamariye mai kirki a dā? (b) Ta yaya aka bayyana wannan almarar yanzu?

14 To, mene ne za mu iya faɗa game da labarai ko almara da Yesu ya yi dalla-dalla? Wasu ma’anarsu a alamance ne, wasu kuma suna koya mana darussa da za mu iya amfani da su. Amma ta yaya za mu iya bambanta su? A shekaru da yawa yanzu, ana samun ƙarin haske a kan waɗannan batutuwa da sannu-sannu. Alal misali, ka yi la’akari da yadda muka taɓa bayyana almarar Yesu na wani Basamariye mai kirki. (Luk. 10:30-37) A shekara ta 1924, Hasumiyar Tsaro ta ce Basamariyen yana wakiltar Yesu; hanyar da ta bi daga Urushalima da ke kan dutse zuwa Jericho da ke gangare tana wakiltar taɓarɓarewar rayuwar ’yan Adam tun lokacin da aka yi rashin biyayya a Adnin. Ƙari ga haka, ɓarayin suna wakiltar manyan masana’antu da ’yan kasuwa masu cin mugun riba. Firist ɗin da kuma Balawin suna wakiltar addinan ƙarya. A yau, littattafanmu suna amfani da almarar don su tuna wa dukan Kiristoci cewa wajibi ne mu riƙa taimaka wa kowane irin mutum, musamman ma ta wajen koya musu game da Allah. Babu shakka, muna farin ciki cewa Jehobah yana bayyana mana koyarwarsa a hanya da za mu fahimta.

15. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

15 A talifi na gaba za mu tattauna almara na budurwoyi goma da Yesu ya bayar. (Mat. 25:1-13) Yaya Yesu yake son mabiyansa a wannan kwanaki na ƙarshe su fahimci wannan kwatancin? Shin yana son su fahimci cewa kowane mutum ko abu ko kuma wani yanayi da aka ambata a cikin kwatancin yana nuna abin da zai faru a nan gaba? Ko kuwa yana son mabiyansa su koyi wani darasi ne da zai taimaka musu a wannan kwanaki na ƙarshe? Bari mu gani.

a An soma wallafa Hasumiyar Tsaro a Turanci mai sauƙi a watan Yuli na shekara ta 2011. Tun daga lokacin, ana wallafa irin wannan mujallar a harsuna kaɗan ne kawai.

b Ana kan yin shirin fassara wannan sabon juyin zuwa wasu harsuna.

c Alal misali, littafin nan Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu ya tattauna labaran wasu bayin Allah guda sha huɗu a cikin Littafi Mai Tsarki. Littafin ya mai da hankali ga darussan da aka koya ne ba abin da suke wakilta ba.

d Babu shakka, Kalmar Allah tana ɗauke da wasu koyarwa da suke da ‘wuyar ganewa’ kuma wannan ya haɗa da rubutun da Bulus ya yi. Duk da haka, ruhu mai tsarki ne ya hure dukan mutanen da suka rubuta Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, ya taimaka wa Kiristoci a yau su fahimci “zurfafan al’amuran Allah,” wato koyarwar Littafi Mai Tsarki masu wuya.—2 Bit. 3:16, 17; 1 Kor. 2:10.