Ka Tuna?
Shin ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan kuwa? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:
A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yin shiri don taron Tuna Mutuwar Yesu kowace shekara?
Hanya ɗaya ita ce ta bin tsarin karatun Littafi Mai Tsarki da ake yi don taron Tuna Mutuwar Yesu. Wata hanya kuma ita ce ta ƙara ƙwazo a wa’azi a wannan lokacin. Ƙari ga haka, zai dace mu riƙa yin addu’a a kai a kai game da begen da muke da shi na yin rayuwa a cikin aljanna a duniya ko kuma a sama.—1/15, shafuffuka na 14-16.
Wace kyauta ce aka ba ’yan’uwa a Japan da ta sa su farin ciki?
An fito da wata sabuwar ƙasida ta linjilar Matta da aka fassara daga New World Translation. Ana rarrabawa a wa’azi, kuma mutane da yawa da ba su taɓa karanta Littafi Mai Tsarki ba sun karɓi ƙasidar.—2/15, shafi na 3.
Waɗanne abubuwa ne suka taimaka wajen yaɗa bishara a ƙarni na farko?
Kwanciyar hankali da aka yi a masarautar Roma ya taimaka. An ƙera hanyoyi da dama kuma hakan ya taimaka wa almajiran Yesu na farko su yi tafiya zuwa wurare dabam-dabam a masarautar. Girkanci yare ne da ake yi a ko’ina a masarautar kuma yaren ya taimaka wajen yaɗa bishara, har ga Yahudawa da ke zama a masarautar. Ƙari ga haka, tsarin dokokin Roma ya taimaka wajen kāre bishara.—2/15, shafuffuka na 20-23.
Mene ne Mulkin Allah kuma ta yaya zai kawar da cin hanci da rashawa?
Mulkin Allah gwamnati ne da a yanzu haka yana mulki a samaniya, kuma zai sauya dukan gwamnatocin duniya. (Zabura 2:8, 9; Ru’ya ta Yohanna 16:14; 19: 19-21) Zai kawar da cin hanci da rashawa ta koya wa mutane yadda za su shawo kan munanan muradi da ke haifar da wannan halin.—3/1, shafi na 4, 7.
Me ya sa ba a bayyana a littattafanmu yanzu cewa wasu labaran Littafi Mai Tsarki suna wakiltar muhimman mutane ko abubuwa, kamar yadda ake yi a dā?
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa wasu mutane da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki suna wakiltar wasu muhimman abubuwa. Wani misali shi ne wanda aka ambata a Galatiyawa 4:21-31. Amma idan Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba, bai kamata mu ɗauka cewa wani mutum ko yanayi ko abu yana wakiltar wani abu dabam ba. Duk da haka, za mu iya koyan darussa daga mutane da kuma labarai da aka yi maganarsu a cikin Littafi Mai Tsarki. (Rom. 15:4)—3/15, shafuffuka na 17-18.
Me ya sa ya dace a yi wa wanda ya ƙi tuba yankan zumunci?
Littafi Mai Tsarki ya ambaci tsari mai muhimmanci da za a bi kafin a yi wa wani yankan zumunci. Kuma hakan yana da amfani. (1 Kor. 5:11-13) Yana sa a girmama sunan Allah, yana kāre ikilisiya. Ƙari ga haka, yana iya sa mai zunubin ya fahimci kuskurensa ya tuba.—4/15, shafuffuka na 29-30.
Me ya sa ya dace ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki?
Domin miliyoyin mutane sun sami amsoshi masu gamsarwa a Littafi Mai Tsarki. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ba da amsoshin waɗannan tambayoyi: Wane ne Allah? Mene ne kamanninsa da kuma halayensa? Shin yana da suna? A ina yake da zama? Za mu iya ƙulla dangantaka da shi kuwa?—5/1, shafi na 5.