Za Mu Iya Kasancewa da Dabi’a Mai Kyau
‘Ku tsabtace hannuwanku, . . . ku tsarkake zukatanku.’ —YAƘ. 4:8.
1. Ta yaya mutanen duniya suke ɗauka kasancewa da ɗabi’a mai kyau?
MUNA rayuwa a zamani da zina da fasikanci sun zama ruwan dare. A ƙasashe da yawa, mutane suna gani cewa luwaɗi da zina ba laifi ba ne. Fina-finai da littattafai da kuma kafofin yaɗa labarai suna ɗaukaka irin wannan salon rayuwa. (Zab. 12:8) Zina da fasikanci sun zama ruwan dare da har ma za mu iya tambayar nan, ‘Anya mutum zai iya kasancewa da ɗabi’a mai kyau kuwa?’ Hakika, da taimakon Jehobah, Kiristoci na gaskiya za su iya kasancewa da ɗabi’a mai kyau.—Karanta 1 Tasalonikawa 4:3-5.
2, 3. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu guji sha’awoyin banza? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
2 Amma, wajibi ne mu guji sha’awar banza idan muna son mu yi rayuwa da za ta faranta wa Jehobah rai. Kamar yadda ƙugiya da aka sa tānā za ta ja hankalin kifi, hakan nan ma tunani da sha’awoyin banza za su iya rinjayar Kirista idan bai yi watsi da su ba. Idan ba haka ba, suna iya sa mu soma sha’awar banza. Da shigewar lokaci, sha’awar za ta mamaye Yaƙub 1:14, 15.
zuciyarmu. A wannan lokacin, za mu iya yin zunubi idan muka sami zarafin yin haka. Hakika, “sha’awa . . . takan haifi zunubi.”—Karanta3 Yana da muhimmanci mu yi tunani a kan yadda sha’awa na ɗan lokaci zai sa mutum ya yi zunubi mai tsanani. Amma yana da ban ƙarfafa mu san cewa idan muka ƙi yin tunanin banza, za mu guji yin zina da kuma mugun sakamakonsa! (Gal. 5:16) Za mu tattauna abubuwa uku da za su taimaka mana mu guji sha’awoyin banza, wato dangantakarmu da Jehobah da shawarar da ke cikin Kalmarsa da kuma taimakon Kiristoci da suka manyanta.
KA KUSACI ALLAH
4. Me ya kamata mu yi don mu kusaci Jehobah?
4 Littafi Mai Tsarki ya ba da wannan shawara ga waɗanda suke so su kusaci Allah: ‘Ku tsabtace hannuwanku . . . ku tsarkake zukatanku.’ (Yaƙ. 4:8) Idan mun mutunta dangantakarmu da Jehobah, za mu yi ƙoƙari mu faranta masa rai a kowane fanni na rayuwarmu, har da tunaninmu. Za mu kasance da “zuciya mai-tsarki” ta wajen yin tunanin abubuwa masu tsarki, masu adalci da kuma abubuwa da suka cancanci yabo. (Zab. 24:3, 4; 51:6; Filib. 4:8) Hakika, Jehobah ya san cewa mu ajizai ne kuma muna iya soma tunanin banza. Amma yana baƙin ciki idan muka mai da hankali ga abubuwa marasa ɗa’a, maimakon mu yi iya ƙoƙarinmu don mu guji yin tunanin banza. (Far. 6:5, 6) Sanin haka zai sa mu ƙudura niyyar yin tunani mai kyau.
5, 6. Ta yaya addu’a za ta taimaka mana mu guji sha’awoyin banza?
5 Muna nuna cewa mun dogara ga Jehobah idan muna roƙonsa cewa ya taimaka mana mu guji tunanin banza. Idan muka kusaci Jehobah ta yin addu’a, shi ma zai kusace mu. Zai ba mu ruhunsa mai tsarki, kuma hakan zai ƙarfafa mu mu ƙudura niyyar guje wa tunanin banza kuma mu kasance da ɗabi’a mai kyau. Bari mu yi addu’a ga Allah cewa muna so tunaninmu ya faranta masa rai. (Zab. 19:14) Shin muna gaya masa ya bincika zuciyarmu ko zai ga wani “rashin gaskiya” wato, sha’awoyin banza da za su iya sa mu yi zunubi? (Zab. 139:23, 24) Shin muna roƙonsa a kai a kai ya taimaka mana mu kasance da aminci sa’ad da muke fuskantar gwaji?—Mat. 6:13.
6 Yadda aka yi rainonmu ko kuma halinmu a dā zai iya sa mu soma son yin abubuwan da Jehobah ba ya so. Duk da haka, Jehobah zai iya taimaka mana mu daina yin waɗannan abubuwa kuma mu yi abin da zai faranta masa rai. Alal misali, bayan Sarki Dauda ya yi zina da Bathsheba, sai ya tuba kuma ya roƙi Jehobah ya ba shi ‘zuciya mai-tsabta, . . . ya sabonta daidaitacen ruhu daga cikinsa.’ (Zab. 51:10, 12) Saboda haka, idan muna mugun sha’awoyi a dā kuma har ila muna kokawa da su, Jehobah zai taimaka mana mu kasance da ƙarfin halin yi masa biyayya. Ko da tunanin banza ya yi saiwa a zuciyarmu kuma hakan yana sa ba ma iya tunanin abin da ya dace, Jehobah zai iya ja-gorarmu don mu bi dokokinsa kuma za mu yi nasara. Hakika, zai iya taimaka mana mu guji tunanin banza.—Zab. 119:133.
‘KU ZAMA MASU AIKATA MAGANA’
7. Ta yaya Kalmar Allah za ta kāre mu daga yin tunanin banza?
7 Jehobah zai iya amsa addu’armu ta shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Yaƙ. 3:17, Littafi Mai Tsarki) Karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini a kan abin da muka karanta zai sa mu guji yin tunanin banza. (Zab. 19:7, 11; 119:9, 11) Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da misalai da takamaiman shawara da za su taimaka mana mu guji sha’awoyin banza.
Shawarar da ke cikin Kalmar Allah “da farko dai tsattsarka ce.” (8, 9. (a) Me ya sa wani saurayi ya yi zina da wata karuwa? (b) A waɗanne yanayi ne za mu iya bin gargaɗin da ke cikin Misalai sura ta 7?
8 Misalai 5:8 ta ce: “Ka nisanta tafarkinka da ita [karuwa]; Kada ka kusanci ƙofar gidanta.” An kwatanta hadarin ƙin bin wannan shawara a littafin Misalai sura ta 7. A wurin, an ambata wani saurayi da ya je yawo kusa da gidan wata karuwa. Sa’ad da magariba ta yi sai karuwar ta tare shi, tana sanye da tufafi da ke nuna siffar jikinta. Sai ta rungume shi, ta sumbace shi, kuma ta soma masa magana don ta ja hankalinsa. Sakamakon haka, sai suka yi zina. Hakika, wannan saurayin bai yi niyyar yin lalata ba. Amma ba shi da wayo da kuma basira. Duk da haka, wajibi ne ya fuskanci mugun sakamako da yin zina take haifarwa. Inda ya guje ta da bai faɗa cikin wannan jarabar ba.—Mis. 7:6-27.
9 Wani lokacin mukan nuna rashin wayo ta wajen kasancewa a cikin yanayin da zai ta da sha’awoyin banza. Alal misali, daddare wasu tasoshin talabijin sukan nuna wasu shirye-shirye marasa ɗa’a, saboda haka ba zai dace mu riƙa dudduba tsarin ayyukan da ke talabijin don kawai muna so mu ƙayatar da kanmu. Wataƙila za mu riƙa shiga shafuffuka a intane ko kuma dandalin hira da suke ɗauke da batsa da wasu shirye-shirye marasa ɗa’a. A irin wannan yanayin, wasu shirye-shirye da za mu kalla za su iya nuna abubuwa da za su sa mu riƙa sha’awoyi da ba su dace ba kuma hakan zai iya sa mu ɓata dangantakarmu da Jehobah.
10. Me ya sa yin kwarkwasa bai da kyau? (Ka duba hoton da ke shafi na 13.)
10 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana yadda ya kamata maza da mata za su bi da juna. (Karanta 1 Timotawus 5:2.) Wannan shawarar ta hana yin kwarkwasa. Wasu suna ganin ba laifi ba ne su riƙa motsa jikinsu da nuna alamu ko kuma kashe ido don su nuna cewa suna son wani. Amma idan mutane biyu suna kwarkwasa da juna, sukan iya soma tunanin banza kuma hakan zai iya sa su yi zina. Hakan ya faru a dā kuma zai iya sake faruwa.
11. Wane misali mai kyau ne Yusufu ya kafa mana?
11 Yusufu ya kafa mana misali mai kyau a wannan batun. Ya guji matar Fotifa sa’ad da ta yi ƙoƙari ta rinjaye shi. Kowace rana, ta yi ta matsa masa ya kasance da ita. (Far. 39:7, 8, 10) Wani masanin Littafi Mai Tsarki ya ce kamar dai matar Fotifa, tana cewa: “‘Bari mu kasance tare na ɗan lokaci,’ don tana ganin hakan zai sa [Yusufu] ya soma sha’awarta.” Amma, Yusufu ya tsai da shawara cewa ba zai yi kwarkwasa da ita ba, hakan ya taimaka masa bai yi tunanin banza ba. Kuma sa’ad da ta yi ƙoƙari ta tilasta masa ya yi jima’i da ita, Yusufu ya ɗauki mataki nan da nan, ya “bar rigatasa a hannunta, ya gudu, ya fita waje.”—Far. 39:12.
12. Ta yaya muka san cewa abin da muke kallo zai iya shafan zuciyarmu?
12 Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu cewa abin da muke gani zai iya shafan zuciyarmu kuma ya sa mu riƙa sha’awar banza. Idan namiji yana yawan kallon mata ko kuma mace tana yawan kallon maza, hakan zai iya kai ga yin tunanin yin zina. Yesu ya yi gargaɗi cewa “dukan wanda ya dubi mace har ya yi sha’awarta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.” (Mat. 5:28) Ka tuna da abin da ya faru da Sarki Dauda. “Daga kan bene kuwa [Dauda] ya hangi wata mace tana wanka.” (2 Sam. 11:2) Sai ya ci gaba da kallonta kuma hakan ya sa ya soma tunaninta. Sakamakon haka, ya soma sha’awar matar wani kuma ya yi zina da ita.
13. Me ya sa muke bukatar mu ‘yi wa’adi da idanunmu,’ kuma me hakan ya ƙunsa?
13 Idan muna son mu guji tunanin banza, muna bukatar mu ‘yi wa’adi da idanunmu,’ kamar yadda amintaccen bawan Allah, wato Ayuba ya yi. (Ayu. 31:1, 7, 9) Wajibi ne mu guji zura wa mutum ido da kuma yin tunanin banza game da shi ko ita. Kuma mu kawar da idanunmu nan da nan idan muka ga hoton batsa a kwamfuta ko allon talla ko bangon mujalla ko kuma wani wuri.
14. Ta yaya za mu amfana idan muka bi shawarar kasancewa da ɗabi’a mai kyau?
14 Idan abubuwan da muka tattauna ya sa ka ga cewa akwai wasu wuraren da kake bukatar ka ɗauki wasu matakai Yaƙub 1:21-25.
don ka guji sha’awoyin banza, ka yi hakan nan da nan. Ka bi shawarar da ke cikin Kalmar Allah, hakan zai taimaka maka ka guji yin zunubi kuma ka ci gaba da kasancewa da ɗabi’a mai kyau.—Karanta‘KA KIRA DATTAWA’
15. Idan muna fama da sha’awoyin banza, me ya sa yake da muhimmanci mu nemi taimako?
15 ’Yan’uwa masu bi za su iya taimaka mana idan muna fama da sha’awoyin banza. Ko da yake, gaya wa wani game da irin wannan matsalar ba shi da sauƙi, amma neman taimakon ɗan’uwa da ya manyanta zai taimaka mana mu yi canja-canje. (Mis. 18:1; Ibran. 3:12, 13) Tattauna kasawarmu da Kirista da ya manyanta zai taimaka mana mu san canje-canje da muke bukatar mu yi. Hakan zai taimaka mana mu yi gyara da suka dace don Jehobah ya ci gaba da ƙaunarmu.
16, 17. (a) Ta yaya dattawa za su iya taimaka wa waɗanda suke fama da mugun sha’awoyi. Ka bayyana. (b) Me ya sa ya kamata waɗanda suke kallon batsa su nemi taimako ba tare da ɓata lokaci ba?
16 Dattawa sun cancanta su taimaka mana. (Karanta Yaƙub 5:13-15.) Wani saurayi a ƙasar Brazil ya yi shekaru da yawa yana fama da sha’awoyin banza. Ya ce: “Na san cewa tunanin da nake yi ba ya faranta wa Jehobah rai, amma ina tsoron gaya wa dattawa yadda nake ji.” Abin farin ciki shi ne, wani dattijo a ikilisiyarsu ya ƙarfafa shi ya nemi taimako. Saurayin ya ce: “Yadda dattawan suka bi da ni cikin ƙauna ya ba ni mamaki. Sun nuna min ƙauna fiye da yadda nake gani ya kamata. Sun saurare ni yayin da nake bayyana musu damuwata. Sun yi amfani da Littafi Mai Tsarki wajen tabbatar mini cewa Jehobah yana ƙaunata kuma suka yi addu’a tare da ni. Hakan ya sa na amince da shawarar Littafi Mai Tsarki da suka ba ni.” Shekaru bayan ya sake ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah, ɗan’uwan ya ce: “Yanzu, na san cewa yana da muhimmanci mutum ya nemi taimakon dattawa maimakon ya riƙa fama shi kaɗai.”
17 Neman taimako yana da muhimmanci idan abin da ya sa mutum yake tunanin banza shi ne kallon batsa. Idan mutum ya ƙi neman taimako da wuri, hakan zai iya sa wannan mugun sha’awar ta “habala” kuma ta kai ga yin ‘zunubin’ da zai shafi wasu kuma ya ɓata sunan Jehobah. Bayin Jehobah da yawa sun nemi taimakonsa don suna son su faranta masa rai kuma su ci gaba da kasancewa a cikin ikilisiya.—Yaƙ. 1:15; Zab. 141:5; Ibran. 12:5, 6.
KA ƘUDURA NIYYAR KASANCEWA DA ƊABI’A MAI KYAU!
18. Mene ne ka ƙudura niyyar yi?
18 Yayin da tarbiyyar mutanen wannan duniyar da Shaiɗan yake mulki take ƙara taɓarɓarewa, Jehobah yana farin ciki cewa bayinsa suna iya ƙoƙarinsu don su guje wa duk wani tunanin banza kuma suna kiyaye dokokinsa game da ɗabi’a. Saboda haka, bari kowannenmu ya yi ƙudurin kasancewa kusa da Jehobah kuma ya amince da ja-gorar da yake bayarwa ta wurin Littafi Mai Tsarki da kuma ƙungiyarsa. Kasancewa da ɗabi’a mai kyau yana sa gamsuwa da kwanciyar hankali yanzu. (Zab. 119:5, 6) Ƙari ga haka, a nan gaba bayan an kawar da Shaiɗan, za mu sami gatan yin rayuwa har abada a Aljanna a duniya don tasirin Shaiɗan ba zai sake kasancewa ba.