Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Albarkar Jehobah Ta Sa Na Wadata

Albarkar Jehobah Ta Sa Na Wadata

AN HAIFE ni a shekara ta 1927, a ƙaramin garin Wakaw, Saskatchewan da ke ƙasar Kanada. Mu yara bakwai ne a gidanmu, maza huɗu da mata uku. Saboda haka, na saba da zama da mutane tun ina ƙarama.

Mun yi fama da matsanancin talaucin, wato Great Depression da ya faru a tsakanin shekara ta 1931 da 1939. Mu ba masu arziki ba ne, amma ba ma rasa abinci. Muna kiwon kaji da kuma wata saniya, saboda haka ba ma rasa ƙwai da madara da man shanu da cuku da kuma dunƙulen mai. Kowa a gidanmu yana da aikin da aka ba shi ko wajen kula da dabobbi ko kuma yin wasu aikace-aikace a cikin gidan.

Ban na mantawa da abubuwan masu ban farin ciki da suka faru a lokacin, har da ƙanshin aful (apple) da ke cika ɗakin. A lokacin kaka sa’ad da ake girbin amfanin gona, mahaifinmu yakan je ya sayar da amfanin gona a cikin gari, kuma ya dawo da kwalin aful. Hakan ya sa muna jin daɗin cin aful kowace rana!

YADDA MUKA KOYI GASKIYA

Lokacin da iyayena suka soma sanin Jehobah, ina ’yar shekara shida. Ɗansu na fari ya mutu jim kaɗan bayan an haife shi. Iyayena sun yi baƙin ciki sosai kuma suka tambayi firist ɗin cocinsu, “Ina ɗanmu Johnny yake?” Sai firist ɗin ya ce ba a yi masa baftisma ba, saboda haka, bai je sama ba kuma ya ce idan iyayena suka ba shi kuɗi, zai yi addu’a don Johnny ya je sama. Da iyayena suka ji haka, ba su ji daɗi ba kuma suka daina sha’ani da firist ɗin. Duk da haka, suna so su san abin da ya faru da Johnny.

Wata rana mahaifiyata ta sami wata ƙasida mai jigo Where Are the Dead? (Ina Matattu Suke?) da Shaidun Jehobah suka buga. Sai ta karanta ƙasidar. Sa’ad da mahaifinmu ya dawo, cike da farin ciki ta ce: “Na san inda Johnny yake! Yana barci yanzu, amma wata rana zai tashi.” Sai mahaifinmu ya ɗauki ƙasidar kuma ya karanta gaba ɗaya. Sa’ad da iyayena suka koyi cewa Littafi Mai Tsarki ya ce waɗanda suka mutu suna barci kuma za a yi tashin matattu a nan gaba, sai hankalinsu ya kwanta.—M. Wa. 9:5, 10; A. M. 24:15.

Abin da suka koya ya inganta rayuwarsu, sun sami ƙarfafa kuma sun yi farin ciki. Suka amince Shaidun Jehobah su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su kuma suka soma halartan taro a wani ƙaramin ikilisiya da ke Wakaw. Yawancin ’yan ikilisiya sun fito daga Yukiren ne. Nan da nan iyayena suka soma wa’azin bishara.

Jim kaɗan bayan haka, sai muka ƙaura zuwa yankin British Columbia kuma ’yan’uwa a wata ikilisiya da ke wurin sun marabce mu da hannu bibbiyu. Ba na mantawa da yadda muke himmar shirya Hasumiyar Tsaro da ake nazarinsa a taro ranar Lahadi. Yayin da muke ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah sai muka soma shaida yadda Jehobah yake yi mana albarka.

Bayyana imaninmu a makaranta bai kasance da sauƙi sa’ada da muke ƙanana ba. Amma muna shirin gabatarwa na wa’azi da ake yi kowane wata don mu gudanar a Taron Hidima kuma hakan ya taimaka wa ni da ƙanwata Eva sosai. Wannan tsarin ya taimaka mana mu san yadda za mu yi wa mutane wa’azin bishara duk da cewa mu masu kunya ne. Ina godiya cewa an horar da mu a yin wa’azi!

Masu hidima ta cikakken lokaci sukan sauka a gidanmu kuma hakan na sa mu yara farin ciki sosai. Alal misali, muna jin daɗi sa’ad da mai kula da da’irarmu mai suna Jack Nathan ya ziyarci ikilisiyarmu. * Yana ba mu labarai masu daɗi kuma yana yaba mana. Hakan ya sa mun kuɗiri niyyar bauta wa Jehobah da aminci.

Na tuna wani lokacin da na ce: “Ina son in zama kamar ɗan’uwa Nathan sa’ad da na girma.” Daga baya ne na gane cewa misalin da ya kafa ya taimaka min in biɗi hidima ta cikakken lokaci. Sa’ad da na kai ’yar shekara 15, sai na yanke shawarar bauta wa Jehobah. A shekara ta 1942 ne aka yi wa ni da ƙanwata Eva baftisma.

MUN FUSKANCI GWAJI

Sa’ad da aka soma Yaƙin Duniya na biyu, sai aka soma kishin ƙasa sosai. Wata malama Scott ta kori ƙannena uku daga makaranta. Domin sun ƙi sara wa tuta. Sai ta sami malamarmu kuma ta gaya mata ta kore ni. Amma malamarmu ta ce, “Ƙasarmu ta ba wa kowa ’yanci da kuma izinin ƙin saka hannu a batutuwa na kishin ƙasa.” Malama Scott ta matsa wa malamarmu sosai, duk da haka, malamata ta ce: “Wannan shawarata ce.”

Malama Scott ta ce: “Wannan ba shawarar ki ba ce. Zan kai ƙarar ki idan ba ki kore Melita daga makaranta ba.” Saboda haka, malamarmu ta gaya wa iyayena cewa wajibi ne ta kore ni don ba ta son ta rasa aikinta, ko da ta san cewa hakan bai dace ba. Amma mun samu littattafai da za mu riƙa karantawa a gida. Jin kaɗan bayan haka sai muka ƙaura zuwa wani wuri da ke nisan kilomita 32 kuma muka shiga wata makaranta a wurin.

Yaƙin ya sa doka ta hana mu rarraba littattafanmu, amma mun yi amfani da Littafi Mai Tsarki wajen yin wa’azi gida-gida. Wannan yanayin ya sa mun ƙware a yin amfani da Littafi Mai Tsarki kai tsaye wajen yin wa’azi. Sakamakon haka, muka san Littafi Mai Tsarki sosai kuma muka kyautata ibadarmu ga Jehobah.

HIDIMA TA CIKAKKEN LOKACI

Na ƙware a gyaran gashi har ma na sami wasu lambobin yabo

Sa’ad da ni da Eva muka sauke karatu, sai muka soma hidimar majagaba ba tare da ɓata lokaci ba. Na soma aiki a wani shagon sayar da kayan abinci. Daga baya, na koyi yadda ake gyaran gashi na wata shida da yake aiki ne da na yi sa’ad da nake gida. Sai na soma aiki a wani shagon gyaran gashi kwana biyu a mako. Ƙari ga haka, ina horar da mutane a sana’ar sau biyu a wata. Ta hakan ne nake samun kuɗin biyan bukata yayin da nake hidimar majagaba.

A shekara ta 1955, na yi shirin halartan babban taro na “Triumphant Kingdom” (Mulki Mai Nasara) a biranen New York da ke Amirka, da kuma Nuremberg a ƙasar Jamus. Amma kafin in kama hanya zuwa New York, sai Allah ya haɗa ni da Ɗan’uwa Nathan Knorr da ya zo daga hedkwatarmu. Hakan ya faru ne sa’ad da shi da matarsa sun zo halartan wani babban taro da aka yi a birnin Vancouver da ke ƙasar Kanada. Sai na gyara wa matar Ɗan’uwa Knorr gashinta. Abin ya burge ɗan’uwa Knorr sosai kuma ya ce yana son ganina. Yadda muka haɗu da ɗan’uwa Knorr ke nan. Na gaya masa cewa ina shirin tafiya birnin New York kafin in wuce zuwa ƙasar Jamus. Ɗan’uwa Knorr ya gayyace ni zuwa Bethel da ke Brooklyn don in yi aiki na kwana tara.

Wannan tafiyar da na yi ta canja rayuwata. Mun haɗu da wani saurayi mai suna Theodore Jaracz, (ana kiransa Ted). Ba da daɗewa ba bayan muka haɗu, sai ya tambaye ni, “Ke majagaba ce?” Hakan ya ba ni mamaki kuma na ce, “A’a.” Ashe abokiyata mai suna LaVonne ta ji, sai ta ce, “E, ita majagaba ce.” Hakan ya ɗan birkitar da Ted, kuma ya ce wa abokiyata LaVonne, “Wa ta fi sani, ke ko ita?” Na bayyana masa cewa na yi hidimar majagaba kuma da zarar na koma gida daga taron, zan soma kuma.

NA AURI MAI ƘAUNAR JEHOBAH SOSAI

An haifi Ted a jihar Kentucky da ke Amirka a shekara ta 1925. Ya yi baftisma sa’ad da yake shekara 15 kuma ya soma hidimar majagaba shekaru biyu bayan haka duk da cewa shi kaɗai ne a iyalinsu da ya zama Mashaidi. Ya yi kusan shekara 67 yana hidima ta cikakken lokaci.

Ɗan’uwa Ted ya sauke karatu a aji na bakwai na Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gileyad a watan Yuli, a shekara ta 1946 sa’ad da yake shekara 20. Bayan haka, ya yi hidimar mai kula da da’ira a birnin Cleveland da ke jihar Ohio. Shekaru huɗu bayan haka, aka naɗa shi mai kula da ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasar Ostareliya.

Ɗan’uwa Ted ya halarci babban taron da aka yi a birnin Nuremberg da ke Jamus, kuma muka yi hira. Soyayya ta soma haɓaka a tsakaninmu. Na yi farin ciki cewa ya kafa maƙasudai da za su taimaka masa ya bauta wa Jehobah da dukan zuciyarsa. Shi mai natsuwa ne kuma mai son ibada sosai amma yana alheri da fara’a. A ra’ayina, yana son taimaka wa mutane. Bayan wannan babban taron, ɗan’uwa Ted ya koma Ostareliya, ni kuma na koma Vancouver. Amma mun ci gaba da aika wa juna wasiƙa.

Bayan Ted ya yi shekaru biyar a Ostareliya, sai ya koma Amirka. Daga baya, ya zo Vancouver don ya yi hidimar majagaba. Na yi farin ciki cewa ’yan gidanmu sun so shi sosai. Yayana Michael yana yawan damuwa da ni musamman ma idan ya ga cewa wani saurayi yana so na. Amma jininsu ya haɗu da Ted. Ya ce min: “Melita, Allah ya ba ki saurayi mai hankali. Kada ki yi wasa, ki riƙe shi hannu bibiyu don kada ki rasa shi.”

Bayan mun yi aure a 1956, kuma mun ji daɗin yin hidima ta cikakken lokaci tare

Ni ma na so Ted sosai kuma muka yi aure a ranar 10 ga watan Disamba, shekara ta 1956. Muka yi hidimar majagaba tare a birnin Vancouver. Bayan haka muka koma jihar California kuma muka ci gaba da hidimarmu ta majagaba. Sai aka tura mu hidimar kula da da’ira a jihohin Missouri da Arkansas. Mun yi shekaru 18 muna ƙaura daga wani gida zuwa wani gida kowane mako yayin da muke hidimar a yankuna dabam-dabam a ƙasar Amirka. Mun ji daɗin hidimarmu da kuma cuɗanya da ’yan’uwa maza da mata. Hakan ya taimaka sosai duk da cewa tafiya kowane mako zuwa wurare dabam-dabam bai da sauƙi.

Mijina Ted ba ya wasa da dangantakarsa da Jehobah kuma hakan yana burge ni. Ya ɗauki hidimarsa ga Allah Maɗaukakin Sarki da muhimmanci sosai. Muna son karatu da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki tare. Kafin mu kwanta da dare, mukan durƙusa kusa da gadonmu kuma sai ya yi mana addu’a. Bayan haka, sai kowa ya yi addu’arsa. A duk lokacin da wani abu yake damun Ted sosai, zai sauka daga kan gado ya sake durƙusa ya daɗe yana addu’a. Yadda yake son yin addu’a game da duk wani batun da yake damunsa yana burge ni sosai.

Wasu shekaru bayan mun yi aure, mijina Ted ya gaya min cewa zai soma cin gurasa da kuma shan ruwa inabi a taron tuna mutuwar Yesu. Ya ce: “Na yi addu’a game da batun sosai don in tabbata cewa abin da Jehobah yake so in yi ke nan.” Hakan bai ba ni mamaki sosai ba cewa an shafe shi da ruhu mai tsarki don ya je sama ba. Tun daga lokacin nan, na ɗauki hakan gata na tallafa wa ɗaya daga cikin ’yan’uwan Kristi.—Mat. 25:35-40.

MUN SOMA WATA HIDIMA

A shekara ta 1974, wani abin mamaki ya faru da mu, wato an ba wa mijina Ted gatan zama memban Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. Da shigewar lokaci, aka ce mu je hidima a Bethel da ke Brooklyn. Na yi aiki a matsayin mai kula da ɗaki da kuma wajen gyaran gashi yayin da mijina yake hidima a matsayinsa na memban Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah.

Ayyukan mijina Ted yake yi sun ƙunshi zuwa ziyara a ofisoshin Shaidun Jehobah dabam-dabam. Ya mai da hankali ga ƙasashen gabashin Turai da ke ƙarƙashin mulkin tarayyar Soviet, wato ƙasashen da aka saka takunkumi a aikinmu. Akwai lokacin da muka je hutu a ƙasar Sweden, sai mijina ya gaya min: “Melita, an hana wa’azin bishara a Polan, kuma zan so in taimaka wa ’yan’uwa da ke wurin.” Saboda haka, muka nemi bisa kuma muka je Polan. Ted ya haɗu da wasu ’yan’uwa da ke kula da aikinmu a ƙasar kuma suka taka da kafa suna tafiya don kada kowa ya ji abin da suke faɗa. Sun yi kwanaki huɗu suna taro, amma na yi farin ciki sosai cewa Ted ya gamsu don yadda ya taimaka wa ’yan’uwansa, wato Shaidun Jehobah da ke ƙasar Polan.

A watan Nuwamba na shekara ta 1977 ne muka sake ziyartan Polan. ’Yan’uwa F. W. Franz da Daniel Sydlik da mijina Ted ne suka kai ziyara ta farko a Polan a madadin Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. A lokacin, ba a ɗaga takunkumi a kan aikinmu ba har ila. Duk da haka, mambobi uku na Hukumar sun sami damar zuwa birane dabam-dabam don ƙarfafa masu kula da majagaba da waɗanda suka daɗe suna bauta wa Jehobah.

Ted da wasu a Ma’aikatan Shari’a a ƙasar Moscow bayan gwamnati ta yi rajistar aikinmu

Sa’ad da ɗan’uwa Milton Henschel da mijina Ted suka ziyarci Polan a shekarar da ta biyo baya, sai suka haɗu da ma’aikata da suka soma amincewa da Shaidun Jehobah da kuma wa’azin bishara. A shekara ta 1982, gwamnatin ƙasar Polan ta amince mu yi babban taro na kwana ɗaya. A shekara ta 1983, mun sami damar gudanar da manyan taro. Mun yi hayar majami’u don gudanar da yawancin taron. A shekara ta 1985, mun gudanar da manyan taro guda huɗu a filayen wasa masu girma. Yayin da ake shirin gudanar da manyan taro a watan Mayu na shekara ta 1989, sai gwamnatin Polan ta ba wa Shaidun Jehobah ’yancin gudanar da addininsu. Hakan ya sa mijina Ted farin ciki sosai.

Taron Gunduma a ƙasar Polan

FAMA DA RASHIN LAFIYA

Sa’ad da muke zuwa taron keɓe ofishin Shaidun Jehobah a Afirka ta Kudu a shekara 2007, sai hawan jini ya soma damun mijina Ted a Ingila. Likita ya gaya masa cewa ya ɗaga tafiyarsa. Bayan ya sami sauki, sai muka koma Amirka. Amma ’yan makonni bayan haka, sai ya kamu da cutan shan inna kuma ɓangaren jikinsa na dama ya shanye.

Ted bai sami sauƙi da wuri ba, kuma bai samu ya koma bakin aiki a kan lokaci ba. Mun gode cewa rashin lafiyar bai shafi yadda yake magana ba. Ko da yake ya ɗan naƙasa, amma ya ci gaba da aikinsa. Sa’ad da membobin Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah suna taro, yakan kira su a taron ta wayar tarho da ke falonmu don a gudanar da taron tare da shi.

Ted ya amfana sosai daga jinyar da aka yi masa a sashen kula da marasa lafiya da ke Bethel kuma ya yi godiya saboda haka. Da sannu a hankali, sai ya soma tafiya. Ta hakan, ya koma bakin aikinsa, ya kasance da fara’a.

Shekaru uku bayan haka, cutar shan inna ta sake addabar shi kuma ya mutu a ranar Laraba, 9 ga watan Yuni, 2010. Ba zan iya kwatanta yadda nake ji saboda wannan babban rashin da na yi ba duk da cewa na san zai gama hidimarsa a duniya. Amma na gode wa Jehobah don abubuwan da na yi don in tallafa wa Ted. Mun yi shekaru 53 muna hidima ta cikakken lokaci tare kuma na gode wa Jehobah don yadda Ted ya taimaka min in kyautata dangantakata da Jehobah. Yanzu, ina da tabbaci cewa yana jin daɗin hidimarsa a sama.

FAMA DA WASU ƘALUBALE

Ina jin daɗin yin aiki da kuma horar da mutane a shagon gyaran gashi

Shekaru da yawa da na yi tare da mijina muna jin daɗi hidima ya sa jimrewa da ƙalubalen da nake fuskanta yanzu bai da sauƙi. Ni da mijina Ted muna farin cikin karɓan baƙin da ke zuwa Bethel da kuma Majami’ar Mulki. Amma yanzu mijina ya mutu kuma ban da ƙarfi kamar dā. Ƙari ga haka, ba na iya cuɗanya da mutane kamar dā. Duk da haka, ina jin daɗin kasancewa tare da ’yan’uwana maza da mata a Bethel da kuma a ikilisiya. Aiki a Bethel bai da sauƙi, amma bauta wa Allah a wannan hanyar yana sa ni farin ciki. Har ila, ina son wa’azin bishara ko da yake ba na iya tsayawa na tsawon lokaci. Amma ina wa mutane wa’azi a titi kuma ina nazarin Littafi Mai Tsarki da su.

Idan na yi la’akari da munanan abubuwan da ke faruwa a wannan duniyar, ina gode wa Jehobah cewa ya ba ni damar yi masa hidima kuma ya ba ni abokin aure mai ƙaunarsa! Hakika albarkar Jehobah ta sa na wadata.—Mis. 10:22.

^ sakin layi na 13 An wallafa tarihin Jack Nathan a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Satumba, shekara ta 1990, shafuffuka na 10-14 a Turanci..