TATTAUNAWA TSAKANIN SHAIDUN JEHOBAH DA MUTANE
Yaushe Ne Mulkin Allah Ya Soma Sarauta? (Sashe na 2)
Tattaunawar da ke gaba misali ne na yadda Shaidun Jehobah suke yi wa mutane wa’azi. A ce wani Mashaidi mai suna Cameron ya sake ziyartar wani mutum mai suna Jon.
BITAR MAFARKIN NEBUCHADNEZZAR
Cameron: Barkanmu da sake saɗuwa, Jon. Ina jin daɗin tattaunawar da muke yi a kan Littafi Mai Tsarki kowane mako. * Ya kake?
Jon: Lafiyata ƙalau.
Cameron: To, madalla. A wancan karon, mun tattauna dalilin da ya sa Shaidun Jehobah suka ce Mulkin Allah ya soma sarauta a shekara ta 1914. * A tattaunawarmu, mun sami ƙarin haske a kan wannan batun daga wani annabcin da ke littafin Daniyel sura 4. Ka tuna abin da wurin ya ce?
Jon: Mafarkin da Sarki Nebuchadnezzar ya yi ne game da wani babban itace.
Cameron: Haka ne. A cikin mafarkinsa, Nebuchadnezzar ya ga wani babban itace da tsawonsa ya kai sama. Ya ji wani mala’ikan Allah ya ce a sare itacen, amma a bar gindinsa da saiwarsa a ƙasa. Bayan “lokatai guda bakwai,” itacen zai sake girma. * Mun kuma tattauna dalilin da ya sa muka ce wannan annabcin ya cika a hanyoyi biyu. Ka tuna bayani da muka yi a kan cikarsa na farko?
Jon: Hakan ya faru da Nebuchadnezzar ne da kansa ko? Ya haukace har tsawon shekaru bakwai.
Cameron: Daidai ne. An dakatar da mulkin Nebuchadnezzar a lokacin da ya haukace. Amma a cikarsa na biyu, za a dakatar da sarautar Allah bisa duniya har tsawon lokatai bakwai. Kamar yadda muka gani, waɗannan lokatai bakwai sun soma a lokacin da aka halaka Urushalima a shekara ta 607 kafin zamaninmu. Daga wannan lokacin, ba a sake yin wani sarki a duniya da ya wakilci Jehobah ba. Amma a ƙarshen lokatai bakwai ɗin, Allah zai naɗa sabon Sarki a sama bisa mutanensa. A taƙaice dai, Mulkin Allah a samaniya zai soma sarauta ne a ƙarshen lokatai bakwai ɗin nan. Yanzu, mun riga mun ga lokacin da waɗannan lokatai bakwai suka soma. Idan muka san tsawon waɗannan lokatan, za mu san lokacin da Mulkin Allah ya soma sarauta. Ka fahimci bayanin da na yi yanzu?
Jon: E. Wannan bitar ta taimaka mini in tuna abin da muka tattauna kwanaki.
Cameron: Da kyau. To bari mu ci gaba da tattaunawarmu don mu san tsawon lokatai bakwai ɗin. Na yi bincike a kan wannan batun domin in tuna wa kaina wasu muhimman bayanai. Zan yi ƙoƙari in bayyana shi daidai gwargwado.
Jon: To.
LOKATAI BAKWAI SUN ƘARE, AN SHIGA KWANAKI NA ƘARSHE
Cameron: A cikar farko na annabcin da ya shafi Nebuchadnezzar, lokatai bakwai ɗin suna nufin
shekaru bakwai ne a zahiri. Amma a cikarsa na biyu da ya shafi Mulkin Allah, lokatai bakwai ɗin sun fi shekaru bakwai na zahiri.Jon: Me ya sa ka faɗi hakan?
Cameron: Ka tuna cewa lokatai bakwai ɗin sun soma sa’ad da aka halaka Urushalima a shekara ta 607 kafin zamaninmu. Idan muka ƙirga shekaru bakwai a zahiri daga wannan shekarar, za mu tsaya a shekara ta 600 kafin zamaninmu. Amma babu wani gagarumin abu da ya faru da Mulkin Allah a wannan shekarar. Ban da haka ma, kwanakin baya mun tattauna cewa a lokacin da Yesu yake duniya, shekaru da yawa bayan somawar shekaru bakwai ɗin, Yesu ya nuna cewa waɗannan shekarun ba su ƙare ba tukun.
Jon: Oho, yanzu na tuna.
Cameron: Saboda haka, waɗannan lokatan ba shekaru bakwai na zahiri ba ne, amma tsawonsu ya fi hakan sosai.
Jon: Shekaru nawa ne to?
Cameron: Littafin Ru’ya ta Yohanna yana da alaƙa da littafin Daniyel kuma shi ne ya taimaka mana mu san tsawon waɗannan lokatai bakwai. Littafin ya nuna cewa lokatai uku da rabi sun yi daidai da kwanaki 1,260. * Da hakan, in ka ninka lokatai uku da rabi sau biyu, za ka sami lokatai bakwai kuma hakan zai yi daidai da kwanaki 2,520. Ka fahimci wannan bayanin?
Jon: E. Amma ban ga yadda hakan ya nuna cewa Mulkin Allah ya soma sarauta a shekara ta 1914 ba.
Cameron: To, bari mu ga yadda za mu iya tabbatar da alaƙarsu. A wasu lokatai, ana ƙirgen shekara guda a matsayin rana guda a cikin annabcin Littafi Mai Tsarki. * Idan muka bi ƙa’idar rana guda a matsayin shekara guda, lokatai bakwai ɗin za su zama shekaru 2,520. Idan muka ƙirga shekaru 2,520 daga shekara ta 607 kafin zamaninmu, za mu tsaya a shekara ta 1914. * Ta hakan ne muka sani cewa lokatai bakwai ɗin sun ƙare a shekara ta 1914, kuma shekarar da Yesu ya soma sarauta a Mulkin Allah ke nan. Kuma a shekara ta 1914 ne annabcin da aka yi a Littafi Mai Tsarki game da kwanaki na ƙarshe ya soma cika.
Jon: Waɗanne irin aukuwa ke nan?
Cameron: Ka yi la’akari da kalmomin Yesu da aka rubuta a Matta 24:7. A cikin bayanin da Yesu ya yi a kan lokacin da zai soma sarauta a sama, Yesu ya ce: “Al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki kuma za ya tasa wa mulki: za a yi yunwa da rayerayen duniya wurare dabam-dabam.” Ka lura cewa Yesu ya ce za a yi yunwa mai tsanani da kuma girgizar ƙasa a wannan lokacin. Babu shakka, waɗannan abubuwan sun addabi ’yan Adam sosai a shekarun da suka wuce, ko ba haka ba?
Jon: Haka ne.
Cameron: A wannan ayar ma Yesu ya annabta cewa za a yi yaƙi a lokacin da zai bayyana a matsayinsa na Sarkin Mulkin Allah. Kuma littafin Ru’ya ta Yohanna ya nuna cewa a kwanaki na ƙarshe, za a yi yaƙe-yaƙe a duniya gaba ɗaya, ba a ɓangare guda kawai ba. * Ka tuna lokacin da Yaƙin Duniya na Ɗaya ya ɓarke?
Jon: Ai a shekara ta 1914 ne, shekarar da kake cewa Yesu ya soma mulki! Ban taɓa tunanin hakan ba.
Cameron: Idan muka haɗa bayanan nan, wato, annabcin lokatai bakwai ɗin da kuma wasu annabce-annabce a Littafi Mai Tsarki game da kwanaki na ƙarshe, za mu ga cewa bayanin nan gaskiya ne. Shaidun Jehobah sun yi imani cewa Yesu ya soma sarauta a shekara ta 1914, kuma kwanaki na ƙarshe ma sun soma a wannan shekarar ne.Jon: A gaskiya, ina ƙoƙarin fahimtar wannan sabon bayanin.
Cameron: Ai na san hakan ba zai zama maka da sauƙi ba. Ko ni ma ban fahimci wannan bayanin da sauri ba. Amma ina fatan tattaunawarmu ta taimake ka ka ga cewa ko da yake Littafi Mai Tsarki bai ambata shekara ta 1914 ba, koyarwar Shaidun Jehobah game da wannan shekarar daga Littafi Mai Tsarki ne.
Jon: Hakika, na daɗe ina gaya maka cewa kuna burge ni sosai a yadda kuke yin koyarwa bisa ga Littafi Mai Tsarki. Ba ra’ayinku kuke koyarwa ba. Amma har ila ina mamakin abin da ya sa wannan batun yake da wuyar fahimta. Me ya sa Allah bai gaya mana kawai a cikin Littafi Mai Tsarki cewa a shekara ta 1914 ne Yesu zai soma sarauta a sama ba?
Cameron: Wannan tambaya ce mai kyau Jon. Kai, akwai abubuwa da yawa da Littafi Mai Tsarki bai bayyana su filla-filla ba. To don me Allah ya sa a rubuta Littafi Mai Tsarki a hanyar da sai mutum ya yi ƙoƙari sosai kafin ya fahimci abin da ke cikinsa? Ina ganin wannan ne batun da za mu tattauna idan na sake dawowa.
Jon: Ina sauraron zuwanka.
Akwai wani batu a cikin Littafi Mai Tsarki da za ka so ka sami ƙarin bayani a kai? Za ka so ka sami ƙarin bayani a kan wasu daga cikin koyarwa ko kuma abubuwan da Shaidun Jehobah suka yi imani da su? Idan haka ne, ka sami Shaidun Jehobah don su yi maka bayani a kan waɗannan batutuwan. Za su yi farin cikin tattaunawa da kai.
^ sakin layi na 5 Shaidun Jehobah suna tattauna Littafi Mai Tsarki kyauta da maƙwabtansu ta wajen bin wani tsari na nazari.
^ sakin layi na 7 Ka duba talifin nan “Tattaunawa Tsakanin Shaidun Jehobah da Mutane—Yaushe Ne Mulkin Allah Ya Soma Sarauta?—Sashe na 1” a Hasumiyar Tsaro ta Nuwamba–Disamba na 2014.
^ sakin layi na 9 Ka duba Daniyel 4:23-25.
^ sakin layi na 22 Ka duba Ru’ya ta Yohanna 12:6, 14.
^ sakin layi na 24 Ka duba Littafin Lissafi 14:34; Ezekiyel 4:6.
^ sakin layi na 24 Ka duba jadawalin nan, “Mafarkin Nebuchadnezzar Game da Itace.”
^ sakin layi na 28 Ka duba Ru’ya ta Yohanna 6:4.
^ sakin layi na 30 Ka duba babi na 9 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa. Za ka iya samunsa a dandalin www.dan124.com/ha.