ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZA KA IYA FAHIMTAR LITTAFI MAI TSARKI
Samun Taimako don Fahimtar Littafi Mai Tsarki
A ce ka ziyarci wata ƙasar da ba ka taɓa zuwa ba. Sai ka ga cewa mutanen da al’adunsu da abincinsu da wasu abubuwa ba irin wanda ka saba gani ba ne. Babu shakka, za ka ji wani iri.
Za ka iya jin hakan a lokaci na farko da ka karanta Littafi Mai Tsarki. Za ka ga abubuwa da yawa na zamanin dā da ba ka taɓa ji ba. A ciki za ka ga mutanen da ake kira Filistiyawa da waɗansu irin al’adu kamar na ‘tsatsage tufafi’ ko wani irin abinci da ake kiran manna. (Fitowa 16:31; Joshua 13:2; 2 Sama’ila 3:31) Waɗannan abubuwan za su iya ruɗar da kai. Kamar misalin zuwa wata ƙasa da muka ambata a sama, babu shakka, za ka yi farin ciki idan wani ya zo ya yi maka bayani game da ƙasar. Ko ba haka ba?
TAIMAKO A ZAMANIN DĀ
A lokacin da aka soma rubuta Littafi Mai Tsaki, wato a ƙarni na 16 kafin haihuwar Yesu, Allah ya riga ya shirya abubuwan da za su taimaki mutane su fahimci abin da ke cikinsa. Alal misali, Musa wanda shi ne ya fara yi wa al’umar Isra’ila ja-gora ya “bayyana” rubutun.—Kubawar Shari’a 1:5.
Wajen ƙarnuka goma bayan zamanin Musa, ƙwararrun malamai sun ci gaba da bayyana Littafi Mai Tsarki. A shekara ta 455 kafin haihuwar Yesu, Yahudawa da dama, har da ƙananan yara sun taru a birnin Urushalima. Malaman Littafi Mai Tsarki kuma suka “karanta daga littafin dokokin Allah sosai.” Bayan haka, sai “suka fassara musu, saboda haka, jama’a suka fahimci karatun.”—Nehemiya 8:1-8, Littafi Mai Tsarki.
Ƙarnuka biyar bayan hakan, Yesu ma ya koya wa mutane Littafi Mai Tsarki, har mutane suna kiran sa malami. (Yohanna 13:13) Ya koyar da jama’a da kuma mutane ɗaɗɗaya. Alal misali, ya yi Huɗuba a kan dutse a gaban jama’a mai girma, kuma sai “taron mutane suka yi mamaki da koyarwarsa.” (Matta 5:1, 2; 7:28) A shekara ta 33, Yesu ya tattauna da almajiransa biyu sa’ad da suke tafiya kusa da wani ƙauye da ke dab da Urushalima. Yesu ya yi ta “bayyana” musu Nassosi.—Luka 24:13-15, 27, 32.
Almajiran Yesu ma sun koya wa mutane Kalmar Allah. Akwai wani lokaci da wani Bahabashe yake karanta wasu ayoyin Nassosi. Sai wani almajiri mai suna Filibus ya tambaye shi cewa: “Ka fahimci abin da kake karantawa?” Bahabashen ya ce, “Yaya zan iya, sai ko wani ya bishe ni?” Bayan haka, sai Filibus ya bayyana masa ma’anar ayoyin.—Ayyukan Manzanni 8:27-35.
TAIMAKO A ZAMANINMU
Shaidun Jehobah ma suna kamar waɗannan malamai na zamanin dā domin a yau, suna koya wa mutane Littafi Mai Tsarki a ƙasashe 239 a faɗin duniya. (Matta 28:19, 20) Suna taimaka wa mutane sama da miliyan tara a kowane mako don su fahimci Littafi Mai Tsarki. Da yawa cikin mutanen da suke koya wa Littafi Mai Tsarki ba Kiristoci ba ne. Wannan nazarin kyauta ce kuma za a iya yin sa a gidanka ko a wani wurin da ka fi so. Ana ma yin nazarin da wasu ta tarho ko kwamfuta.
Idan kana son ƙarin bayani a kan yadda za ka amfana daga wannan tsarin, don Allah ka tuntuɓi kowane Mashaidin Jehobah. Za ka lura cewa Littafi Mai Tsarki bai da wuya ainun, amma yana da ‘amfani ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adalci,’ domin ka “zama kamili, shiryayye sarai domin kowane managarcin aiki.”—2 Timotawus 3:16, 17.