Ta Yaya Za Ka Daidaita Yadda Kake Shan Giya?
Wasu mutane sukan kara yawan giyan da suke sha idan sun gaji, ko sun kadaita ko sun rasa abin yi. Kana shan giya fiye da yadda ka saba? Idan haka ne, ya za ka tabbata cewa giyar da kake sha ba ta wuce kima ko ta zama maka jaraba ba? Ga wasu abubuwa da za su taimaka maka ka daidaita yadda kake shan giya.
Me ake nufi da shan giya daidai wa daida?
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ka hada kai da masu buguwa.”—Karin Magana 23:20.
Ka yi tunani a kan wannan: Littafi Mai Tsarki bai hana shan giya daidai wa daida ba. (Mai-Wa’azi 9:7) Amma ya yi magana a kan buguwa da kuma zama bawa ga shan giya wato shan giya da yawa. (Titus 2:3; Ishaya 5:11) Ko da ba ka bugu ba, shan giya da yawa zai iya sa ka tsai da shawarwarin da ba su dace ba, kuma zai iya jawo maka rashin lafiya ko ya bata dangantakarka da mutane.—Karin Magana 23:29, 30.
Hukumomi a wurare da dama sun nuna bambancin da ke tsakanin shan giya daidai wa daida da kuma shan giya fiye da kima. Kuma suna kwatanta hakan da yawan kwalaban da mutum yake sha a rana ko yawan ranakun da yake shan giya a cikin mako guda. a Yadda shan giya yake shafan mutane ya bambanta, kuma a wasu lokuta gwamma kar mutum ya sha giya. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:
“Kwalba daya ko biyu ma za su iya zama matsala—alal misali:
Idan kana tuki ko kana aiki da wani inji.
Idan mace tana da ciki ko tana shayarwa.
Idan kana shan wasu irin magunguna.
Idan kana wani irin rashin lafiya.
Idan ba ka iya daina shan giya a lokacin da kake so.”
Abubuwan da za su nuna maka cewa giyar da kake sha ta yi yawa
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bari mu gwada, mu bincika hanyoyinmu.”—Makoki 3:40.
Ka yi tunani a kan wannan: Idan kana bincika yadda kake shan giya a kai a kai kuma kana yin gyara idan da bukata, shan giya ba zai yi maka lahani ba. Ga wasu abubuwa da za su nuna maka cewa giyar da kake sha ta soma yawa.
Sai ka sha giya ne kake farin ciki. Kana ganin sai ka sha giya kafin hankalinka ya kwanta, ko ka ji dadin shakatawa da abokanka, ko kuma kana shan giya don ka mance matsalolinka.
Kana shan giya fiye da yadda ka saba. Kana shan giya a kai a kai, ko karfin giyar da kake sha yanzu ya fi na dā. Kana sha fiye da yadda ka saba kafin ka ji daidai.
Giyar da kake sha ya jawo maka matsala a gida ko a wurin aikinka. Alal misali, kana kashe kudi wajen sayan giya fiye da kudin da kake samu.
Kana yin abin da bai dace mutum yi ba bayan ya sha giya, kamar yin tuki, ko iyo, ko aiki da wani inji.
Wasu sun gaya maka cewa ba sa son yadda kake shan giya. In sun fadi hakan sai ka ji haushi. Kana shan giya a boye ko kana yin karya a kan yawan giya da kake sha.
Ka kasa daina sha. Ka yi kokarin rage yawan gida da kake sha ko ka daina sha amma ka kasa.
Abubuwa biyar da za su taimaka maka ka daidaita yadda kake shan giya
1. Ka yi shiri.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Shirye-shirye na mai kwazo lallai sukan kai ga [nasara].”—Karin Magana 21:5.
Ga abin da za ka yi: Ka zabi ranakun da za ka sha giya a mako. Ka kimanta yawan giyan da za ka sha a ranankun. Kuma ka zabi a kalla ranaku biyu da ba za ka sha giya ba kowane mako.
Wata kungiya da take ilimantar da mutane a kan shan giya a kasar Turai ta ce: “Abin da zai fi taimaka wa mutum kar shan giya ta zama masa jaraba shi ne, ya rika yin wasu kwanaki ba ya sha.”
2. Ka yi abin da ka shirya.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku gama aikin da irin zuciyar da kuka fara.”—2 Korintiyawa 8:11.
Ga abin da za ka yi: Ka yi hankali da yawan giyan da kake sha. Ka lura da karfin giyan da kake sha ta wajen duba abin da aka rubuta a jikin kwalbar. Hakan zai sa ka san yadda za ka sha giyar daidai wa daida. Ka samo wasu abin sha marar lahani, da ba giya ba, sa’an nan ka ajiye su a inda za ka yi saurin ganinsu.
Wata kungiya da ake kira National Institute on Alcohol Abuse and Alcoholism a Amirka, ta ce: “Za ka iya kāre kanka daga matsalolin da ke tattare da shan giya idan ka yi wasu ’yan canje-canje.”
3. Kar ka canja abin da ka shirya yi.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “In kun ce ‘I,’ ya tsaya kan ‘I’ din kawai, in kuwa kun ce ‘A,a,’ ya tsaya kan ‘A’a’ din kawai.”—Yakub 5:12, Littafi Mai Tsarki.
Ga abin da za ka yi: Ka kasance a shirye don ka ce “A’a” idan wani ya ba ka giya a lokacin da ka shirya cewa ba za ka sha giya ba, amma ka yi hakan a hanyar da ba zai bata wa mutumin rai ba.
Kungiyar National Institute on Alcohol Abuse and Alcoholism a Amirka, ta ce: “Idan ka yi saurin ce a’a, hakan zai taimaka maka ka cim ma burinka.”
4. Ka rika tunani a kana amfanin da za ka samu.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gwamma karshen abu da farawarsa.”—Mai-Wa’azi 7:8.
Ga abin da za ka yi: Ka rubuta dalilai da suka sa kake so ka rage yawan giya da kake sha. Za ka iya rubuta abubuwa kamar yadda hakan zai inganta barcinka, da lafiyarka, da yadda kake kashe kudi, da kuma dangantakarka da mutane. Idan kana magana da mutane a kan matakin da ka dauka, ka rika magana a kan yadda hakan zai amfane ka, ba yadda hakan yake maka wuya ba.
5. Ka roki Allah ya taimaka maka.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zan iya yin kome ta wurin . . . wanda yake karfafa ni.”—Filibiyawa 4:13.
Ga abin da za ka yi: Idan yadda kake shan giya yana damunka, ka roki Allah ya taimake ka. Ka roke shi ya ba ka karfin da kake bukata don ka iya kame kanka. b Ka bincika Kalmarsa, wato Littafi Mai Tsarki don ka ga shawarwari masu kyau da za su iya taimaka maka. Da taimakon Allah, za ka iya daidaita yadda kake shan giya.
a Alal misali, a Amirka, sashen da ake kira Department of Health and Human Services ya ce shan giya fiye da kima shi ne, “mace ta sha wajen kwalabai 4 ko fiye da hakan a rana ko kwalabai 8 ko fiye da hakan a mako, sa’an nan namiji ya sha wajen kwalabai 5 ko fiye da hakan a rana ko kwalabai 15 ko fiye da hakan a mako.” Girman kwalaban ya dangana da kasar da kake, don haka likitanka ne zai iya gaya maka yawan giyan da ya dace ka rika sha.
b Idan ka kasa daidaita yadda kake shan giya, mai yiwuwa za ka bukaci taimakon likita.