Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

YADDA AKE AMFANI DA GUDUMMAWARKA

Yadda Wasu Suka Yi Taron Yanki

Yadda Wasu Suka Yi Taron Yanki

1 GA AGUSTA, 2021

 Taron Yanki na 2020 shi ne taro na farko da aka yi a lokaci daya a dukan duniya kuma an yi hakan ta wurin amfani da Intane! A Malawi da Mozambik, yawancin ꞌyanꞌuwanmu sun yi taron amma ba ta intane ba. Ta yaya hakan ya yiwu?

 Kwamitin Masu Tsara Ayyuka da Kwamitin Koyarwa na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah sun yi abin da ba su saba yi ba, wato sun ba da izini a watsa taron a rediyo da talabijin don ꞌyanꞌuwa a Malawi da Mozambik su saurara. Me ya sa aka ba da izini a yi hakan? Malawi tana daya daga cikin kasashen da Intane ya fi tsada a duniya, saboda haka Shaidun Jehobah kadan ne kawai suke iya shiga Intane. Wani memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah a Malawi mai suna William Chumbi ya ce: “Ta wurin rediyo da talabijin ne kadai ꞌyanꞌuwa za su iya sauraron taron yankin.” Luka Sibeko wanda shi ma memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah a Malawi ya ce: “Da a ce ba mu iya mun saurara ta wajen talabijin da rediyo ba, da ꞌyanꞌuwa kadan ne kawai za su amfana daga taron.” A Mozambik ma, ꞌyanꞌuwa kalilan ne kawai suke da wayoyi da za su iya shiga intane, balle ma a ce su iya saukar da abubuwa daga intane.

Shirye-shiryen da Aka Yi

 Annobar korona ta sa an soma watsa taron ikilisiya a tashar rediyo da talabijin. a ꞌYanꞌuwanmu sun yi magana da tashoshin rediyo da talabijin don su nemi karin lokaci da za su watsa taron.

 A Malawi, ꞌyanꞌuwanmu sun fuskanci wani kalubale. Gidajen rediyo da talabijin ba sa ba kwastomominsu fiye da awa daya a lokaci guda na watsa shirinsu. Suna ganin cewa mutane za su gaji da saurarar abu guda har tsawon awa daya. Amma ꞌyanꞌuwanmu sun bayyana musu cewa aikin da muke yi yana taimaka wa jamaꞌa. Ko a lokacin annobar da ba a fita daga gida, muna yi wa mutane waꞌazi daga Littafi Mai Tsarki da zai taimaka musu su zama mutanen kirki, kuma su rika farin ciki a iyalinsu. Da suka ji hakan, sai gidajen rediyo da talabijin sun yarda su ba ꞌyanꞌuwan karin lokacin da suke bukata.

 A Malawi, an watsa taron yankin a tashar talabijin daya da tashar rediyo daya, kuma miliyoyin mutane a fadin kasar ne suke iya kama tashoshin biyu. A Mozambik kuma, an watsa taron a tashar talabijin daya da tashoshin rediyo guda 85.

 A kasashen biyun, an kashe dala 28,227 b wajen watsa taron a tashoshin talabijin da kuma kusan dala 20,000 wajen watsawa a tashoshin rediyo. Kudin sayan lokacin watsa shirin a karamar tashar rediyo ya bambanta daga dala 15 zuwa dala 2,777 don watsa shirin a babbar tasha.

 ꞌYanꞌuwanmu sun yi amfani da gudummawa da aka bayar yadda ya kamata. A Malawi, ꞌyanꞌuwanmu sun nemi sauki har sai da suka sami ragi. Akwai lokacin da aka rage musu kashi 30 cikin dari na kudin da ya kamata su bayar. Duka ragin da aka yi musu ya kai dala 1,711. A Mozambik, wasu tashoshi sun yi mana ragi domin halin kirki da muke da shi da kuma yadda muke biyansu a kan lokaci.

Yadda ꞌYanꞌuwanmu Suka Yi Godiya

 ꞌYanꞌuwanmu sun yi godiya sosai don yadda suka iya kallo da kuma sauraron taron yankin a tashoshin da ke yankinsu. Wani dattijo mai suna Patrick daga Malawi ya ce: “Mun gode wa Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah don duka abubuwan da suka yi mana a lokacin annobar korona.” Wani danꞌuwa mai suna Isaac wanda shi ma daga Malawi ne ya ce: “Ba mu da wayoyi, shi ya sa muna godiya don yadda kungiyar Jehobah ta shirya mana mu saurari taron yankin ta rediyo. Saboda wannan shirin, dukanmu a iyali mun amfana daga taron. Hakan ya nuna mana cewa Jehobah yana kaunar mutanensa.”

 Taron yanki na 2020 shi ne taron yanki na farko da wani mai shela a Mozambik ya halarta. Ya ce: “Shirin da aka yi mana don mu kalli taron yankin a talabijin ya tuna min cewa Jehobah shi ne Allah mai iko duka. Annobar ba ta hana Jehobah ba mu abubuwa da muke bukata don karfafa dangantakarmu da shi ba, kuma ya ba ni har ma a cikin dakina. Na ga tabbaci cewa mutanen Jehobah suna kaunar juna. Hakan ya nuna min cewa wannan shi ne addini na gaskiya.”

 Wani dattijo mai suna Wyson ya ce: “Ina so in nuna godiyata don yadda bawan nan mai aminci ya kula da mu a lokacin annobar. Yadda aka watsa taron yankin ta rediyo da talabijin ya taimaka ma da yawa cikinmu sosai da yake mu talakawa ne.”

 Kwamitin Masu Tsara Ayyuka da Kwamitin Koyarwa sun sake ba da izini a watsa taron yanki na 2021 a talabijin da rediyo a wasu yankuna. Mun samu kudin watsa wannan taron yanki ne ta wurin gudummawar da kuka bayar ta hanyoyi dabam-dabam da ke donate.dan124.com. Mun gode muku don yadda kuke bayarwa hannu sake.

a A farkon shekara ta 2020, Kwamitin Masu Tsara Ayyuka ya amince a watsa taron ikilisiya a rediyo da kuma talabijin a wasu wurare a lokacin annobar korona. Wannan tanadin ya taimaka ma wadanda suke yankunan da babu Intane kuma ba za su iya yin amfani da wayarsu wajen halartar taro ba don babu sabis ko kuma yana da tsada sosai. Amma ba a yi wannan tanadin ba don yankunan da za su iya halartar taro ta Intane.

b Dukan daloli da aka ambata a wannan talifin na Amirka ce.