WAƘA TA 130
Mu Rika Gafartawa
(Zabura 86:5)
-
1. Ubanmu mai ƙauna
Ya aiko da Yesu fa,
Domin ya yafe zunubi,
Ya cire mutuwa ma.
Idan mun yi tuban gaske,
Zai yafe zunubanmu.
Allah zai gafarta mana
Don fansar Yesu Kristi.
-
2. Allahnmu Jehobah
Zai nuna mana jinƙai
In mun koyi halayensa
Na yafe wa mutane.
Nuna tausayi ga kowa
Da kuma yin haƙuri,
Mu riƙa girmama juna,
Mu ƙaunaci junanmu.
-
3. Ya dace dukanmu
Mu riƙa nuna jinƙai.
Domin kar mu riƙe juna
A cikin zuciyarmu.
In mun yi koyi da Allah
Wanda shi mai ƙauna ne,
Za mu riƙa nuna jinƙai
Kamar Mahaliccinmu.
(Ka kuma duba Mat. 6:12; Afis. 4:32; Kol. 3:13.)