WAƘA TA 69
Mu Ci Gaba da Yin Wa’azi Game da Mulkin Allah!
(2 Timotawus 4:5)
-
1. Mu ci gaba da yin wa’azi
Ga dukan maƙwabtanmu.
Mu nuna musu ƙauna sosai,
Mu sa su san Jehobah.
Muna murnar yaɗa bishara,
Don hakan gata ne babba.
Mu riƙa yin shelar bishara,
Mu girmama sunan Allah.
(AMSHI)
Mu je mu yi wa dukan
Mutane wa’azin Mulkin.
Mu ci gaba da riƙe aminci
ga Maɗaukaki.
-
2. Mu tashi mu je yin bishara,
Bisharar Mulkin Allah.
Mu matasa da tsofaffi ma,
Har da dukan shafaffu.
Dukan mutane na bukatar
Su ji wa’azin Mulkin nan.
Jehobah zai taimaka mana,
Mu yi gaba gaɗi sosai!
(AMSHI)
Mu je mu yi wa dukan
Mutane wa’azin Mulkin.
Mu ci gaba da riƙe aminci
ga Maɗaukaki.
(Ka kuma duba Zab. 23:4; A. M. 4:29, 31.)