Mu Sasanta
Ka Saukar:
1. Na riƙe shi a zuciya
Domin ya min wani laifi.
Jehobah ka taimaka min
In gafarta. Hakan zai fi,
Zai ban sauƙi.
(AMSHI)
Yanzu ba ɓata lokaci.
Zan yi iya ƙoƙarina
In je domin mu sasanta.
Mu sasanta, mu sasanta.
2. Ko da me ya yi zan yafe.
Jehobah na gafartawa.
Ni ma zan yi koyi da shi.
Zan gafarta, zan bar fushi;
Ƙauna ke nan!
(AMSHI)
Yanzu ba ɓata lokaci.
Zan yi iya ƙoƙarina
In je domin mu sasanta.
Mu sasanta, mu sasanta.
3. Aboki, na zo
Mu yi zama kamar na dā.
Kar mu tuna baya.
Ni naka ne, kai nawa ne.
3. Allah yana son dukanmu.
Yana so mu zauna tare.
Yafewa zai sa ni murna,
Shi ya sa zan yafe masa
In bar kome.
(AMSHI)
Yanzu ba ɓata lokaci.
Zan yi iya ƙoƙarina
In je domin mu sasanta.
Mu sasanta, mu sasanta,
Mu sasanta, mu sasanta.
Zan je mu shirya.