Zan Tabbatar ma Kaina
Ka Saukar:
1. ‘Ya zan yi, shin wannan shi ne addini na gaskiya?’
Damuwoyi sun yi yawa, abin yana sa
In ma rikice.
Amma na dau lokaci don in yi bincike.
Ina so in kara bangaskiyata.
Ba zan daina ba!
(AMSHI)
Zan bincika maganarsa,
In san wannan ne gaskiya,
In kara samun tabbaci.
Kuma Allahna yana taimaka min don
In tabbata,
In tabbata,
In tabbata.
2. Ibilis yana so ya hana mutane bin gaskiya.
Ga Jehobah Allahna ni fa zan dogara,
Ba duniyar nan ba.
Shi ya sa nake kauce wa duk karairayi.
Kalmar Jehobah na taimaka min
In daina yin shakka.
(AMSHI)
Zan bincika maganarsa,
In san wannan ne gaskiya,
In kara samun tabbaci.
Kuma Allahna yana taimaka mini
In tabbata,
In tabbata,
In tabbata.
3. Ina samun karfafa ta ꞌyanꞌuwa,
Ko ta nassosi, ko a wakokinmu.
Jehobah na amsa adduꞌoꞌina,
Ba na shakka!
(AMSHI)
Zan bincika maganarsa,
In san wannan ne gaskiya,
In kara samun tabbaci.
Jehobah Allahna yana taimaka mini
In tabbata,
In tabbata,
In tabbata,
In tabbata,
In tabbata,
In tabbata.