“Anini Biyu”
Ka Saukar:
1. Zuciyata
Tana ta bugawa.
Kudina
Ba shi da yawa kamar na sauran.
Ya Allahna,
Aninai biyu ne nan.
Na san za ka karba,
Ko da yake ba shi da yawa.
(AMSHI)
Ko da kadan ne
Jehobah yana so,
Domin Ya san kokarinmu.
Na san hakan domin
Yana son mu sosai.
Zai karbi gudummawata,
Ba shakka!
2. A zucinta
Kila ta manta cewa
Takan bayar da
Fiye da hakan idan ta samu.
Da ta saka su
Ba wanda ya ji karar.
Amma ga Allahnmu,
Wannan kyautar babban abu ne.
(AMSHI)
Ko da kadan ne
Jehobah yana so,
Domin Ya san kokarinmu.
Na san hakan domin
Yana son mu sosai.
Zai karbi gudummawata,
Ba shakka!
3. Yana daraja duk kokarinmu,
Ko da ba shi da yawa, Ya sani.
Ya san zuciyarmu.
(AMSHI)
Ko da kadan ne
Jehobah yana so,
Domin Ya san kokarinmu.
Na san hakan domin
Yana son mu sosai.
Zai karbi gudummawata,
Ba shakka!
Don Jehobah ya san kome.