Bangaskiya Za Ta Sa Mu Cim ma Kome
Ka saukar da:
1. Ina son amsoshin, tambayoyina,
Na gamsu da amsar; da kin ba ni.
Wa’azinki, ya yi daɗi.
Tambayoyina kun amsa duka.
Na gamsu sosai, ina murna.
Zuciyata, ta kwanta fa.
(AMSHI)
Hanyar rai ba ta da sauƙi,
Bangaskiya na da kyau.
In muna cikin matsaloli,
Bangaskiya na da kyau,
Tana da kyau.
2. Ina son wa’azin, ina shelarsa.
Na gama yin shiri, za mu fita.
Za mu fita
Yin wa’azi.
Bangaskiyata tana ci kamar wuta.
Ba zan bar wutar nan ta yi sanyi.
Ta yi sanyi a zuciyata.
(AMSHI)
Hanyar rai ba ta da sauƙi,
Amma ba zan manta ba:
In muna cikin matsaloli,
Bangaskiya na da kyau,
Tana da kyau.
(KAFIN AMSHI)
Matsaloli, ƙunci, na sa ɓacin rai.
Yin addu’a a kullum, da kusantar Jehobah.
Ya ce, “In ka dogara da ni,
Zan ƙarfafa ka ba shakka
Domin ka yi maganin,
Matsalolinka.”
(AMSHI)
Hanyar rai ba ta da sauƙi,
Amma ban zan manta ba:
In muna cikin matsaloli,
Bangaskiya na da kyau
(AMSHI)
Na tabbata, ba na shakka,
Bangaskiya na da kyau.
In muna cikin matsaloli,
Bangaskiya na da kyau.
Tana da kyau.