Mu Iyali Ne
Ka Saukar:
1. Mun isa inda za mu je
Mun yi tafiya mai nisa.
Mun bar gidanmu,
Amma Jehobah
Ya biya bukatarmu.
Muna yin ayyuka sosai domin,
Mu daukaka Jehobah.
Kuma muna kaunar ’yan’uwanmu sosai,
Shi ya sa muka ce:
(AMSHI)
Mu bayin Jehobah ne;
Dukanmu, mu iyali ne.
Duk da bambancin Kasarmu,
Dukanmu.
Mu iyali ne.
2. Sa’ad da muka iso nan,
Kun fito kun marabce mu.
Mun soma taron da rera waka,
Kaunarmu ta yi karfi.
Kuma da taimakon Jehobah ne
Kome ya tafi daidai.
Dukanmu za mu yabe shi da bauta masa
Tare har abada.
(AMSHI)
Mu bayin Jehobah ne;
Dukanmu, mu iyali ne.
Duk da bambancin kasarmu,
Dukanmu.
Mu iyali ne.
3. Mun kai wa’azin bishara
A wata kasa mai nisa.
Kuma mutanen, da muka samu
Suna da kirki sosai.
Da kuma kauna ta ’yan’uwanmu
Na sa mu farin ciki.
Ko’ina muka je a duk inda muke,
Muna son junanmu!
(KAFIN AMSHI)
Sanin cewa
Muna da ’yan’uwa a duk duniya,
A Mali da Meziko,
Har Jafan da Jamaika.
(AMSHI)
Mu bayin Jehobah ne;
Dukanmu, mu iyali ne.
Duk da bambancin kasarmu,
Dukanmu.
Mu iyali ne.
Daga dukan al’umma—
Dukanmu, mu iyali ne.
Muna kaunar juna sosai
Domin mu Shaidun Jehobah ne!
Cadi, Malawi, da ma Italiya;
Kamaru, Gana, da Uganda;
Najeriya, Kazakhstan, da Estoniya—
Dukanmu, mu iyali ne.