Soyayya Ruwan Zuma
Ka Saukar:
1. Allah ya ba mu wata kyauta,
Kyautar nan soyayya fa.
Idan aka soma son juna,
Akan yi farin ciki sosai.
(AMSHI)
Soyayya da sauki da kuma dadi.
In mun yi nufin,
Jehobah.
In mun bi ja-gorancin Jehobah Allah,
Soyayyarmu ruwan zuma ce
Ke ce nake so,
Ke nake so.
2. Komin damuwa,
Ba za mu daina son juna ba.
Babu wanda zai iya raba mu.
Don soyayyarmu ruwan zuma ce.
Ba mai raba mu.
(AMSHI)
Soyayya da sauki da kuma dadi.
In mun yi nufin,
Jehobah.
In mun bi ja-gorancin Jehobah Allah,
Soyayyarmu ruwan zuma ce
Ke ce nake so,
Ke nake so.
(KAFIN AMSHI)
Ba mai iya raba mu.
Soyayyarmu kyauta ce daga Allah.
‘Ikon kauna kamar na mutuwa ce.’
Ke ce rabin raina; da kuma “namana,”
Ke mace ce mai kirki abin ƙaunata.
Ba zan daina kaunar ki ba sam.
3. Ina son ki san da hakan
Soyayyarmu fa ruwan zuma ce.
Ina murnar rayuwarmu tare.
Ba na da-na-sanin aurenmu.
Ba shakka.
(AMSHI)
Soyayya da sauki da kuma dadi.
In mun yi nufin,
Jehobah.
In mun bi ja-gorancin Jehobah Allah,
Soyayyarmu ruwan zuma ce
Ke ce nake so,
Ke nake so.
Soyayyarmu ruwan zuma ce
Ke ce nake so.