Zan Canja Hanyoyin Wa’azina
Ka Saukar:
1. Ina ta tunanin
Yadda nake
Bauta wa Jehobah
Da kuma yin wa’azi,
Iri ɗaya ne a kowace rana.
Shi ya sa nake so in canja
Salon hidimata.
(AMSHI)
Za ni canja hanyoyin wa’azina.
A yanzu zan soma sabon salo.
Jehobah, na san abin da zan yi.
Zan dogara da kai, domin taimako.
2. Yin canji ba sauƙi,
Amma na ga
Yadda hakan ke sa
Ni farin ciki sosai.
Na soma bin sabon, salon wa’azi.
Da akwai hanyoyi da yawa,
Da ban lura da su ba.
(AMSHI)
Za ni canja hanyoyin wa’azina.
A yanzu zan soma sabon salo.
Jehobah, na san abin da zan yi.
Zan dogara da kai, domin taimako.
(NA UKU)
A dā, na zata ba zan
Iya hidimar nan ba.
Na zata hidimar na,
Da wuya sosai.
Yanzu na ga albarkar
Da yin hakan ya kawo.
Kuma na sani za su
ƙaru a nan gaba.
(AMSHI)
Za ni canja hanyoyin wa’azina.
A yanzu zan soma sabon salo.
Jehobah, na ga abin da zan yi,
Kai ka yi min albarka, don amincina.
(AMSHI)
Za ni canja hanyoyin wa’azina.
A yanzu zan soma sabon salo.
Jehobah, na san abin da zan yi.
Zan dogara da kai.
(AMSHI)
Za ni canja hanyoyin wa’azina.
A yanzu zan soma sabon salo.
Jehobah, na san abin da zan yi.
Zan dogara da kai, domin taimako.
Taimake ni.