Yin Wa’azin Bishara a Yarukan Kasar Ireland da Biritaniya
Shaidun Jehobah suna yin kokari musamman don su yada bishara ga mutanen da ke yin yarukan Ireland da kuma Biritaniya. * Ban da Turanci, yarukan da ake yi a wadannan kasashen su ne: Irish da Scottish Gaelic da kuma Welsh.
A watan Satumba ta 2012, mun kaddamar da dandalinmu na jw.org da aka yi masa gyaran fuska kuma ya kunshi yaruka da yawa har da Irish da kuma Welsh. A watan Agusta, 2014, an kara yaren Scottish Gaelic a dandalin. Kari ga haka, muna buga littattafai da yawa da ke bayyana Littafi Mai Tsarki a wadannan yaruka. Mene ne sakamakon haka?
Shaidun Jehobah sun ba ma wani malamin addini wata ’yar warka a yaren Scottish Gaelic. Mutumin ya karanta warkar a take, sai ya fashe da kuka. Me ya sa shi kuka? Ya ji dadin fassarar warkar kuma ya ce: “Wane ne ya fassara wannan warkar? Kai, fassarar tana da dadi sosai!”
A cikin wata daya da aka kaddamar da dandalin jw.org a yaren Scottish Gaelic, kimanin mutane 750 ne suka shiga dandalin.
Wani malamin jami’ar National University of Ireland, a birnin Galway ya gaya ma wani Mashaidi cewa ba ya sha’awar addini ko kadan. Amma, sa’ad da ya ji cewa dan’uwan yana da wata kasida mai jigo Littafi Mai Tsarki—Wane Sako Ne Ke Cikinsa? a yaren Irish, sai ya ce a ba shi. A ra’ayinsa, zai yi kyau kowa ya sami littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki a yarensa, kuma ya yaba wa Shaidun Jehobah don yadda suke fassara littattafai a yaren Irish.
Wata tsohuwa ta nuna godiyarta bayan da aka ba ta wata kasidar da aka fassara zuwa yaren Welsh, kuma ta ce: “A kashin gaskiya, da kasidar nan da Turanci aka buga, da ban karba ba, amma na yi murna cewa da yarenmu aka buga.”
A watan Agusta ta 2014, an kara yawan littattafai da ake wallafawa a yaren Welsh a dandalinmu na jw.org. Domin wannan, yawan mutane da suka shiga dandalinmu ya ninka na dā fiye da sau biyu.
“Yare Daya Muke Yi”
Almajiran Yesu sun yi farin ciki sosai bayan da Yesu ya yi musu bayani daga cikin Nassosi, kuma suka ce wa juna: ‘Zuciyarmu ba ta yi kuna daga cikinmu ba, sa’ad da yake yi mana zance a kan hanya, yana bayyana mana littattafai?’ (Luka 24:32) Idan muka bayyana wa mutane gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki a yarensu, hakan zai iya ratsa zuciyarsu sosai.
Wani mutum mai suna Emyr a kasar Wales ya auri wata Mashaidiyar Jehobah amma ba ya yin ayyukan ibada tare da ita, ko kadan. A kwana a tashi, sai shi da wani Mashaidi mai suna Russell suka fara abokantaka. Daga baya Emyr ya canja ra’ayinsa kuma ya bayyana dalilin hakan da cewa: “Na yanke shawara zan rika nazarin Littafi Mai Tsarki a lokacin da Russell ya kawo mini littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? * Da ya ba ni littafin sai ya ce, ‘Wannan littafin da yaren Welsh aka buga, kuma za mu fara yin nazarinsa tare da kai yanzu.’” Me ya sa Emyr ya ji dadin yadda Russell ya bi da shi? Ya ce: “Ni da Russell yarenmu da al’adunmu daya ne saboda haka muna fahimtar juna sosai.” Zuciyar Emyr ta yi “kuna” yayin da ake koya masa Littafi Mai Tsarki a yarensa na Welsh domin ya fahimci bayanin da aka yi masa sosai.
Shaidun Jehobah za su ci gaba da koya wa mutane gaskiya game da Allah a yarensu domin hakan yana ratsa zukatan mutane sosai.
^ sakin layi na 2 Biritaniya da ake nufi a nan ta kunshi Ingila da Scotland da kuma Wales.
^ sakin layi na 11 Littafin da Shaidun Jehobah suka wallafa don nazarin Littafi Mai Tsarki.