Me Ake Yi a Bikin Daurin Auren Shaidun Jehobah?
A yawancin bikin auren Shaidun Jehobah, akan yi gajeren jawabi daga Littafi Mai Tsarki. Bayan haka, ana iya yin liyafa ko kuma a raba abinci. a Ba da jimawa ba bayan Yesu ya soma hidimarsa a duniya, ya je irin wannan bikin a birnin Kana.—Yohanna 2:1-11.
Yaya ake daura auren?
Jawabin da ake yi a wurin daurin aure yana da muhimmanci sosai a bikin auren. Wajen minti 30 ake yin jawabin, kuma wani dattijo da Mashaidin Jehobah ne yake yinsa. Wannan jawabi mai ban karfafa yakan bayyana yadda Littafi Mai Tsarki zai taimaka wa ma’auratan su ci gaba kaunar juna, su zauna lafiya kuma aurensu ya kasance na dindindin.—Afisawa 5:33.
A kasashe da yawa, gwamnati ta ba wa dattawan Shaidun Jehobah ikon daura aure. A wannan yanayin, ma’auratan za su dauki alkawarin aure a karshen jawabin. Kuma za su iya ba wa juna zobe. Bayan haka, sai wanda ya daura auren ya sanar cewa sun zama mata da miji.
A wasu kasashe kuma ana kafa doka cewa wani wakilin gwamnati ne kadai zai iya daura aure. A irin wuraren nan, wadanda suke so su yi aure sukan je a daura musu auren kafin su zo a yi musu jawabi. Idan ba su dauki alkawarin aure a gaban wakilin gwamnatin ba, za su iya yin hakan a karshen jawabin. Idan kuma sun riga sun dauki alkawari a inda aka daura auren, za su iya maimaita shi kuma su nuna cewa sun riga sun dauki alkwarin a amsarsu. Akan kammala jawabin da addu’a don a roki Allah ya albarkaci auren.
A ina ake daura auren shaidun Jehobah?
Shaidun Jehobah da dama sukan yi bikin daura aurensu a Majami’ar Mulki, wato inda Shaidun Jehobah suke yin taro, idan ba abin da aka shirya za a yi a wurin. b Idan ma’auratan suna so a yi liyafa bayan auren, za su zabi wani wuri dabam don hakan.
Wa zai iya zuwa wurin auren?
Idan a Majami’ar Mulki za a daura auren, kowa zai iya zuwa, da Shaidun Jehobah da wadanda ba Shaidun Jehobah ba. Idan kuma za a yi liyafa bayan daurin auren, ma’auratan ne za su zabi wadanda za su je wurin.
Wane irin kaya ya kamata mutum ya saka zuwa wurin?
Ko da yake ba a gaya wa mutane irin kayan da za su saka su zo aure a Majami’ar Mulkinmu, Shaidun Jehobah sukan saka kayan da ya dace bisa ga ka’idar Littafi Mai Tsarki. Kuma za su ji dadi idan wadanda ba Shaidu ba ma suka yi hakan. (1 Timoti 2:9) A wurin liyafar ma, ya kamata kowa ya saka kayan da ya dace.
Ana ba da kyaututtuka?
Littafi Mai Tsarki ya ce mu rika bayarwa hannu sake. (Zabura 37:21) Don haka, Shaidun Jehobah suna jin dadin ba da kyauta da kuma karban kyauta a wurin aure. (Luka 6:38) Amma Shaidun Jehobah ba sa rokon mutane su ba su kyauta kuma ba sa sanar da sunayen mutane da suka ba su kyautai. (Matiyu 6:3, 4; 2 Korintiyawa 9:7; 1 Bitrus 3:8) Hakan ya saba wa ka’idar Littafi Mai Tsarki kuma zai iya sa wadanda suka zo bikin su ji wani iri.
Ana yin toast ko hada kofi da kofi a wurin?
A’a. Shaidun Jehobah ba sa yin toast, wato mutum ya daga kofi kuma ya hada shi da na wasu, domin hakan ya samo asali ne daga wadanda ba sa bauta wa Allah. c Shaidun Jehobah suna yi wa ma’auratan fatan alheri amma ba sa yin hakan ta wurin hada kofi da kofi.
Ana watsa abubuwa masu kyalli wato confetti a wurin?
A’a. A wasu wurare, a kan watsa wa ma’auratan abubuwa masu kyalli ko shinkafa ko makamantansu. Sun yi imani cewa hakan zai sa ma’auratan su yi sa’a a aurensu, kuma wai hakan zai iya sa su yi farin ciki ko su yi tsawon rai. Amma Shaidun Jehobah ba sa yin duk wani abin da ke da alaka da camfi. Wannan ya hada da rokon allahn sa’a kuma Littafi Mai Tsarki ya haramta yin hakan.—Ishaya 65:11, New World Translation.
Ana ci da sha a wurin?
Ba a ci da sha a cikin Majami’ar Mulki a lokacin daurin aure. Wasu ma’aurata sukan shirya liyafa bayan daurin auren inda za a ci a sha. (Mai-Wa’azi 9:7) Idan za su ba da giya, ba za su ba da shi yadda mutane za su sha har su bugu ba. Ban da haka, wadanda shekarunsu suka kai na shan giya bisa ga dokar kasar ne kadai za a ba su.—Luka 21:34; Romawa 13:1, 13.
Za a saka kida ko a yi rawa a wurin?
Idan ma’auratan sun shirya liyafa, za a iya sa kida kuma a yi rawa. (Mai-Wa’azi 3:4) Wakoki da suke so ko irin wakokin da ake sakawa a ala’darsu ne za su zaba, amma za su zabi wakoki masu dadi da za su amfani wadanda suka zo bikin. A kan yi wakoki da aka dauko daga Littafi Mai Tsarki sa’ad da ake daura aure a Majami’ar Mulki.
Shaidun Jehobah suna yin bikin zagayowar ranar aure kuwa?
Da yake Littafi Mai Tsarki bai goyi bayan ko a yi ko kar a yi bikin zagayowar ranar aure ba, Shaidun Jehobah da suka yi aure ne za su zaba da kansu ko za su yi wannan bikin ko a’a. Idan suna so su yi bikin zagayowar ranar aurensu, za su iya yinsa su kadai, ko su yi tare da ’yan’uwa da abokan arziki.
a Wasu al’adu da dokoki game da yadda za a yi aure za su iya bambanta bisa ga inda za a yi auren.
b Ba a biyan wanda yake ba da jawabin auren, kuma ba a biya don a yi amfani da Majami’ar Mulkin.
c Don karin bayani a kan asalin al’adar kara kofi da kofi, ka duba littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Kaunar Allah,” shafi na 154, sakin layi na 19 da 20, da kuma “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” da ke Hasumiyar Tsaro na 15 ga Fabrairu, 2007 a Turanci.