Mene ne Ra’ayin Shaidun Jehobah Game da Zuwa Makaranta?
Ra’ayinmu game da Zuwa makaranta ya jitu da abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar. Kowane Mashaidi yana yin amfani da lamirinsa don ya bi ka’idodin Littafi Mai Tsarki, kamar wadanda aka ambata a kasa. a
Samun ilimi yana da muhimmanci sosai
Zuwa makaranta yana taimaka wa mutum ya yi “hikima da hankali,” kuma wannan halaye ne da Littafi Mai Tsarki ya yaba wa. (Karin Magana 2:10, 11; 3:21, 22) Kari ga haka, Yesu ya gaya wa mabiyansa su rika koyar da abubuwan da ya koya musu. (Matiyu 28:19, 20) Don haka, muna karfafa membobinmu su je makaranta su koyi karatu da rubutu da yin cudanya da mutane b da samun ilimi game da wasu addinai da kuma al’adu.—1 Korintiyawa 9:20-22; 1 Timoti 4:13.
Gwamnati ma ta san cewa zuwa makaranta yana da muhimmanci, don haka ta bukaci mutane su je makarantar firamare da kuma sakandare. Muna bin wannan dokar domin umurnin da Allah ya ba da ke nan cewa: “Kowa ya yi biyayya ga shugabannin gwamnati, gama babu wani ikon shugabanci,” ko kuma gwamnati. (Romawa 13:1) Kari ga haka, muna karfafa yaranmu su saka kwazo sosai a makaranta. c Kalmar Allah ta ce: “Duk abin da kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku kamar ga Ubangiji ne kuke yi wa, ba ga mutum ba.”—Kolosiyawa 3:23.
Samun ilimi yana taimaka mana mu yi wa iyalinmu tanadi.
Allah ya ce, “duk wanda ba ya kula da danginsa, musamman iyalin gidansa, ya yi mūsun bangaskiyarsa ke nan, ya kuma fi wanda yake marar ba da gaskiya muni.” (1 Timoti 5:8) Samun ilimi yana iya taimaka mana mu cika hakkin yi wa iyalinmu tanadi. Littafin nan The World Book Encyclopedia ya ce, abin da ya sa samun ilimi yake da muhimmanci shi ne domin “yana sa mutane su zama da amfani a yankinsu . . . a matsayin ma’aikata, kuma hakan yana taimaka wa tattalin arzikin kasa.” Mutumin da ke da ilimi kuma yake da aikin yi yana iya yi wa iyalinsa tanadi a kai a kai fiye da mutumin da bai da ilimi.—Karin Magana 22:29.
Ƙari ga haka, iyaye suna yi wa yaransu tanadi ta wajen shirya su don rayuwar da za su yi idan sun girma. Saka yaran a makaranta yana taimaka musu su yi hakan. (2 Korintiyawa 12:14) Muna karfafa iyaye su rika saka yaransu a makaranta. Suna bukatar su yi hakan ko da yin hakan ba kyauta ba ne ko yana da wuya ko kuma ba al’adarsu ba ce. d Ban da haka, muna ba iyaye shawarwarin da za su taimaka musu su tallafa wa yaransu su sami ilimi. e
Mutum ne zai tsai da shawarar makarantar da zai je
Muna mai da hankali sosai wajen zaban makarantar da za mu je. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Marar tunani yakan gaskata kome, amma mai hankali yakan yi tunani kafin ya fara wani abu.” (Karin Magana 14:15) Muna bin wannan shawarar ta wajen yin bincike don mu san irin makarantu da suka dace mu je da kuma kudi da lokaci da muke bukatar yin amfani da su don zuwa makarantar. Alal misali, a yawancin lokaci makarantu da suke koya wa mutane aikin hannu ba sa cin lokaci sosai.
Samun ilimi game da Allah shi ne ya fi muhimmanci. Samun ilimin Littafi Mai Tsarki zai sa mu san Allah kuma hakan zai sa mu sami rai, amma samun ilimi a makaranta ba ya hakan. (Yohanna 17:3) Kari ga haka, yana sa mu kasance da dabi’a mai kyau mu ‘gane adalci da shari’ar gaskiya, da yadda za mu aikata abin da yake daidai. Kuma mu gane kowace hanya mai kyau.’ (Karin Magana 2:9) Makarantar da manzo Bulus ya je yana nan ne kamar makaranta jami’a a yau. Amma duk da haka, ya ce ‘darajar sanin Almasihu Yesu Ubangijina,’ ita ce ta fi muhimmanci. (Filibiyawa 3:8; Ayyukan Manzanni 22:3) Haka ma yake a yau, Shaidun Jehobah da yawa sun je makaranta, amma sun amince cewa abubuwan da suke koya game da Allah ne ya fi muhimmanci. f
Zuwa jami’a yana iya bata dangantakar mutum da Allah
Littafin Karin Magana ya ce: “Mai hankali yakan ga hatsari, ya kauce, amma marar tunani yakan sa kai, ya sha wahala.” (Karin Magana 22:3) Shaidun Jehobah sun fahimci cewa mahallin wasu jami’a ko kuma wasu makarantu suna iya gurbata dabi’a kuma su sa mutum ya bata dangantakarsa da Allah. Saboda haka, Shaidun Jehobah da yawa sun yanke shawarar kin zuwa jami’a ko kuma saka yaransu. Suna ganin cewa a irin wadannan wuraren ana koyar da abubuwan da ba su dace ba kamar:
Ra’ayin da bai dace ba: Kudi yana sa mutum ya sami kāriya da kuma farin ciki
Ana koyar da ra’ayin nan cewa zuwa Jami’a ne zai sa mutum ya sami aikin da za a rika biyan sa albashi mai soka. Don haka, dalibai da yawa suna zuwa jami’a don mu sami kudi. Wasu suna ganin cewa kudi zai sa su sami kāriya da kuma farin ciki, amma Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa hakan ba gaskiya ba ne. (Mai-Wa’azi 5:10) Mafi muhimmanci ma, Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa “ƙaunar kudi ita ce tushen kowace irin mugunta. A cikin marmarin yin arziki da sauri, wadansu sun rabu da bangaskiyarsu.” (1 Timoti 6:10) Shaidun Jehobah suna kokari sosai don kada su soma “son arziki.”—Matiyu 13:22.
Ra’ayin da bai dace ba: Daraja da kuma sakamako da za ka samu idan ka je jami’a shi ne ya fi muhimmanci
Alal misali, wani mai suna Nika Gilauri da firayim mista ne a kasar Georgia a dā ya rubuta game da ra’ayin da mutanen ke da shi a kasarsa, ya ce: “A kasar Georgia [A dā,] idan kana so a daraja ka dole ne sa kana da digiri. . . . Abin kunya ne ga iyaye a kasar Georgia idan dansu ko ’yarsu ba ta da digiri.” g Akasin haka, Allah ya yi mana gargadi a Littafi Mai Tsarki cewa kada mu nemi yin suna a wannan duniyar. Yesu ya gaya wa shugabannin addini da suke neman yin suna a zamaninsa cewa: “Yaya za ku ba da gaskiya sa’ad da kuke ƙoƙarin samun yabo daga junanku?” (Yohanna 5:44) Makarantar jami’a tana iya sa mutum soma rena wasu, kuma Allah ya tsani hakan.—Karin Magana 6:16, 17; 1 Bitrus 5:5.
Ra’ayin da bai dace ba: Kowane mutum ne zai kafa mizanin abin da ya dace da wanda bai dace ba
Shaidun Jehobah sun amince da mizanan Allah game da abin da ya dace da wanda bai dace ba. (Ishaya 5:20) Amma a wani talifi da aka buga a jaridar Journal of Alcohol and Drug Education an ce matsi daga abokai a jami’a yana sa dalibai da yawa su “tsai da shawarar da sun san bai dace ba.” h Abin da wannan talifin ya ce ya yi daidai da abin da ke Littafi Mai Tsarki cewa: “Zama da mugaye yakan ɓata halayen kirki.” (1 Korintiyawa 15:33) A mahallin jami’a, ana karfafa yin abubuwan da Allah ya haramta, kamar su buguwa da giya da shan kwaya da kuma yin lalata.—1 Korintiyawa 6:9, 10; 2 Korintiyawa 7:1.
Ra’ayin da bai dace ba: Zuwa makarantar Jami’a ita ce hanyar inganta wannan duniya
Mun sani cewa mutane da yawa suna zuwa makaranta ne ba don su yi arziki ba ko a daraja su ko kuma don lalata, amma domin suna so su inganta kansu da kuma duniya. Wadannan makasudai ne masu kyau, amma Shaidun Jehobah suna da makasudai dabam. Kamar Yesu, mun san cewa Mulkin Allah ne kadai zai magance matsalolinmu. (Matiyu 6:9, 10) Amma ba jiran lokacin da Mulkin zai magance matsalolinmu kawai muke yi ba. Kamar Yesu, muna wa’azin “labari mai daɗi na Mulkin” a dukan duniya. Hakan yana taimaka wa dubban mutane su canja salon rayuwarsu. i—Matiyu 24:14.
a Matasa Shaidun Jehobah da ke zama da iyayensu suna bin umurnin iyayensu kuma su je makaranta idan hakan bai sabawa dokokin Allah ba.—Kolosiyawa 3:20.
b Saboda haka, mun wallafa littattafai kamar Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa da za su taimaka wa mutane su sami ilimi. Mun wallafa irin wadannan littattafai fiye da kofi miliyan 11. Kari ga haka, muna gudanar da ajin koyar da wadanda ba su iya karatu ba a yaruka 120. A tsakanin shekara ta 2003 da 2017, mun koya wa mutane wajen 70,000 karatu da kuma rubutu.
c Ka duba talifin nan “Kamar Na Daina Makaranta.”
d Alal misali, muna karfafa iyaye su saka yaransu maza da mata a makaranta. Ka duba talifin nan “Should My Child Go to School?” a Hasumiyar Tsaro na 15 ga Maris, 2003 a Turanci.
e Ka duba talifin nan “Yadda Za Ka Taimaka wa Danka Ya Rika Samun Maki Mai Kyau a Makaranta.”
f Ka duba sashen “Ra’ayoyi Game da Yadda Rayuwa ta Soma” a dandalin jw.org.
g Practical Economics: Economic Transformation and Government Reform in Georgia 2004—2012, page 170.
h Volume 61, No. 1, April 2017, page 72.
i Don ka ga yadda Littafi Mai Tsarki da kuma wa’azin Mulkin Allah suke da iko, ka duba sashen “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” a dandalin jw.org.