Mene ne Ra’ayin Shaidun Jehobah Game da Kashe Aure?
Muna iya kokarinmu mu ga cewa mun bi tsarin da ke Littafi Mai Tsarki game da zaman aure da kuma kashe aure. Asalin nufin Allah shi ne ma’aurata su zauna tare har abada. Littafi Mai Tsarki ya ce zina ce kadai dalilin da zai iya sa ma’aurata su kashe aurensu.—Matta 19:5, 6, 9.
Shin, Shaidun Jehobah za su iya taimaka wa ma’auratan da suke da matsala a aurensu?
E, ga wasu daga cikin taimakon nan:
Littattafai. Akwai littattafanmu da suke dauke da shawarwarin da za su iya taimaka wa ma’aurata su yi gyare-gyare a aurensu. Wasu talifofin su ne, “Ku Manne wa Wa’adin da Kuka Ɗauka a Aurenku,” da kuma “Yadda Za A Sake Amincewa da Juna.”
Taro. A wajen taronmu na ikilisiya ko na da’ira ko kuma na yanki, akan tattauna shawarwarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki game da yadda ma’aurata za su yi zaman lafiya.
Dattawa. Wadannan mazaje suna taimaka wa ma’aurata su bi ka’idodin Littafi Mai Tsarki, kamar wadanda aka rubuta a Afisawa 5:22-25.
Shin, dattawa a cikin ikilisiya ne suke ba wa ma’aurata izini su kashe aurensu?
A’a. Ko da yake ma’aurata za su iya zuwa neman shawara a wurin dattawa idan suna fuskantar matsala a aurensu, dattawa ba su da izinin gaya musu abin da za su yi. (Galatiyawa 6:5) Amma, duk wanda ya kashe aurensa ba bisa ka’idar Littafi Mai Tsarki ba, bai cancanci a ba shi wani matsayi a cikin ikilisiya ba kuma ba shi da izini ya sake aure.—1 Timotawus 3:1, 5, 12.
Mene ne ra’ayin Shaidun Jehobah game da rabuwar ma’aurata?
Littafi Mai Tsarki ya ce kada mata da miji su rabu da juna ko da suna da matsaloli sosai a aurensu. (1 Korintiyawa 7:10-16) Idan ma’aurata suna bin abin da Littafi Mai Tsarki ya fada, suna addu’a tare kuma suna kaunar juna sosai, za su iya warware yawancin matsalolin da za su taso a tsakaninsu.—1 Korintiyawa 13:4-8; Galatiyawa 5:22.
Amma a wasu lokuta, ma’aurata Kiristoci suna iya yanke shawarar rabuwa da juna idan suka ga cewa ci gaba da zama zai jefa rayuwarsu cikin hadari. Wasu dalilan da za su iya sa su rabu su ne:
Idan mijin ya ki biyan bukatun iyalinsa da gangan.—1 Timotawus 5:8.
Dūkan da zai iya ji wa mutum rauni sosai.—Zabura 11:5.
Hana mutum bauta wa Jehobah. Alal misali, idan mata ko miji yana tilasta wa matarsa da Mashaidiya ce ta taka dokar Allah, matar za ta iya zaban ta rabu da shi don ta samu ta yi “biyayya ga Allah [fiye] da mutane.”—Ayyukan Manzanni 5:29.