LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE
“Ina Kwana A Titi”
Shekarar Haihuwa: 1955
Kasar Haihuwa: Sifen
Tarihi: Shaye-shaye da Fada
RAYUWATA A DĀ
Yana daukan lokaci sosai kafin wasu su koyi darasi daga rayuwa marar kyau da suka yi. Abin da ya faru da ni ke nan. An haife ni a birnin Barcelona kuma shi ne birni na biyu da ya fi girma a kasar Sifen. Iyalinmu suna zama a yankin da ake kira Somorrostro, kuma wurin yana kusa da kogi. Ban da haka ma, a wurin ne yawancin mutanen birnin suke zama. Birnin Somorrostro ya yi suna a harkar kwayoyi da kuma aikata laifuffuka.
Mu yara tara ne a iyalinmu kuma ni ne dan fari. Da yake mu talakawa ne sosai, sai mahaifina ya tura ni yin aiki a kungiyar kwallon tenis. Shekara na goma a lokacin kuma ina aiki na awa goma a kowace rana. Don haka, ban yi makaranta kamar yadda wasu yara suka yi ba. Da na kai shekara 14, sai na soma aikin makaniki.
A 1975 ne aka tilasta mini in shiga soja a kasar Sifen, a lokacin ana tilasta wa mutane su yi hakan a wurin. Na so in yi wasu abubuwan a zo a gani, sai na soma aiki na dan lokaci a rukunin sojojin kasar Sifen da ke Melilla a arewacin Afirka. A lokacin na soma shaye-shaye sosai.
Da na bar wannan aikin, sai na koma Barcelona kuma muka kafa rukunin ta da zaune tsaye. Muna sace-sace da wasu ayyukan da ba su dace ba. Mukan sayar da kayan da muka sata don mu sami kudin sayan kwayoyin da muke sha. Har na soma shan kwayoyi kamar su aji-garau da kuma wani da ake kira LSD. Ban da haka ma, na soma zina da yin maye da kuma caca. Wannan salon rayuwar ya sa na zama mai zafin rai da mai son fada. Ina yawo da wuka da adda ko kuma gatari kuma ina ji wa mutane rauni da shi idan rigima ta taso.
Akwai wani lokacin da muka saci wata mota kuma ‘yan sanda suka kama bin mu. Abin kamar wani wasan kwaikwayo ne. Mun yi gudu da motar har kilomita 30, sai ‘yan sandan suka fara harbinmu da bindiga. A karshe, sai direbanmu ya bugi wani abu kuma dukanmu muka fita daga motar muka gudu. Da mahaifina ya ji labarin abin da ya faru, sai ya kore ni daga gidansa.
Na yi shekara biyar ina kwana a kan titi. Nakan kwana a kofar gidajen mutane ko a cikin manyan motoci ko a kan bencuna da ke tasha ko kuma a makabarta. Akwai lokacin da na yi rayuwa a kogo. Rayuwata ba ta tabarbare, don haka, ina abubuwan da na ga dama don ban damu da rayuwata ba, ko in mutu ko in rayu. Idan na bugu, sai in rika jima hannayena rauni kuma har yanzu ina da tabbunan a jikina.
YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA
Da na kai shekara 28, sai mahaifiyata ta same ni ta ce in koma gida. Na amince da hakan kuma na yi mata alkawari cewa zan gyara salon rayuwata, amma cika wannan alkawarin ya dauke ni lokaci sosai.
Wata rana da tsakar rana, sai wasu Shaidun Jehobah guda biyu suka zo yin wa’azi a gidanmu. Da nake sauraron su, sai mahaifina ya leko daga ciki kuma ya tsauta min ya ce in rufe kofar. Da yake ni ba mai jin magana ba ne, sai na yi banza da shi. Sun ba ni wasu littattafai kanana guda uku, sai na karba. Na tambaye su wurin da majami’arsu take kuma bayan wasu kwanaki, sai na je Majami’ar Mulkin.
Abin da na fara lura shi ne kowa a wurin ya yi ado mai kyau. Amma ni ba haka nake ba, ina da dogon suma da gemu kuma adon da na yi ba kai. Na ga cewa ban dace da wurin ba, sai na tsaya a waje. Amma abin mamaki shi ne na ga Juan wanda a dā muke ta da zaune tsaye tare da shi kuma ya saka kwat. Daga baya na gane cewa ya yi shekara daya da zama Mashaidin Jehobah. Ganinsa ya ba ni karfin halin shiga majami’ar don in ji abin da za a fada. Haka na soma canja salon rayuwata.
Sai na amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni kuma na gane cewa idan ina son Allah ya kaunace ni, wajibi ne in canja salon rayuwata kamar yawan fushi da zina. Daina wadannan halayen ba su kasance min da sauki ba. Kuma na gane cewa idan ina son in faranta wa Jehobah rai, dole in ‘sabunta hankalina ɗungum.’ (Romawa 12:2, Littafi Mai Tsarki) Jin kan Allah ya sa ni yin tunani sosai. Duk da kurakurai da nake yi, na san cewa yana ba ni lokaci don in iya canja salon rayuwata. Abin da na koya game da Jehobah ya shafi rayuwata sosai. Kuma hakan ya sa na fahimta cewa akwai Mahalicci da yake kula da mu.—1 Bitrus 5:6, 7.
Sai na soma daina wasu halayen banza da nake yi. Alal misali, sa’ad da na koya a Littafi Mai Tsarki cewa shan taba ba shi da kyau, sai na ce, ‘Idan Jehobah yana son in kasance da tsabta, wajibi ne in daina shan taba.’ (2 Korintiyawa 7:1) Sai na zubar da shi cikin kwandon shara!
Na so in daina sha da kuma sayar da kwaya. Hakan bai zo min da sauki ba sam, sai da ya dauke ni lokaci. Na san cewa idan ina son in daina hakan, wajibi ne in bar abokantaka da wadanda suke yin hakan. Halinsu ba ya taimaka min in cim ma burina na daina halayen banza. Amma a karshe, na dogara ga Jehobah sosai da kuma sabbin abokaina na ikilisiya. Yadda suka kaunace ni kuma suka nuna cewa sun damu da ni ya sa ni farin ciki don ban taba ganin haka ba. Bayan wasu watanni, na daina shan kwayoyi da kuma sayar da shi kuma na “ɗauki sabon halin,” da zai sa Allah ya kaunace ni. (Afisawa 4:24, LMT) A watan Agusta na 1985 ne na yi baftisma kuma na zama Mashaidin Jehobah.
YADDA NA AMFANA
Littafi Mai Tsarki ya kyautata rayuwata. Ya taimaka min in daina salon rayuwa da nake yi kuma in kāre mutuncina. A gaskiya, abokaina fiye da 30 sun mutu tun suna matasa sanadiyyar cutar kanjamau da wasu cututtuka da ake samu daga shan kwayoyi. Ina godiya cewa bin ka’idodin Littafi Mai Tsarki ya taimaka mini in guji wasu mummunan sakamako.
Na daina rike wukake da adda da kuma gatari kamar yadda nake yi sa’ad da nake matashi. Ban san cewa wata rana zan fita ina koya wa mutane Littafi Mai Tsarki ba. A yanzu, ni da matata Shaidun Jehobah ne da suke hidima ta cikakken lokaci.
Iyayena ba su zama Shaidun Jehobah ba, amma duk da haka, sun yi farin ciki cewa na amfana sosai daga abin da na koya a Littafi Mai Tsarki. Akwai wata rana da mahaifina ya kāre Shaidun Jehobah a gaban jama’a. Ya tabbata cewa abin na yi imani da shi ya taimaka min in iya gyara salon rayuwata. A yawancin lokaci mahaifiyata takan ce da na yi nazarin Littafi Mai Tsarki tun da wuri. Kuma abin da ta fada gaskiya ne.
Abubuwan da suka faru da ni a rayuwata sun sa na san cewa mutum ba zai sami kome daga shan kwayoyi da kuma wasu ayyukan rashin da’a ba. Yanzu ina farin ciki sosai da yake ina koya wa mutane gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki domin ita ce ta ceto ni.